Mace Mai Ciki Za Ta Iya Ajiye Azumi?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malan dafatan kana lfy mlan ina da tambaya inada ciki ne kuma ya tsufa kuma cikin azumin nan zan haihu amman duk ranan da na yi azumi ɗan cikina se ya wuni ko kwana be motsa ba sannan kuma ga ulcer ya tashi shi ne na ce malan zan iya ciyarwa?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

    Da farko dai mace mai ciki ko mai shayarwa za ta iya ajiye azumi idan tana tsoron cutuwarta ko cutuwar yaron da take shayarwa ko kuma na yaron dake cikinta idan ta yi azumin.

    Dalili yana cikin Hadisin da aka ruwaito daga Anas dan-malik al-ka’abi (Allah ya yarda da shi), daga Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam ya ce: “Hakika Allah ya ɗaukewa matafiyi rabin Sallah, kuma ya ɗaukewa matafiyi da mai ciki da mai shayarwa azumi’’. Ibn Maajah ne ya ruwairo wannan hadisi. Haka kuma Abu dawud da Tirmuzi suma sun ruwaito wannan Hadisi.

    Malamai sun yi saɓani dangane da ramuwa ga mai ciki da mai shayarwa. Waɗansu sun tafi akan fatawar Abdullahi Ɗan-umar da Abdullahi Ɗan abbas da Ishaq bin Rahawaih cewa; mai ciki da mai shayarwa babu ramuwa akansu sai dai ciyar da miskini. Dalilinsu kuwa shi ne faɗin Allah ta’ala:

    أَيَّامًا مَّعْدُودَاتٍ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ فِدْيَةٌ طَعَامُ مِسْكِينٍ فَمَن تَطَوَّعَ خَيْرًا فَهُوَ خَيْرٌ لَّهُ وَأَن تَصُومُوا خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ

    Kwanuka ƙidãyayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam. Kuma a kan waɗanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya ƙãra alhri to, shi ne mafi alhri a gare shi. Kuma ku yi azumi (da wahalar) ne mafi alhri a gare ku idan kun kasance kuna sani. (suratul Baqara aya ta 184)

    Suka ce wannan ayar ta haɗa da tsofaffi da ba za su iya yin azumi ba, da mai ciki da mai shayarwa.

    Haka zalika shaykh Nasiruddeen Albani a cikin littafinsa Irwaa al-Ghaleel, da kuma almajiransa a cikin littafin Sifatus-Saum-an-Nabiyi, sun tafi akan cewa fatawar bin Umar da bin Abbas babu wanda ya saɓa musu a cikin sahabbai, don haka za’a iya cewa kamar ijima’i ne na jamhurin sahabbai baki ɗaya.

    To sai dai jamhur na mafiya yawan malamai sun tafi akan cewa, mai ciki da mai shayarwa suna cikin marasa lafiya ne, don haka zasu rama azumin da suka sha maimakon ciyarwa. Wannan shi ne ra’ayin Imam Auza’i da Imam Hasanul Basari da Ibrahim an-Nakha’i da Ataa, da imamuz-zuhuri da kuma Imam Malik. Kuma wannan shi ne ra’ayin waɗansu daga cikin magabata kamar su Ibn Taimiyya da almajiransa. Daga cikin malamai na kusa waɗanda suka tafi akan wannan fahimta akwai ibn Baz da Al-uthaimin da sauransu.

    Allah shi ne mafi sani.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.