Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Tubalan Turken Zuga A Wakokin 'Yan Tauri Na Sale Kudo Kusada – Kashi Na Uku

Kundin Digiri Na Biyu (M.A Hausa Culture) Da Aka Gabatar A Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero Kano (Maris, 2024)

Nazarin Tubalan Turken Zuga A Waƙoƙin 'Yan Tauri Na Sale Kudo Kusada

Aminu Musa
07036420021
ameenumusa12@gmail.com

BABI NA UKU

3.0 Share Fage

A wannan babi za a kawo hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan bincike sannan a yi bayanin samfurin bincike da sigar bincike, duk a cikin babin za a kawo kayan aikin da aka yi amfani da su wajen gudanar da wannan bincike. Haka kuma za a kawo sunayen waɗanda aka tattauna da su domin samun bayanai tun daga 'yan tauri da makaɗan tauri da masana da manazarta da kuma masu alaƙa da aikin tauri. Duk a cikin babin ne za a kawo ɗa'ar bincike, sannan a naɗe babin gaba ɗayansa.

3.1 Nau'in Bincike

Wannan bincike yana ɗauke da nau'in bincike bi-bayani domin zai yi sharhi ne a kan salon sarrafa Harshe a cikin waƙar tauri tare da bayyana irin yadda ake sarrafa kalmomi da sunayen wasu halittu yadda ya dace da tunanin mai sauraro, tare da kawo irin tasirin da wannan salon zai iya kawo wa a cikin al'umma musamman ga waɗanda su ke sauraren waƙoƙin tauri da masu kallon wasannin su. Don haka bincike ne bi-bayani kamar yadda (Doryn 2011) da (Cresswell 2019) suka bayyana sharhantau na cikin nau'in bincike na bayani.

3.2 Sigar Bincike

Wannan bincike yana da sigogi kamar haka; bayyana yadda makaɗin tauri Sale kudo ke kallon Halaye da ɗabi'un wasu halittu yana danganta ɗan tauri da su. Da kuma yadda yake amfani da hikima da azanci wajen sarrafa abubuwa na amfani da suke da baiwa ko buwaya, yana alaƙanta masu yin tauri da su a cikin kirarin da yake masu. Kamar yadda Cresswell (2019) da Doryn (2011) da Muhammad (2012) suka bayyana cewa ''ana bukatar manazarci ya fito da inda binciken sa ya dosa kai tsaye''.

3.3 Kayan Aikin Bincike

Wannan bincike an yi amfani da kayayyaki kamar su, kundayen bincike, da Littattafai, da mujallu da aka zaɓa da wayar hannu domin naɗar bayanai a yayin tattaunawa da na'ura mai ƙwaƙwalwa da takardu da alƙalamin rubutu.

3.4 Ginshiƙan Bayanai

Akwai waɗansu bayanai masu muhimmanci waɗanda za a bi ta kansu a gudanar da wannan bincike, ga su kamar haka:

3.4.1 Karanta Ayyuka A ɗakin Karatu

A wannan nazari an yi bitar Ayyukan da suka gabata da suka haɗa da Kundayen bincike tun daga kundin digiri na ɗaya da na biyu da na uku, haka suma bugaggun Littattafai an duba su, sannan a ka yi bitar maƙalu da mujallu da sauran takardun ilimi waɗanda suka danganci wannan bincike.

Duk a waɗannan kundaye da Bugaggun Littattafai da muƙalu an duba su ne a waɗannan wurare:

-          Ɗakin karatu na sashen koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero Kano.

-          Babban ɗakin karatu na Jami'ar Bayero Kano.

-          Cibiyar nazarin Harsunan Nijeriya da Adabin baka da fassara da ke jami'ar Bayero Kano.

-          Ɗakin karatu na Sashen Hausa na Jami'ar Umaru Musa yar'adua da ke Katsina.

-          Babban ɗakin karatu na Jami'ar Umaru Musa yar'adua dake Katsina.

-          Ɗakin karatu na Sashen Koyar da Hausa na Kwalejin ilimi ta Isa Kaita da ke Dutsinma, Katsina.

-          Babban ɗakin karatu na kwalejin Gwamnatin tarayya da ke katsina

-          Ɗakin karatu na Hukumar Adana tarihi ta Jahar Katsina.

Sannan an samu wasu Littattafai a shagon siyar da Littattafai na Alhikima da ke cikin garin Kaatsina, an samu wasu a makarantar jeka- ka-dawo ta Gwamnatin jahar Katsina da ke Rimaye ƙaramar Jukumar Kankia Jahar Katsina.

3.4.2 Tattaunawa Da Wasu 'Yan Tauri

An tattauna da wasu 'yan tauri domin bunƙasar wannan aiki, an nemi bayanai daga bakinsu, domin su ne suke aiwatar da kirare-kirare da kuma ganin cewa su ne makaɗan tauri ke wasawa da irin wannan salo na zugawa. Waɗannan bayanai da aka samo daga bakinsu zai taimaka wajen cim ma manufar wannan bincike. Daga cikin 'yan tauri da aka tattauna da su akwai waɗannan:

I) Buhari Canko, Ɗan shekara Arba'in (40)

A garin Rimaye ƙaramar hukumar Kankia

Ranar 10 /08/ 2022

Kamar tsawon minti Hamsin (50m)

Mai sana'ar Gini da kuma huɗɗar Tauri

II) Sama'ila Miloniya, ɗan shekara Hamsin (50)

A garin Naƙawa, ƙaramar Hukumar Kusada

Ranar 12 /08/ 2022

Kamar tsawon minti talatin da biyar (35m)

Mai sana'ar harbi da kuma sayar da ƙore

III) Buhari Lawal Yashe, ɗan shekara Hamsin da biyar (55)

A garin Yashe, ƙaramar hukumar Kusada

12 /08/ 2022

Kamar tsawon Awa ɗaya

Ma'aikacin Gwamnati, kuma ɗan tauri

IƁ) Nababa UK, ɗan shekara Hamsin da shidda (56)

A garin tsohuwar Dokoki, ƙaramar Hukumar Kankia

Kamar tsawon Awa ɗaya

Manomi, kuma ɗan Tauri

Kuma an yi masu tambayoyi kamar haka:

-          Waɗanne Irin Abubuwa ne Makaɗin tauri ke siffanta ɗan tauri da su, a lokacin da ya ke zuga sa domin fitowa cikin fili?

-          Ko makaɗin tauri kan ji kunyar faɗar wasu kalamai kai tsaye a cikin Waƙoƙin sa, ta yadda sai ya sakaya ma'anarsu?

-          Wace irin zuga ce ta fi Jan hankalin ɗan tauri

-          Ko makaɗin Tauri ya taɓa alaƙantaka da wata halitta a cikin waƙarka, kuma ya ka ji lokacin da ya ke ma kirarin?

4.4.3 Tattaunawa Da Masana Da Manazarta A kan Kiɗan Tauri

A wannan bincike akwai buƙatar tattaunawa da masana, al'adun Hausawa domin samun bayanai a kan cikakkiyar al'adar kiɗan tauri, domin samun nasarar cim ma wannan manufar aiki.

Daga cikin masana da Manazartan da aka tattauna da su da waɗanda ake sa ran tattaunawa da su a nan gaba har zuwa kammaluwar aikin akwai:

-          Farfesa Aminu Lawal Auta - Jami'ar Bayero kano

-          Dr, Abdulhadi Uba Gabari - Jami'ar Bayero Kano

-          Dr, Muhammad Ammani- Jami'ar Bayero Kano

-          Dr, Nura Lawal - Jami'ar Bayero Kano

-          Dr, Mustapha Sha'aibu Dafana- Jami'ar Umaru Musa yar'adua Katsina

-          Dr, Abubakar Sani Sayaya - Ma'aikatar yaɗa labarai da ɗab'i, ta Jahar Katsina

-          Dr Aminu Galadima Ɓatagarawa- Jami'ar Umaru Musa yar'adua Katsina

-          Dr, Sabiu Alti - Kwalejin Ilimi Isah Kaita Dutsinma, Katsina

-          Malam Tukur Aliyu - kwalejin ilimi Isah Kaita Dutsinma, Katsina

-          Malam Umar Ibrahim- GDSS Rimaye, Kankia Katsina

-          Malam Buhari Lawal Yashe- GDSS Rimaye Kankia Katsina

 

Daga cikin tambayoyin da aka yi wa waɗannan masana da manazarta da kuma waɗanda za a yi masu a nan gaba akwai waɗannan:

I)                   Shin an taɓa yin Nazarin salon sarrafa harshe a cikin kiɗan tauri?

II)                Ko an taɓa Nazarin Waƙoƙin wannan makaɗi Sale Kudo?

III)               Miye fahimtar ka game da salon sarrafawa a cikin kiɗan tauri?

IV)             Ko masu kiɗan tauri na duba wasu halayyar dabbobi a lokacin da suke danganta ɗan tauri da su.

4.4.4 Tattaunawa Da Masana Ilimin Tauri

Domin samun ganin kwalliya ta biya kuɗin sabulu, akwai bukatar tattaunawa da masana ilimin tauri (Masu wasan tauri) domin samun bayanai mabambanta waɗanda za su taimaka wa wannan bincike ya cim ma manufofinsa. Daga cikin 'yan tauri da aka tattauna da su akwai:

I) Salisu Rabe, ɗan shekara talatin da biyar (35)

A garin Rimaye, ƙaramar Hukumar Kankia

Kamar tsawon minti arba'in (40m)

Ɗan Tauri

II) Hassan Ya'u, ɗan shekara sittin da biyu (62)

A garin ɗankawari, ƙaramar Hukumar Kankia Jahar Katsina

Kamar tsawon minti hamsin (50)

Ɗan Tauri

III) Sani Na'aba, ɗan shekara hamsin da shidda (56)

A garin Magami, ƙaramar Hukumar Kusada, Jahar Katsina.

Kamar tsawon awa daya (1)

Dan tauri

IƁ) Iro ɗan baiwa, ɗan shekara talatin da biyar (35)

A garin Sabarawa, ƙaramar Hukumar Kusada Jihar Katsina

Kamar tsawon minti Hamsin

Ɗan tauri

Ɓ) Musa Leko, ɗan shekara sittin da biyar (65)

A garin Rimaye, ƙaramar hukumar kankia jahar katsina

Kamar tsawon minti Hamsin

Ɗan tauri

ƁI) Isihu Auta, ɗan shekara talatin da uku (33)

A garin Dokoki, ƙaramar Hukumar Kankia Jahar Katsina

Kamar tsawon minti arba'in

Ɗan tauri

ƁII) Sa'adu Gambo, ɗan shekara arba'in da biyar (45)

A garin Nasarawa, ƙaramar hukumar Kankia Jahar Katsina

Kamar tsawon minti talatin

Ɗan tauri

Kuma an yi masu tambayoyi kamar haka:

I.                    Wane kallo ka ke wa Tauri ?

II.                 A faɗi yadda ake yin kirari

III.              Yaushe ka fara yin wasan tauri

IV.              A faɗi ire-iren maganganun da ake cikin kirari

 

 

3.4.5 Jugowa Da Sauraren Hira Da Aka Yi Da Makaɗin Tauri Sale Kudo

Domin samun ganin kammaluwar wannan bincike da kuma samun madosar aikin da sanin yadda za a gabatar da shi, an tattauna da makaɗin tauri Sale Kudo Kusada a gidansa da ke garin magami, tare da yi masa tambayoyi a kan irin salon da ya ke amfani da shi a lokacin da yake waƙa, ko yake so ya taso da wani ɗan tauri cikin fage. An yi amfani da takarda da biro da wayar hannu domin naɗo irin amsoshin da ya bayar. Daga cikin tambayoyin da aka yi masa akwai:

I.                    Ko za ka bamu taƙaitaccen tarihin rayuwarka?

II.                 Shin kana amfani da salo wurin aiwatar da waƙa, musamman sakaya wasu kalmomi?

III.              Ya ka ke yin zuga a cikin waƙoƙin ka?

IV.              Waɗanne abubuwa kafi lissafowa a cikin Waƙoƙin ka?

3.5 Da'ar Gudanar Da Bincike

Wannan bincike ne da aka gudanar cikin natsuwa da ladabi da girmama waɗanda aka je neman bayanan bincike wurinsu. An yi amfani da kalamai masu taushi da sunkuyar da kai domin inganta aikin da ganin an samu ingantattun amsoshin da ake bukata Haka kuma an yi amfani da shiga ta mutunci ta kaya na kamala a lokacin aiwatar da binciken.

Bincike ne da ya gudana cikin ladabi da girmama waɗanda aka je neman bayanai wurinsu.

3.6 Naɗewa

A wannan babi an yi cikakken bayani akan sigar da wannan bincike yake da ita da kuma bayanin kayan aikin bincike sannan an kawo ginshiƙan bayanai da lissafo ɗakunan karatun da aka ziyarta a lokacin binciken haka kuma an yi bayanin tattaunawar da aka yi da masana da manazarta da kuma masu sana'ar tauri. A cikin babin ne aka yi bayanin hira da aka yi da makaɗin tauri Sale Kudo Kusada sannan aka yi bayanin ɗa'ar bincike daga ƙarshe aka naɗe babin da kammaluwa.

Post a Comment

0 Comments