Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Tubalan Turken Zuga A Wakokin 'Yan Tauri Na Sale Kudo Kusada – Kashi Na Biyu

Kundin Digiri Na Biyu (M.A Hausa Culture) Da Aka Gabatar A Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero Kano (Maris, 2024)

Nazarin Tubalan Turken Zuga A Waƙoƙin 'Yan Tauri Na Sale Kudo Kusada

Aminu Musa
07036420021
ameenumusa12@gmail.com

BABI NA BIYU

2.0 Shinfiɗa

A Babin da ya gabata an fahimci cewa manufar wannan bincike ita ce fito da wasu abubuwa da suka shafi halayen rayuwar al'ummar Hausawa, kamar yadda suke zuwa a cikin Waƙoƙin Makaɗin Tauri, sannan kuma aka bayyana cewa aniyar wannan binciken ta ginu ne a kan ganin an ƙara samar da abun bita ga ɗalibai da ƙara fito da waɗansu hikimomi na adon harshe dake ƙunshe cikin Waƙoƙin 'yan Taurin. A cikin Babin ne a ka yi bayanin iyakancewar Bincike tare da kawo irin gudummuwar da binciken zai bayar a cikin al'umma baki ɗaya. A halin yanzu kuma wannan Babi na biyu zai mayar da hankali ne wajen nazartar kaɗan daga cikin tarin abubuwan da masana suka gabatar a kan wannan ɓangare na kirari baki ɗayansa. Kamar yadda yake, sanannen abu ne babu wani fage na ilimi da za a bugi gaba a ce babu magabatan da suka tofa albarkacin bakin su a cikinsa. Ko dai kai tsaye ko kuma a kaikaice wannan dalili ne ya sa aka ce babu wani bincike da zai samu kammaluwa ba tare da an waiwayi hidimomin da magabata suka yi wa wannan fage na ilimi, ba domin kuwa ana cewa, daga na gaba ake gane zurfin ruwa, kuma waiwaye adon tafiya.

Wannan ce ta sa a halin yanzu za a waiwayi masana wannan fage na Al'adun Hausawa da Harshen su da dai sauran fannonin ilimin da suke da alaƙa da wannan bincike domin ganin irin abin da suka faɗi game da Waƙoƙin tauri da salon dake ƙunshe da shi, da ya shafi zuga ko koɗawa da kuma kururuta 'yan tauri.

2.1 Ayyukan Da Suka Gabata

A wannan fage za a kawo bayani ne akan ayyukan masana da manazarta da ɗaliban ilimi waɗanda suke da alaƙa da wannan aiki, kuma za a yi bitarsu domin samun nasarar wannan bincike da aka gabatar. Sannan tun a farko sai da aka kawo tarihin Makaɗin Tauri Sale Kudo da tarihin Kusada waɗanda aka samu daga Nazarin masana.

2.1.1 Kundayen Bincike

Kundayen Bincike su ne binciken nazari na ilimi waɗanda aka gabatar domin samun Digiri na ɗaya ko na biyu ko na uku, saboda ƙoƙarin samun hanyar da za a ɗora wannan bincike ya kai ga nasara, an yi bitar Kundayen bincike kamar haka:

Ammani (2009) a cikin kundin digirinsa na biyu ya bayyana Ma'anar kirari da maganganun azanci, sannan ya yi bayanin ma'anar nazari a cikin kundin binciken sa. Sai dai shi a cikin waƙoƙin Aliyu Ɗan dawo ya kawo. Wannan aiki yana da alaƙa da aikin da za a gabatar musamman ta fuskar maganganun azanci da makaɗan tauri ke furtawa a lokacin da suke waƙoƙin tauri. Aikin yana da bambanci da wannan Bincike domin shi ya taƙaita ne akan maganganun azanci, wannan kuwa zai mayar da hankali ne akan adon harshe a cikin kirari Wanda shi ma salo ne na azanci a cikin waƙoƙin tauri. Aikin na Ammani (2009) zai ba wannan bincike gudummuwa sosai musamman wajen ganin irin yadda salo ya ke a cikin waƙa da kuma yadda salon ke zuwa da yadda ake aiwatar da shi.

Sharifai (1990) a cikin kundin digirinsa na biyu ya kawo Ma'anar kirari da rabe-rabensa, da bambancin da ke tsakanin Kirari da Take, ya yi bayani akan Ma'anar nazari da kuma gargajiya. Bincikensa na da dangantaka da wannan aiki domin ganin irin yadda ya kawo Ma'anar Kirari da yadda kirari yake zuwa sai dai ya sha bamban da wannan ta fuskar aiwatarwa. Aikin Sharifai (1990) zai zamewa wannan Bincike tamkar fitila da za ta haska masa hanya zuwa ga nasara.

Dogarai (1992) a kundin digirinsa na ɗaya ya yi bayanin Namun Daji a ƙasar Hausa, da ire-irensu da magungunansu sannan ya bayyana yadda Namun Daji suke da bai wa da isharori, da kuma waɗansu magunguna da ake samu daga jikinsu, aikinsa zai tallafi wannan bincike, duba da yadda masu kiɗan Tauri ke kallon halaye da ɗabi'un dabbobi suna danganta ɗan Tauri da su. Aikin yana da alaƙa da wannan ta fuskar amfani da sunayen Namun Daji a cikin kirari domin nuna buyawa ko zugawa. Binciken na Dogarai (1992) wani babban mataki ne da za ai amfani da shi domin ganin kammaluwar wannan bincike.

Ɗangulbi, (2007) a kundin digirinsa na ɗaya ya gabatar da wani kundin bincike mai taken '' Dangantakar Habaici Da Zambo A Cikin Waƙoƙin Baka Wajen Bunƙasa Sarautun Gargajiya A Ƙasar Hausa'' A cikin aikin nasa an kawo Ma'anar Habaici daga bakin Masana sannan aka yi bayanin Ma'anar Zambo kamar yadda Masana da Manazarta suka tofa albarkacin bakinsu akai, sai a ka ci gaba da kawo dangantakar Habaici da Zambo, duk a cikin aikin nasa an yi bayanin yadda Mawaƙan baka ke amfani da salo wajen muzanta Sarakuna da kuma 'ya'yan sarki da yadda suke muzanta Fadawan Sarki tare da kawo misalai daga cikin wasu Waƙoƙin baka na Makaɗa. Wannan aiki ne da yake da 'yar alaƙa da wannan bincike musamman ta fuskar amfani da salo wajen isar da saƙo kai tsaye a cikin waƙa da kuma yadda aka tsara dabarun salon sarrafawa wajen aiwatar da aikin, sai dai akwai bambanci tsakanin aikin da binciken namu kasancewar shi wannan nazari ya mayar da hankalinsa ne akan salon Zuga wadda za a duba a cikin kirarin Makaɗan Tauri Sale Kudo, duk da wannan aikin zai ƙara fito da wannan bincike da yi masa tallafi da misalai na yadda salo yake a Waƙoƙin Makaɗa.

Yusuf (1992) a cikin kundin digirinsa na ɗaya ya bayyana Ma'anar salo da kuma sarrafa Harshe a Hausa , a cikin aikinsa ya bayyana dabarun jawo hankali ya kuma yin nazari a kan Ma'ana ta ɓoye. Haƙiƙa aikin zai ba wannan bincike gudummuwa musamman ta fuskar maganganun hikima da irin yadda ake sarrafa harshe wajen jawo hankali. Aikin ya sha bamban da wannan domin shi ya kawo wasu maganganun hikima ne masu kama da kirari wanda suke da ma'anoni irin na Adon harshe. Aikin zai ba da gudummuwa wajen kammaluwar wannan bincike da ake aiwatarwa.

Zamfara (2020) a cikin kundin digirinta na biyu mai taken '' Salon Kambamawa A cikin Waƙoƙin Kassu Zurmi'' ta kawo Ma'anar salo a cikin aikin nata sannan ta ci gaba da bayanin ire-iren salo inda ta baje kolinta a salon kambamawa, ta yi bayanin salon kambamar zulaƙe da kuma salon kambamar yabo ta kawo misalai na kowane ɗaya a cikin Waƙoƙin da Kassu Zurmi ya yi wa mutane. Wannan aiki na Zamfara (2020) wani babban mataki ne da aka yi amfani da shi wajen ci gaba da wannan bincike duk da cewa sun bambanta domin ita ta gabatar da aikin nata ne a kan kambamawa kaɗai wannan kuma yana magana ne a kan zuga duk da cewa kambamawa ta faɗo daga cikin nau'in Adon harshe kamar yadda wannan bincike ya kasa ta.

Yahaya (1990) a digirinsa na ɗaya ya yi bayani a kan kayan yaƙin Hausawa na gargajiya a cikin aikinsa ya bayyana Ma'anar yaƙi, sannan ya jero waɗansu kayan yaƙi waɗanda suka haɗa da makamai. Sannan ya yi bayanin yadda ake yaƙi da irin ƙaimin da mayaƙa ke samu. Aikinsa zai taimaka wa wannan aiki, wajen ganin waɗansu kayayyaki da Makaɗan Tauri ke amfani da su, da kuma irin yadda suke kallon makaman suna danganta ɗan tauri da su domin zuga shi ko gurza shi. Aikin ya bambanta da wannan bincike domin shi ya yi bayani ne a kan kayan yaƙin Hausawa, wannan kuma zai kalli yadda ake kallon kayan yaƙin a siffanta ɗan Tauri da su. Aikin nasa zai ƙara haskawa wannan binciken hanya domin kai wa ga matakin kammaluwa.

Yusuf (1990) a cikin kundin digirinsa na ɗaya ya gabatar da bayani a kan Maharba, da kuma yadda ake sana'ar harbi, sannan ya kawo waɗansu halaye na Maharba da al'adunsu duk a cikin aikin nasa ya yi ƙoƙarin bayyana shahara da ƙwarewa ta aikin harbi. Wannan bincike zai ƙara mana haske sosai wajen gudanar da wannan bincike, musamman ta fuskar isharori da ɗabi'un masu sana'ar harbi, sannan da ganin irin dangantakar da ke tsakanin Maharba da 'yan Tauri. Aikin nasa yana da bambanci da wannan domin za mu kalli irin yadda ake bayyana Buwaya ko ishara a lokacin da ake kiɗa. Aikin zai ƙara wa binciken haske sosai domin ganin ya kammalu.

Tukur (2001) a cikin kundin digirinsa na biyu ya gabatar da aikinsa a kan ''salon Kambamawa a cikin waƙar Shago ta Ɗan Anace, cikin aikinsa ya kawo Ma'anar salo da kuma ta kambamawa, sannan ya yi bayanin irin yadda ake amfani da azancin magana wajen nuna hikima a cikin waƙa, ya kawo wasu kalmomi masu maganganu a dunƙule da suke buƙatar sharhi. Wannan aiki nasa yana da alaƙa da wannan bincike da ake gabatarwa, musamman ta fuskar amfani da kalmomi cikin salon jan hankali da isar da saƙo da kuma irin yadda ake sarrafa sunayen waɗansu halittu a ƙoƙarin bayyana matsayi na wani. Haka kuma aikin yana da bambanci da wannan domin shi ya taƙaita ne akan kalmomin hikima da ake amfani da su cikin Kirari. Sai dai zai taimaki wannan bincike da samar da waɗansu misalai da za a haɗa domin ganin haƙa ta cin ma ruwa.

Zainab (2013) a cikin kundin digirinta, ta gabatar da bincike a kan ''Ginuwar salo a Waƙoƙin Fiyano '' Ta yi Nazarin dabarun jawo hankali da dabarun salon sarrafawa da kuma gudanar da sharhi mai gamsarwa a kan nazarin kamantawa a Waƙoƙin Fiyano kamar su kamance daidaito da kamance fifiko. Inda ta gano wasu dabarun da ake amfani da su, irin su abuntawa da mutumtawa da dabbantarwa da kuma amfani da Karin magana sannan kuma binciken ya yi bayanin kalmomin aro a Waƙoƙin Fiyano kamar kalmomin Larabci da na Turanci. Binciken nata yana da dangantaka da wannan bincike ta fuskar salo da dabarun sa, sai dai sun bambanta domin shi wannan aiki zai mayar da kai ne a kan Adon harshe a cikin Waƙoƙin Sale Kudo makaɗan tauri.

2.2 Mujallu Da Mukalu

Masana da manazarta sun gabatar da abubuwa da dama waɗanda suka taimaka wa wannan nazari, a wajen mabambantan tarukan ilimi da bincike, shi ya sa aka zaƙulo wasu maƙalu da takardun ilimi a ka yi bitarsu, domin su tallafi wannan nazari ya kai ga nasara daga cikin mujallun ilimi da takardun ilimi da aka yi bitarsu akwai waɗannan:

Yakawada (2010) ya rubuta muƙala mai suna ''Jarunta A Waƙoƙin Baka: Nazarin Waƙar Shago Ta Muhammadu Ɗan Anace'' Wannan takarda ta kawo bayani ne a kan ma'anar jarunta da kuma bajinta, haka kuma ya kawo bayanin salalan da ake amfani da su a waƙa irin su kirari da zambo da makamantansu, sannan an nuna tasirin da kirari yake da shi ga wanda ake yi wa waƙar. Wannan aiki zai taimaka wa wannan bincike musamman wajen ganin yadda kirari yake da tasiri, da kuma bayyana ma'anar kirari, tare da bayanin jarunta kamar yadda yake a wajen masu kiɗan Tauri. Bambanci da ke tsakanin aikinsa da wannan bincike shi ne wannan yana magana ne a kan kirarin Makaɗan Tauri kaɗai. Sai dai aikin zai zamo tamkar wani ginshiƙi da zai tallafi wannan bincike zuwa ga nasara.

Yahya (1998) ya gabatar da Takarda mai taken ''Hikima A Cikin Waƙoƙin Hausa '' ya kawo ma'anar hikima da ire-iren maganganun hikima irin su kirari da habaici da yabo ta yadda Mawaƙa ke sarrafa su a cikin waƙoƙinsu bugu da ƙari ya yi bayani a kan kinaya da zayyana da kaifin ma'ana da sauransu. Aikinsa zai ƙara wa wannan aiki haske musamman wajen ganin yadda ake amfani da adon harshe da sauran dabarun sarrafawa a cikin kirari. Akwai bambanci da wannan aiki domin shi ya kalli kirari da ire-iren maganganun hikima a matsayin su na ɓangaren azanci. Wannan kuma zai kalli kirari a cikin waƙar Tauri. Sai dai aikin wata madogara ce da za ta tallafi wannan bincike domin kai wa ga gaci.

Sayaya (2009) ya kawo ma'anar kirari da Tauri sannan ya bayyana ma'anar salo, ya kuma yi bayanin wasu daga cikin kinayoyin 'yan Tauri. Wannan Takarda za ta taimaki wannan aiki sosai wajen gudanarwa. Sai dai aikin nasa ya sha daban da wannan aiki domin shi ya yi bayani ne akan wasu kinayoyi a kirarin tauri ta fuskoki guda biyu kaɗai, wannan kuma za a yi bayanin adon harshe a cikin kiɗan Tauri. Lallai aikin zai bada gagarumar gudummuwa wajen kammaluwar wannan bincike da ake yi.

Nura (2013) ya gabatar da wata Takarda mai Taken '' Nazarin Amfani Da Saye A Waƙoƙin (Dr) Alhaji Mamman Shata Katsina '' A cikin Takardar ya yi bayanin Al'adar Saye a wurin Bahaushe sannan ya kawo nau'oin Sayen sunan yanka da Saye na kaucewa batsa da Saye na mutuwa wannan Takarda tana da dangantaka da wannan bincike musamman wajen irin yadda ake ɓoye ma'ana ta zahiri da canza ta, da wata da za ta maye gurbinta. Aikin nasa zai taimaki wannan bincike sosai wurin ganin ya kammalu.

Abdul-Ƙadeer(2013) A Takardarsa mai suna '' Nazarin Salon Kinaya A Wasu Waƙoƙin Alhaji (Dr) Mamman Shata Katsina '' ya yi bayanin ma'anar salo da kuma ma'anar waƙar baka, duk a cikin Takardar an kawo ma'anar Kinaya da kuma Kinaya a wasu waƙoƙin Shata.

Wannan aiki na Abdul-Ƙader (2013) yana da alaƙa da wannan aiki, sai dai suna da bambanci domin shi ya kalli Kinaya ne a cikin waƙa wannan binciken kuma zai duba adon harshe a cikin kirari, aikin zai taimaki wannan bincike matuƙa domin cin ma iyaka.

Rabi (2014) ta rubuta wata Takarda mai taken ''Salo A Waƙar Baka Misali Daga Waƙoƙin Makaɗa Maza Da Suka Yi Wa Mata'' a cikin Takardar ta yi bayanin ma'anar Kinaya da kuma ma'anar Salo, sannan ta kawo wasu misalai na Kinaya a cikin waƙoƙin Makaɗa, lallai wannan aiki na Rabi (2013) yana da dangantaka da wannan bincike kuma zai kasance wani tsani da za a tattaka domin ƙara haska wannan bincike zuwa ga nasara.

Satatima (2001) a binciken da ya gudanar a kan Salon Tsarma Karin Magana Cikin Waƙoƙin Siyasa: ya yi tsokaci daga wasu fitattun waƙoƙin Jamhuriyya ta huɗu zuwa yau. A inda aka gano irin yadda Mawaƙa suke amfani da karin magana da dabarun jawo hankali a cikin waƙoƙin su kamar su adantawa da kuma laƙantar Harshe. Wannan bincike na Satatima yana da alaƙa da wannan bincike domin ya yi bayanin ma'anar salo da sauran dabarun sarrafawa, sai dai wannan zai fito da adon harshe ne kaɗai a cikin Kirarin makaɗan Tauri. Binciken zai ƙara haska mana hanya domin kammaluwar wannan bincike.

Mashi (2013) a binciken da ya gabatar a kan ''Birgimar Hankakan Balaraben Salo da Musulmin Zubi Cikin Littafin Ruwan Bagaja '' ya yi nazarin salon barkwanci da bandariya da kuma bada labarin da suka mamaye zubin littafi. A inda ya gano salon bada labari da zai faru ta hanyar mafarki, da kuma tafiye-tafiye zuwa birane da ƙauyuka. A cikin wannan maƙala da Mashi ya gabatar ya yi cikakken bayani a kan abinda ya shafi salon kwatanci kuma ya fito da irin hikimomin da dabarun da marubuci ya yi amfani da su, a wannan bincike kuma za a yi Nazarin sarrafawa da ya shafi zuga a cikin waƙoƙin Makaɗan Tauri, takardar za ta tallafi wannan bincike da kuma ƙara haska masa hanya zuwa ga nasara.

Bishir (2016) ya gabatar da wata Takarda mai taken '' Adon Harshe Bazar Mawaƙa: Nazarin Kwalliya Da Tamka A Wasu Waƙoƙin (Dr) Mamman Shata Katsina. A cikin Takardar ya yi bayanin ma'anar waƙar baka daga bakin Masana, sai ya kawo bayanin Adon Harshe tare da warware ma'anarsa, sannan ya kawo bayanin kwalliya da ya kira da wata dabara ta siffantawa wadda ake ɗaukar darajar wani abu a ɗora wa wani abu ba tare da wani tsakani ba. Haka kuma ya kawo misalan irin wannan salo na kwalliya a cikin wasu baituka daga waƙar Shata domin ƙara fito da siffantawa fili. An kawo bayanin Tamka wadda ya kira da Kinaya kamar yadda za a iya kwatanta salon amfani da kwalliya a cikin waƙa. Duk a cikin wannan takarda an kawo irin wannan kinaya daga cikin Waƙoƙin (Dr) Mamman Shata Katsina.

Lallai wannan Takarda ta Bishir (2016) za ta bayar da gagarumar gudummuwa wajen wannan bincike da ake aiwatarwa domin irin alaƙar aikin da binciken ta fuskar salon siffantawa da kuma kinaya duk da cewa shi ya kira kinaya ne da Tamka, aikin ya ƙara ɗora mu hanya domin ƙara fahimtar yadda ake kawo misali da suka shafi Kinaya a cikin waƙa. Sai dai akwai bambanci tsakanin aikin da ake aiwatarwa da binciken nasa domin shi ya yi nazarinsa a kan Adon Harshe ne a cikin waƙa, wannan kuma na maganar adon harshe a cikin kirari.

Usman (2014) ya gabatar da Takardarsa mai Taken '' Gargaɗi Ga Kyautata Zamantakewa: Daga Alƙalamin Isan Kware Ɗan Shehu a cikin wannan Takarda ya kawo bayanin wasu keɓantattun kalmomi da aka yi amfani da su a Takardar da kuma manufar yin Nazarin sannan kuma ya kawo bayani a kan salo da nau'oi'nsa inda aka taɓo siffantawa da ya ce; kwatance ce da ta shafi kamantawa domin daidaito tsakanin abubuwa guda biyu kai tsaye sannan dabara ce ta jawo hankali ta hanyar ɗaukar wani abu a ce shi ne wani abu. Duk a cikin takardar an kawo wasu dabarun salon da suka haɗa da Alamtarwa da kwatantawa da Jinsintarwa da kuma Kinaya. Wannan bincike na Usman (2014) wani babban jigo ne da zai tallafi wannan bincike da ake aiwatarwa domin sun yi tarayya a wajen salo da kuma yadda ake sarrafa salo a cikin abunda ya shafi waƙa ko rubutu. Duk da cewa akwai bambanci tsakanin aikin da wannan bincike domin shi wannan bincike yana bayani ne a kan abunda ya shafi adon harshe a cikin kirari ne.

2.3 Bugaggun Littattafai

Bugaggun Littattafai su ne binciken da aka gabatar aka kuma mayar da shi littafi, a ƙoƙarin gano hanyar da za a ɗora wannan bincike ya kai ga nasara an yi bitar Littattafai kamar haka:

Ɗangambo (2007) ya wallafa littafinsa mai suna Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa (sabon tsari) a cikin littafin an kawo bayani sosai a kan salo da sauran dabarun sarrafawa da suka haɗa da kamantawa da jinsintarwa da sauransu, haka kuma an kawo bayanin wanzuwar waƙar baka.

Wannan Littafi ya daɗa ba ni haske a kan ƙara fahimtar dabarun salon sarrafawa a cikin waƙoƙi tare da ƙara fahimtar yadda ake amfani da salo a cikin waƙa, littafin ya taimake ni sosai a wannan buncike da nake gabatarwa, musamman yadda ya kawo salon kamantawa da na kwantatawa tare da jinsirtawa a cikin nau'in sauran dabarun salon sarrafawa Wanda a ciki Kinaya ta fito ta yadda bayanin ya ƙunshe ta a kaikace ta yadda ake ɓoye ma'ana ta fuskar musanya ta da wata wadda za ta zauna a madadinta. Lallai littafin wani ginshiƙi ne da ya ƙara samar da haske wajen fahimtar kambamawa da kuma yadda ake amfani da ita a cikin waƙa duk da shi wannan aiki yana magana ne akan Adon harshe a cikin Waƙoƙin Makaɗan Tauri Sale Kudo Kusada.

Isma'il da Wasu (2008) Darussan Hausa A Kammale, a cikin littafin an kawo bayanin Habaici da zambo da sauran maganganun azanci na hikima, Wanda ke ƙunshe da saƙonni domin nuna ishara. Wannan littafi yana da alaƙa da wannan aiki musamman ta yadda ake samun salon sarrafa magana da kuma dabarun jawo hankali, littafin zai ƙara ba mu haske sosai wajen fahimtar irin maganganun da Makaɗan Tauri ke furtawa a cikin kirarin su a lokacin da suke kiɗa.

Ƙamusun Hausa(2006) Jami'ar Bayero kano a cikin littafin an yi bayanin Ra'i sannan kuma an kawo ma'anar Kinaya, lallai littafin ya ba wannan bincike gudummuwa da ƙarin haske wurin ganin haƙa ya cim ma ruwa.

Yahya (2016) ya rubuta wani Littafin sa mai suna '' Salo Asirin Waƙa'' a cikin wannan Littafi an yi bayanin salo ta fuskar ma'ana da kuma kawo wasu sauran dabarun salon sarrafawa da suka haɗa da kinaya da kamance da siffantawa da jinsirtarwa da zayyana da kuma Alamtarwa sai kuma kambamawa da sauransu wannan ya sa aka fahimci kinaya tana cikin rukunin nau'in salon sarrafawa da ake amfani da ita a cikin waƙa ko rubutu ko kuma kirari da sauran hanyoyin isar da saƙo domin yi masa kwalliya yadda zai ƙayatar da mai sauraro ko karantawa. A cikin wannan Littafi an bayyana kinaya da cewa '' kiran abu musamman mutum da sunan da ba shi ne nasa da aka san shi da shi ba, domin wannan suna ya bayar da ma'anarsa da kuma tunanin da ma'anar za ta kawo zuwa ga abunda aka kira da wannan suna. Haka kuma aka ci gaba da kawo sharhi na Kinaya da sauran dabarun salon sarrafawa tare da misalai a cikin bayani. Wannan littafi na Yahya (2016) Littafi ne da ya taka rawa sosai domin kammaluwar wannan bincike da ake aiwatarwa musamman idan aka yi duba da yadda aka warware kinaya dalla-dalla. Duk da cewa littafin ya karkata ne a kan waƙa shi kuma wannan bincike ana gudanar da shi ne akan kirari.

Gusau (2005) a cikin littafinsa mai suna ''Makaɗa da mawaƙan Hausa '' ya yi bayanin yadda mawaƙan Hausa suka rabu, ya kasa Littafin har kashi huɗu, kashi na ɗaya makaɗan yaƙi, kashi na biyu Makaɗan Sarakuna kashi na uku Makaɗan Jama'a kashi na huɗu Makaɗan sana'a.

Aikin nasa ya bayar da gudummuwa sosai wajen kammaluwar wannan bincike musamman irin yadda aka taɓo Makaɗan yaƙi da yadda aka gabatar da bayani akan su da irin yadda suke aiwatar da kiɗan, sai dai Littafin yana da bambanci da shi wannan bincike domin shi ya taƙaita ne a kan Makaɗan Tauri kawai da kuma nazartar salon Kinaya a cikin kiɗan na Tauri.

2.4 Ra'in Da Za a Ɗora Bincike

An zaɓi a ɗora wannan nazari ne a kan Ra'i na waƙar Baka Bahaushiya wadda Farfesa sa'idu Muhammad Gusau ya samar a shekarar (1993).

Wannan Mazahaba ta yaɗu a cikin aikace-aikacen Masana musamman ɓangaren da ya shafi nazarin waƙoƙi da maganganun baka. Manufofin wannan ra'i sun haɗa da;

I.        Tana kimanta duniyar ɗan Adam da abinda ke faruwa a cikinta da son bayyana su yadda ya dace.

II.     Tana Sauƙaƙa salon magana da hoton tunani da ƙara mayar da kai a kan halin abubuwa dake wakana a cikin al'umma.

III.  Tana nuna faruwar abubuwa a zahiri, kamar wahala da muzgunawa da yadda ake faɗarsu daidai wa daida.

IV.  Tana fito da abinda ya faru ko yake faruwa, ba wanda ake buri ba ko wanda akai ra'ayi ba.

2.5 Dangantakar Ra'in Da Bincike.

Wannan Ra'i na waƙar baka na da dangantaka da wannan bincike duba da yadda yake da manufa ta hanyoyin zamantakewar rayuwar al'umma da irin ƙalubalen da rayuwa take zuwa da shi da bayyana dabarun da ke cikin maganganu da ake furtawa a cikin zamantakewa ta yau da kullum. Shi kuma wannan bincike na ƙoƙarin bayyana yadda ake kallon halaryar waɗansu abubuwa kamar dabbobi da tsirrai da ƙwari ana alaƙanta su da rayuwar al'umma ta hanyar fayyace salon hoton rayuwa ta zahiri a cikinsu kamar yadda wannan Ra'i ya bayyana.

2.6 Naɗewa

Wannan babi an bayyana abubuwa da suka haɗa da bitar ayyukan Magabata da suka haɗa da Mujallu da Muƙalu da kuma Bugaggun Littattafai, an yi bayanin ma'anonin salo da na kirari da tauri da kuma Ra'in da aka ɗora aikin a kansa sannan aka yi bayanin dangantakar Ra'in da shi aikin da aka gudanar. 

Post a Comment

0 Comments