Ticker

6/recent/ticker-posts

Rama Azumi Ga Wanda Ya Rasu

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam, mahaifina ne Allaah ya yi masa rasuwa, ya yi azumi guda 24, a ranar na 25 ne Allaah ya yi masa rasuwa. Shin za a biya masa sauran azumin da ya rage ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

 إِذَا مَاتَ ابْنُ آدَمَ انْقَطَعَ عَمَلُهُ إِلَّا مِنْ ثَلَاثٍ

 Idan ɗan Adam ya mutu aikinsa ya yanke sai dai ta hanyoyi uku.

Wannan ya nuna: Daga lokacin da muslmi ya rasu ne ayyukansa suka ƙare. Babu wani aiki kuma da ya hau kansa daga wannan lokacin.

Don haka, wanda ya yi azumi na tsawon kwanaki ashirin da huɗu, kuma ya rasu a ran na ashirin da biyar babu komai a kansa, domin iyakan abin da Allaah ya ƙaddara masa kenan a rayuwarsa. Don haka babu wani abin da za a rama masa, kuma ba za a kama shi da abin da ya rage na azumin watan ba.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments