Ticker

6/recent/ticker-posts

Mafificin Aikin Da Mai Azumi Zai Dinga Yi A Watan Ramadan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam. Menene Mafificin Aikin Da Mai Azumi Zai Dinga Yi A Watan Ramadan???

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

Aikin da yafi falala ga mai azumi shine

1. KARATUN AL'QURANI. Ma'ana ya lazimce shi dare da rana, kuma yadinga izna da abin da yake karantawa. Amma idan bazai iya karatun Al-Qurani ba, to sai ya rinka lazimtar inda ake karatun Al-qur'anin ko fassarashi domin hadisi ya tabbata daga nana Fadima 'yar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam da Abu Huraira yardar Allah ta tabbata a garesu sunce: "Mala'ika Jibrilu ya kasance yana bijirowa da Annabi Sallallahu alaihi Wasallam Al'Kur'ani sau ɗaya a kowace shekara, sai ya bijiro masa dashi sau biyu a shekarar da zaiyi wafati. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito (1). (1) Bukhari K=66, Book=7, Hadith=4998 da Muslim

K=44, B= 15, Hadith=2450.

Wannan yana nuna cewa karatun Al-qur'ani shine mafificin ibada a cikin watan Ramadan. Allah maɗaukakin Sarki yace: "Lallai mun saukar dashi a daren Lailatul Kadari.

2. KYAUTA: Ya kamata mai Azumi ya yawaita kyauta wajen ciyar da jama'a, da sadaka, da taimakon gajiyayyu da makusanta. Kamar yadda ya tabbata a hadisin ibn Abbas cewa:"Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yafi kowa kyauta, kuma mafi alkhairinsa yana yinsa ne a Ramadan yayin da yake saduwa da Jibrilu. Kuma ibn Abbas (R.A) yace: Alkhairin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yafi sakakkiyar iska".Bukhari ne ya ruwaito shi (2). (1) Suratul Kadari Aya1 (2) Bukhari K = 1, B = 5, da Muslim K = 43, B = 12, H = 2308.

3. NAFIL-FILI: Anaso mai Azumi ya yawaita Nafil Fili musamman kiyamul laili Saboda hadisin Abu Hurairah yardar Allah ta kara

tabbata a gareshi yace: Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace: "Duk wanda yatsaya kiyamulaili yana mai imani, da neman lada an gafarta masa zunubansa da suka gabata". Bukhari ne ya ruwaito shi (1). Haka kuma Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace: Wanda yayi sallah dare tare da liman har yagama za'a rubuta masa ladan kiyamullaili. Kuma anfison duk wanda zaiyi kiyamullaili ya tsawaita tsayuwar saboda hadisin Khuzaifa (R.A) Targib Wattarhib wanda Albani yayiwa tahkiki lambar (1078). "Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya kasance yana tsawaita karatu a sallar dare a watan Ramadan fiye da sauran sallolin dare, yace, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yakan karanta Suratul Bakarah da Nisa'I da Ali'Imran a raka'a ɗaya, kuma baya wuce ayar da akayi tsoratarwa a cikinta sai ya tsaya ya roki Ubangiji tsari. Kuma bai gama raka'a biyu ba sai ga Bilalu (R.A) yazo yana neman izni ayi sallar Asuba. Ahmad ya ruwaito wannan hadisin kuma ya ingantashi.

4. YAWAN ZIKIRI DA SALATIN ANNABI (Sallallahu alaihi Wasallam): Abune mai matukar falala mutum ya yawaita Zikiri

da Salati ga Shugaban Halitta irin wanda ya tabbata daga bakin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam.

Allah Madaukakin Sarki ya ce

 أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْراً كَثِيراً

Ya ku wadanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa. (Suratul Ahzab aya ta 4)

وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيراً وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْراً عَظِيماً

Da masu ambaton Allah da yawa maza, da masu ambatonsa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma”. [Suratul Ahzab, aya ta 35]

ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﻣَﻠَﺎﺋِﻜَﺘَﻪُ ﻳُﺼَﻠُّﻮﻥَ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲِّ ۚ ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﺻَﻠُّﻮﺍ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠِّﻤُﻮﺍ ﺗَﺴْﻠِﻴﻤًﺎ

Lalle, Allah da mala’ikunSa sunã salati ga Annabi. Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi. [Suratul Ahzab, aya ta 56]

An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara mishi yarda ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garew shi ya ce:- (Mafi dacewan mutane gare ni ranar alkiyama shi ne wanda yafi yawaita min salati).

An karbo daga Abdullahi bn Amru bn Al-As (RA) cewa lallai ya ji Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) yana cewa: “Wanda ya yi min salati daya, Allah zai yi masa salati goma a madadinta. Kuma wanda Ya yi min salati goma Allah zai yi masa salati dari a madadinta. Wanda kuma ya yi min salati dari, Allah zai yi masa salati dubu a madadinta. Wanda kuma ya yi min salati dubu za mu yi kafada-da-kafada da shi wajen shiga Aljanna.”

5. CIYAR DA MAI AZUMI ABIN BUƊA BAKI: Yana daga cikin mafificiyar ibada mutum yayi kokari wajen bawa ɗan'uwansa abin Buɗe baki saboda hadisin da Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yake cewa: "Duk wanda yaciyar da mai Azumi abinda zaiyi buɗe baki yana da kwatan kwacin ladan wanda ya ciyar batare da an rage ladan wanda ya ciyar ba".Tirmizi yace wannan hadisine hasanun sahih.

6. UMRAH: Yin umrah acikin watan Ramadan ga wanda Allah ya bashi iko yana daga cikin Aiyukan da ake kwadaitar da mai Azumi yayi. Amma duk da haka bai kamata mutum yatafi umrah yabar makwabtansa da danginsa da sauran mabukata a cikin yunwa da halin kakani kayi ba. Kuma ya kamata mu fahimci cewa, ciyarwa itace abinda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yafi bawa muhimmanci acikin watan Ramadan.

Ya Allah kasa muna daga cikin wadanda zaka 'yanta acikin wannan wata, domin darajar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments