𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Idan mutum ya musulunta acikin
watan Ramadan, shin ya wajaba akansa ya azumci sauran kwanakin da suka rage na
watan, tun daga ranan da ya musulunta har zuwa ƙarshen watan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Eh Idan mutum ya musulunta acikin
watan Ramadan to yana wajaba akansa ya azumci sauran kwanakin da suka rage na
watan, tun daga ranan da ya musulunta har zuwa ƙarshen watan, wannan ijma'ine na malamai,
ibnu Qudama Allah ya masa rahama ya ambaci wannan ijma'in. Amma kwanakin da
suka wuce na watan Ramadan ɗin
kafin musuluntarsa bazai ramasu ba, wannan shine zancen jumhur na malamai daga
cikin su harda malaman mazhabobi guda huɗu.
Domin kwanakin da suka shuɗe
sun kasance ne alokacin yana halin kafirci, misalinsu shine kamar misalin watan
Ramadan da suka shuɗe
ne kafin musuluntarsa.
Amma idan musuluntar nasa ta
kasance da rana ne to wajibine ya kame bakinsa har zuwa faduwar rana Sannan
kuma ya rama azumin wannan wunin bayan Ramadan, domin ya riski wani ɓangare na ibada alokacin
da ya musulunta hakan sai lizimta masa ramata kamar wanda ya musulunta lokacin
sallah bai fita ba.
HUKUNCIN WANDA YA MUSULUNTA A WATAN
RAMADAN:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Idan mutum
ya musulunta acikin watan Ramadan, shin ya wajaba akansa ya azumci sauran
kwanakin da suka rage na watan, tun daga ranan da ya musulunta har zuwa ƙarshen watan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Eh Idan
mutum ya musulunta acikin watan Ramadan to yana wajaba akansa ya azumci sauran
kwanakin da suka rage na watan, tun daga ranan da ya musulunta har zuwa ƙarshen watan, wannan ijma'ine na malamai, ibnu Qudama
Allah ya masa rahama ya ambaci wannan ijma'in.
Amma
kwanakin da suka wuce na watan Ramadan ɗin kafin musuluntarsa ba zai ramasu ba, wannan shine
zancen jumhur na malamai daga cikin su harda malaman mazhabobi guda huɗu. Domin kwanakin
da suka shuɗe sun kasance ne alokacin yana halin kafirci, misalinsu
shine kamar misalin watan Ramadan da suka shuɗe ne kafin
musuluntarsa.
Amma idan
musuluntar nasa ta kasance da rana ne to wajibine ya kame bakinsa har zuwa
faduwar rana Sannan kuma ya rama azumin wannan wunin bayan Ramadan, domin ya
riski wani ɓangare na ibada alokacin da ya musulunta hakan sai
lizimta masa ramata kamar wanda ya musulunta lokacin sallah bai fita ba.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.