Abubuwan Da Ke Ciki
Aure dai guda ɗ aya ne, sai dai wasu samaye da Bahaushe ya kirashi da su, gwargwadon dalilin yinsa ko wasu abubuwa da suka biyo bayan yin sa. Manfar yinsa ɗ aya ce, sai dai kuma yana da rabe-rabe kamar kashi goma sha biyu. Duk da rabe-raben za ka samu ƙ udurin su ɗ aya ne, ko da za a samu bambanci, sai dai ɗ an abin da ba a rasa ba, Don kuwa za ka sami mata da miji suna ƙ aunar juna da girmama juna ko da haihuwa ko babu. Muna da aurarraki kamar haka:
1. Auren Ku
ɗ
i. (wanda aka biya sadaki, da sauran
ɗ
awainiya)
2
Auren Sadaka. (wanda aka sadaukar da sadakin)
3. Auren Zumunci. (aure na 'yan uwa, dangin
uwa ko na uba.)
4. Auren Dole/
Ƙ
i. (an yi bisa tilas,
ko ango ko amarya wani bai so.)
5. Auren
ɗ
auki sandarka/takalmi. (auren mace tana zaune
a gidanta daban.)
6. Auren je ka da kwarinka. (a auri mace tana
wani gari daban.)
7. Auren daukar buta. (auren tsoho da tsohuwa
don ta zuba mai ruwa.)
8. Auren kashe wuta. (auren da akan yi don a
koma gun tsohon miji.)
9. Auren huce takaici. (auren da akan yi don
a share hawaye.)
10. Auren
ɓ
oyon wata. (aure kafin azumi, in ya wuce sai
a fita.)
11. Auren kangara. (auren da masu arziki kan
yi a tayar baikon wasu.)
12. Auren Jari. (a auri mace saboda ku
ɗ
inta ko na iyayenta.)
Auren Ku
ɗ
i
Shi ne dai auren da aka saba da shi a inda za
a yi duk wani abu da aka saba yi a kowane lokaci, misali kayan toshi da kayan
sa rana da gaisuwar uwa da uba da ku
ɗ
in aure da kuma sadaki, kuma yakan zo cikin
shiri da kuma sani.
Auren Sadaka
Ya
ɗ
an sha bamban da auren ku
ɗ
i, don kuwa sau da
yawa ba a yin wasu abubuwa da ake yi a cikin auren ku
ɗ
i, a wannan lokacin
ma akan yi shi babu sanannen ciki, amma a wasu wuraren akan sanar da iyaye,
kamar misali iyayen yarinya kan aika gidan iyayen yaro a wani lokacin kuma
iyayen yaro sukan ro
ƙ
a domin a bai wa yaronsu, wasu kuma su iyayen yarinya kan
bari sai an gama wahalhalu na aure kamar na ku
ɗ
i, to a
ƙ
arshe sai an zo
ɗ
aurin aure ne sukan
bayyana cewa sun sadaukar ma shi sadakin. Shi dama dai sadaukar da sadakin shi
ne muhimmi a sha'anin auren. Sadaka a wani lokacin akan shawaraci yarinya ko
tana da wanda take so ko babu, don gudun rikici, a wurare da yawa iyayen yarinya
su ne suke yin kome da ya shafi kayan aure.
Auren Zumunci
Shi kuwa yana da ala
ƙ
a da zumunta, yakan
zama na ku
ɗ
i ko na sadaka, wani
lokacin iyayen kan ha
ɗ
a da wannan auren a
inda
ɗ
ayan
ɓ
angaren kan shawarci
ɗ
aya, kamar misali wa
na da yarinya to sai ya shawarci
ƙ
aninsa da yake da
yaro don a ha
ɗ
a auren zumunci ko
kuma
ɗ
an mace, watau ya ya
auri 'yar namiji watau wani amma a wani lokacin su kansu yaran kan shirya
tsakaninsu sai daga baya su sanar da iyayensu.
Misali;
a. Kakanni
Ɗ
aya.
b.
Ɗ
an wa da 'yar
ƙ
ani.
c.
Ɗ
an mace da 'yar
namiji.
d. 'Ya'yan abokan wasa.
e. 'Ya'yan aminai.
Auren Dole
Yadda yake faruwa shi ne, sau da yawa daga
nuna iko ne wajen rashin shawartar yarinya ko uwar yarinya, watau a nan a samun
sa
ɓ
abi tsakanin yarinya
da ubanta, don kuwa za ka samu cewa shi uban akwai wanda take so zai ba shi
aurenta, to sai ta kasance ita kuma ba ta son shi, to idan ya matsa aka yi
auren ba tare da yardarta ba, to sai ka tarar ta fara gudu, watau dai ta
ƙ
i zama, a wani
lokacin laifin daga wurin kakanni yake don kuwa sukan tilasta a yi auren da
wanda suke so, to daga nan fa sai yarinya ta fara guje-guje.
Auren
Ɗ
auki Sandarka
A kan yi shi ne lokacin da mutum ya auri mace
tana gidanta, shi kuma yana gidan shi amma in lokacin kwananta ya zo, to sai ya
tafi, sau da yawa wa
ɗ
anda suka manyanta,
watau suka tsufa don gudun zama kawai da kare mutunci, ko kuma idan mutum
ma'abocin safara ne, watau matafiyi.
Auren Je Ka Da Kwarinka
Auren je ka da kwarinka shi ne auren da zai
auri wata mata tana wani gari daban. Idan zai tafi wurinta ranar da take da
girki, to sai ya
ɗ
auki kwari ya ri
ƙ
e, saboda ha
ɗ
ari ko hari. A wani
lokaci kuma irin wannan aure akan kira shi da auren takalmi. Mafi yawa an fi
samun fatake da direbobi da jakadu su ne suka fi yin irin wannan aure, sannan
manyan mutane su suke yin sa, ba'a cika samun saman da 'yan mata sababbin aure na
yin sa ba, sai dai dattawa da zaurawa.
Auren
Ɗ
aukar Buta
Shi kuma akan yi sa ne musamman tsakanin
sofaffi watau lokacin da mutum ya tsufa musamman ya kasance kuma ba shi da
mata, to sai ya nemi wata tsohuwa mai
ɗ
an
ƙ
arfi su yi aure amina
na daukar buta, watau babu maganar saduwa a tsakanin su kamar yadda yake faruwa
a tsakanin ma'aurata, sai dai wasu ayyuka na yau da kullum.
Auren Kashe/Kisan Wuta
Wani aure ne da mace kan yi bayan mijinta ya
yi mata saki uku, watau babu halin ta sake komawa sai dai ta yi wani auren.
Ma'ana ta auri wani namijin daban kamar dai yadda shari'ar Musulunci ta shimfi
ɗ
a.
Auren kashe wuta kan faru ne ta fuska biyu,
na farko shi ne in mace na kwa
ɗ
ayin komawa wurin mijinta na da, to sai ta samu
ɗ
aya daga cikin
zawarawanta, watau ta za
ɓ
i bazawari
ɗ
aya ta aure shi, amma
ita akwai abin da ta
ƙ
ulla a zuciya, watau ba zama za ta yi ba, koda yake shi
ba za ta nuna masa ba. Sai dai bayan an
ɗ
aura aure an yi tarewa na
ɗ
an kwana biyu, sai
kawai ta tayar da hankali babu gaira babu dalili don ka
ɗ
ai ta cika burinta
har sai mijinta ya gaji ya sake ta. Da haka ta faru sai ta koma gidansu ta yi
idda sannan ta nemo tsohan mijin, watau mijinta na da ta yi kome.
Dangane da fuska ta biyu kuwa da auren kashe
wuta kan faru shi ne, idan shi mijin ne yake son matarsa ta dawo, to a nan ma
dai sukan shirya da matar cewar ta tafi ta yi auren kashe wuta. Koda yake
shari'a ba ta yarda da irin wannan ba, amma dai akwai masu yin shi.
A
ƙ
arshe dai kuma a ta
ƙ
aice, auren kashe
wuta dai shi ne mace ta yi wani aure na wucin gadi da nufin ta halasta ga
tsohon minta wato ta kashe auren don ta yi kome
Auren Huce Takaici
Wani aure ne da akan yi don kawar da
ɓ
acin rai sakamakon
wasu abubuwa da yawa, kamar rasa wani aure, sa
ɓ
a al
ƙ
awari daga iyayen
yarinya, ko kuma ita kanta yarinyar. Wannan kuwa kan faru ne bisa wasu dalilai
da suka ha
ɗ
a da nuna ku
ɗ
i daga wani saurayi
don ya saye iyayen yarinya ko kuma ya kangare yarinyar a sanadin haka, sai
maganar da aka sani da farko ta tashi, sai a koma kan wannan mai ku
ɗ
i ko kuma ana iya
samun, sa
ɓ
ani tsakanin saurayi
da budurwa, wannan shi ma yakan kawo lalacewar maganar aure, koda kuwa an yi
sa-rana (Baiko).
Bugu da k
ƙ
ari neman auren da
aka fi samun irin wannan ala'amari su ne kamar auren sadaka, auren zumunci ko
auren kamu. Auren sadaka shi ne wanda koda mutum ya aiko iyayensa zuwa gidan
iyayen yarinya akan ce to sai dai a sauarara idan rabonsa ce, to sau da yawa na
wasu ba ya yiwuwa sai kawai a ba wani. Haka shi ma auren zumunci sai a samu a
dangin uwa na so na uba basa so ko dangin uba na so na uwa ba sa so, to idan
ɓ
angaren da ba sa so
suka yi rinjaye, sai kawai magana ta lalace a yi auren da wani. Game da auren
kamu, shi kuma iyaye ko kakanni ne suke kama wa
ɗ
ansu ko jika yarinya tun tana
ƙ
arama cewa sun ri
ƙ
ar masa in ta girma
za a ha
ɗ
a su aure, to shi ma
akan samu 'yan rigingimu in yarinyar ta girma, sai ta ce ba ta so, don haka sai
a yi auren da wani.
Bisa ga yadda wa
ɗ
annan abubuwa suka
faru kamar yadda aka saba a
ɗ
abi'a irin ta
ɗ
anAdam, in har ya nemi abu ya rasa, to dole
ne ransa ya
ɓ
aci, to wannan shi ke
haifar da auren huce takaici. Dangane da yadda ake yin auren huce takaici shi
ne kamar haka; da zarar an hana mutum aure ta sanadiyyar wa
ɗ
annan dalilai ko
makamantan su, sai kawai mutum ya ba da cigiyar budurwar da ta isa aure wadda
za a yi cikin gaggawa, a gajeren lokaci ka
ɗ
an. Kuma sau da yawa akan yi wasu abubuwa
cikin gadara ko nuna isa. A wani lokaci kuma, abokai (na
uba ko
ƙ
awaye na uwa) ko 'yan
uwan wanda aka yi wa wannan, sukan bayar da auren 'yarsu in suna da ita don su
share masa hawaye. Wannan she ake cewa auren huce takaici.
Auren
Ɓ
oyon Wata
Auren
ɓ
oyon wata wani aure ne da mafi yawa ake yin
sa in watan Azumi ya kusa tsayawa, sai ka ga mata zawarawa ko kuma mata masu
zaman kansu suna
ƙ
o
ƙ
arin samun mijin da za su aura don su samu su yi azumi da
aurensu.
Babban abin da ya sa aka kira wannan aure da
ɓ
oyo shi ne, na farko
dai sau da yawa kuma mafi rinjaye auren ba ya
ƙ
arko, da zaran watan
Azumi ya wuce watau bayan Sallah da kwanaki ka
ɗ
an sai ka ji auren ya mutu, don haka
ne sai Bahaushe ya ce daman an yi ne don
ɓ
oyewa watan azumi, saboda an yi aure kafin ya
tsaya an kuma kashe bayan ya
ƙ
are.
Fuska ta biyu kuma ita ce kaucewa wata
al'adar Hausawa da suke gudanarwa a cikin watan azumi. Shi ne kuwa kamu gwauro
ko kiran gwauro, koda yake wannan al'adar ba ta bar mace ko namiji ba, a nan
mazan su ma sukan samu su yi auren ko da kuwa na
ɓ
oyon wata ne don su kaucewa kamun da
kiran gwauro. Sannan kuma sun samu mai yi musu abinci da asuba da kuma lokacin
Sahur.
Baya ga wannan kuma, akwai wata al'adar ita
ce yi wa mata zanin tashin asuba, watau dai zanin sallah da maza kan yi wa
matansu. A wani lokaci wasu matan kwa
ɗ
ayin samun kayan sallah/zanin tashin asuba
yakan sanya su su yi wannan aure. Haka kuma wasu mazan koda auren ya mutu ba sa
ƙ
wace
kayan da suka yi wa mace lokacin aureta. Don haka sai kawai mace ta tashi da
kaya masu yawa, wannan a wani lokaci ke kwa
ɗ
aitar da yin auren
ɓ
oyon wata ga wasu
matan.
Auren Kangara
Auren kangara wani aure ne da akan yi shi don
nuna isa ko wadata, amma kuma ya bambanta da auren huce takaici. Wannan irin
aure yakan faru ne a tsakanin ha
ɗ
uwar saurayi ko wani attajiri da wata budurwa
da aka riga aka yi wa baiko da sa-rana, koda kuwa aurensu ya kusa. Matu
ƙ
ar soyayya ta shiga
tsakaninsu, to da zarar rabon saurayin nan ya yi amfani da ku
ɗ
i ya ciwo kan ita
yarinyar da kuma iyayenta, to sai ya tambayi ko nawa wancan tsohon saurayin
nata ya kashe don ya biya shi a soke maganar aurensu a kafa tashi sabuwa. Kuma
an fi yin irin wannan ne idan wanda yake nema da farko ba shi da hali ma'ana
(ku
ɗ
i), shi kuwa wanda ya
zo daga baya mai hannu da shuni ne, ko kuma iyayensa ne masu hannu da shuni.
Dangane da abin da auren Kangara kan ha
ɗ
a da zubar da
mutunci, yankewar zumunci. A wani lokaci kuma bai cika yin
ƙ
arko ba. Duk inda aka
samu auren Kangara, dole ne mutuncin iyayen yarinya ya zube ga
ɓ
a
ɗ
aya, tun daga
ɓ
angaren iyayen
saurayin da aka hana auren har ya zuwa sauran al'umma, a wani lokacin ma yakan
kai har a dangin yarinya a samu sa
ɓ
ani. Wanda daga wannan ne ba za a
ƙ
ara
ɗ
aukar su a matsayin
dattijai ba, don kwa
ɗ
ayinsu ya rinjaye su
sun yi
ƙ
aranta.
Bayan wannan kuma, akan samu yankewar
zumunci, kamar misalin idan manemin auren na farko
ɗ
an uwa ne wato da
dagantaka a tsakani, mafi yawa zumunci kan yi rauni ko kuma ya yanke ya kasance
ba sauran wata hul
ɗ
a a tsakani. Dangane
da wani aibu da auren Kangara kan haifar kuwa shi ne, a mafi yawan lokuta ba ya
yin
ƙ
arko, an yi ne don son abin duniya ne. Bisa ga wannan
dalili ne sai ka iske ana nuna wula
ƙ
anci tun daga kan
yarinya har ga zuwa iyayenta, Wanda idan ba sa'a aka yi ba sai ka ji auren ya
mutu tun ba a je ko'ina ba.
Auren Jari
Auren
jari wani aure ne da akan yi shi don nuna kwa
ɗ
ayi, wato son abin
duniya ku
ɗ
i ko kuma mu
ƙ
ami. A inda za a auri
mace saboda ku
ɗ
inta ko na iyayenta,
isa ko wadata amma kuma ya bambanta da auren huce takaici. Wannan irin aure
yakan faru ne a tsakanin saurayi da budurwa ko bazawari da bazawara. Kamar wani
attajiri ya rasu sai ka ga ana ruguguwar auren matarsa, a dalilin ku
ɗ
in da ta gada.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.