Ticker

6/recent/ticker-posts

Ramukon Azumi Ga Mamaci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam ya dawainiya da al'umma da taimako wajen fahimtar dasu akan abin daya shige musu duhu. Allah ya karawa malam hakuri da juriya da mutane. Ameen.

Malam tambaya ta anan itace 'mutum ne ya kai shekaru hudu da rasuwa kuma ana binshi bashin Azumi, yaran shi basu biya mishi azumin da ake binsa ba, amma dangin shi suke so su biya mishi'. To yaya azumin zai kasance kenan wajen ramukon?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Lallai akwai hadisi Sahihi wanda Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) yace : "DUK WANDA YA MUTU DA AZUMI AKANSA, TO WALIYYINSA YAYI MASA AZUMIN".

To amma Malamai sunyi ma hadisin fahimta daban daban.

Wasu daga cikin Maluman Hadisi da kuma Abu Thaur sunce ya halatta Waliyyin mutum (wato Makusancinsa) yayi masa azumi amadadinsa, saboda hujjar wannan sahihin Hadisin.

Maluman Ahlul Baiti da Imamu Malik da Abu Hanifah sun ce ba za'ayi azumi amadadin Mamaci ba. Abinda ya za wajibi shine aciyar da Miskini guda bisa kowanne azumi guda da ake bin Mamacin. Sun kafa Hujjah da Hadisi Sahihi wanda Imamut Tirmidhiy ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Umar (ra) : "WANDA YA MUTU DA AZUMI AKANSA, TO ACIYAR DA MISKINI GUDA BISA KOWACCE RANA".

(Ibnu Maajah ma ya ruwaito irinsa acikin Sunanu nasa, kuma Hadisi ne Sahihi).

Abinda ke Qara Qarfafar wannan shine Fatawar da aka samu daga Sayyidah A'ishah da kuma Ibnu Abbasin (ra) akan cewa ciyarwar za'ayi.

Ibnu Qudaamah yace Wannan ita ce Sahihiyar Fatawar Mafiya yawan Ma'abota ilimi. Kuma an ruwaito haka daga Nana A'ishah da Ibnu Abbas (ra). Kuma ita ce Fatawar Maliku da Layth bn Sa'ad da Auza'iy da Sufyanuth Thawree da Shafi'iy da Hasan bn Hayyin da Ibnu 'Ulayyah da Abu Ubaidin acikin Sahihiyar Magana daga garesu.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

RAMUWAR AZUMIN MAMACI

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam, ’yar’uwarmu ce ta rasu a cikin Ramadan ɗin nan alhali ba ta yi waɗansu daga cikin azumman watan ba. A bara ma akwai waɗanda ake bin ta duk a sakamakon rashin lafiya. To wai yaya za a yi wurin rama mata?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Malamai sun kasa azumman da ake bin mamaci saboda dalilin rashin lafiya ne kamar haka

1. Idan tun farko rashin lafiyarsa mai tsanani ne wanda shari’a ta ɗora masa ciyarwa kaɗai a maimakon duk yinin da bai iya yin azumin a cikinsa ba, sai kuma ya rasu a hakan bai ciyar ba, to wajibi ne magadansa su ciyar masa. Ba rama masa azumi za su yi ba.

2. Idan kuma rashin lafiyar irin wanda aka ɗora masa ramawa ne idan ya warke, sai kuma ya warken amma bai rama ba har ya rasu, to a nan malamai sun sha bamban a kan hukuncinsa. Maganar da ta fi daidai, in shaa’al Laah ita ce: Magadansa su ciyar masa da abinci kawai.

Dalilin hakan kuwa shi ne fatawar da A’ishah da Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhum) suka bayar a cikin Sunan Abi-Daawud: 2301, da Musannaf Ibn Abi-Shaibah: 3/113 da At-Tahaawiy a cikin Mushkilul Athaar: 2/142 da Ibn Hazm a cikin Al-Muhallaa: 7/4. Ita ce kuma sahihiyar fassara ga hadisan da suka riwaito a kan haka daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a cikin Sahih Al-Bukhaariy: 1952, 1953 da Sahih Muslim: 1147, 1148.

3. Idan kuma rashin lafiyar irin wanda yake fata ya rama ne idan ya warke, amma kuma sai bai warken ba har zuwa rasuwarsa, to a nan malamai sun yarda cewa babu wani laifi a kansa. Haka ma magadansa.

4. Idan kuma azumin da ake bin sa na wani alwashi ko bakance ne da ya yi wa Ubangiji Ta’aala, kuma har ya rasu bai biya ba, to shi kam lallai magadansa su rama masa, ko dai ta hanyar yin azumin a ranaku mabambanta, ko kuma ta hanyar su haɗu dukkansu su yi a rana guda.

Ana iya duba Tamaamul Minnah: 2/172-174 na Al-Azzaaziy domin ƙarin bayani. Ko kuma: Tambaya ta A324 a kan Rama Azumin Mamaci.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments