Ticker

6/recent/ticker-posts

Neman Gafara A Dunkule

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Wanda aka yi masa laifi kuma aka nemi ya yafe, sai ya nemi sanin menene amma ba a gaya masa ba. Sai dai aka cigaba da neman ya yafen kawai, sai shi kuma ya ce, ya yafe. To hakan ya yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Asali dai kamata ya yi a gaya masa irin laifin da aka yi masa, domin haƙƙinsa ne. Amma idan aka ɓoye masa saboda waɗansu dalilai, kamar idan ana ganin bayyana masa zai haifar masa da damuwa ko wani tashin hankali ko rashin yarda da amincewa da wanda ya aikata masa laifin, duk da ya tuba. Ko kuma idan zai ɗauke shi ga rabuwa ko yanke zumunci da shi, ko rashin amincewa da mutane. Ko kuma shi ma ya shiga aikata hakan ga wani, ko dai waɗansu matsaloli irin waɗannan.

A duk lokacin da aka yi tunanin hakan to bai kamata a gaya masa irin laifin da aka yi masa ba, kamar yadda abin yake a nan. Dalili kuwa, malamai sun yarda cewa ƙofar ɓarna a cikin al’umma ƙuntata ta ake yi, bai halatta a faɗaɗa ta ko a yalwata ta ba.

Idan shi kuma da aka yi wa laifin ya amince har ya yarda ya yafe laifin ba tare da ya san nau’insa ba, malamai sun nuna hakan ya yi. Kuma ya wadatar ga shi mai neman a yafe masa laifin, in sha Allah.

Allaah ya saka wa mai irin wannan halin na yafiya da alkhairi, kuma ya shigar da shi cikin waɗanda yake magana a kansu cewa

وَلْيَعْفُوا وَلْيَصْفَحُوا أَلَا تُحِبُّونَ أَنْ يَغْفِرَ اللَّهُ لَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ

Lallai (masu daraja) su yafe kuma su kawar da kai. Ko ba ku son Allaah ya gafarta muku ne, alhali kuma Allaah Mai gafara ne Mai Rahama? (Surah An-Nuur: 22).

Allaah ya gafarta mana gaba-ɗaya.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/K7RkQRMf2b57l3UENoJ1Or

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments