Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Mai Sallar Isha'i Zai Iya Bin Mai Sallar Tarawihi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Wanda Sallar Isha'i ta wuceshi tare da liman, bai riski jam'i ba, Shin Ya Halatta Yabi Sallar Tarawihi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ya kamata Musulmi yazama Mai gaggauta Yin Ayyukan Alkhairi, Musamman Alokuta Kebantattu kamar Watan Ramadan da'ake Buɗe qofofin rahma, Ake kulle qofofin Wuta, ake tsare Shaiɗanu, kowanne dare mai kira yana kira, Duk Mai neman Alkhairai yaqara himma, mai ayyukan sharri ya Bari.

Wanda Sallar Isha'i ta wuceshi tare da liman, bai riski jam'i ba, ana duba yanayin halin mutum, idan ka tarar Angama sallah kuma kuna da yawa kuka rasa Jam'in isha'i ɗin, daga biyu zuwa Sama, zakuyi sallar jam'i tsakaninku, donku kubuta daka saɓanin Malamai na Sallar farillah Abayan Mai nafila. Idan Mutum Yazo ana Tsaka da Sallar Asham, ko yazo liman yafara sallar Asham da tazarar lokaci kaɗan, Kuma yana tsoran l kebewa ya tayar da Wani jam'i na Sallar isha'i da baiyi ba, zai sawa wasu rudani, anan Abunda yafi shine yabi Sallar tarawihi ɗin da niyyar Shi Isha'i yakeyi, idan Liman Yayi Sallama daka raka'a ta Biyu saiya Tashi ya cikaso.

Kamar Yanda Malam Bin Baaz Yace: A cikin Majmu'u fatawa dinsa, Yana mai Hujjah da Hadisin Mu'azu Bin Jabal Allah yaqara masa yarda yace: Yana Sallah Tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasalla., sannan Saiya koma Wajan mutanensa ya sake Yin wannan sallar dayayi Tare da Annabi da Mutanensa, Amatsayin shi nafila yai mutanensa Kuma Sunyi farillah..

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments