Nazarin Tubalan Turken Zuga A Wakokin 'Yan Tauri Na Sale Kudo Kusada – Kashi Na Hudu

    Kundin Digiri Na Biyu (M.A Hausa Culture) Da Aka Gabatar A Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero Kano (Maris, 2024)

    Nazarin Tubalan Turken Zuga A Waƙoƙin 'Yan Tauri Na Sale Kudo Kusada

    Aminu Musa
    07036420021
    ameenumusa12@gmail.com

    BABI NA HUƊU

    4.0 Shinfiɗa

    Wannan babi za ya yi bayani akan salon sarrafa Harshe da Makaɗin Tauri Sale Kudo Kusada yake amfani da shi a lokacin da yake yi wa ɗan tauri waƙa. Babin zai mayar da hankali a kan wasu fasalce-fasalce na Kamantawa da ta haɗa da na daidaito da na fifiko da kuma na gazawa, da kambamawa wadda ta haɗo da kambamar zulaƙe da kuma ta yabo, sai Kamantawa da Alamtarwa da kuma Dabbantarwa. A cikin wannan babi an kawo wasu misalai na kowane ɗaya daga cikin dabarun Sarrafawa da a ka samu a cikin Waƙoƙin Sale Kudo da irin yadda yake zuga ɗan tauri da ƙara masa ƙaimi ta yabonsa, domin ya ƙara fito da ƙarfin maganinsa.

    4.1 Tubalan Gina Turken Zuga a Waƙoƙin Tauri na Sale Kudo kusada

    A waƙoƙin Sale Kudo ya yi amfani da tubalan gina turken zuga wajen wasa da kambama 'yan tauri da ma wasu daga cikin fitattun mutane da suke da alaƙa ko da Tauri ko abokantaka da masu taurin. Wasu daga cikin ire-iren tubalan sun haɗa da tubalan turken kamantawa da tubalan turken dabbantarwa da tubalan turken siffantawa da makamantansu.

    4.2 Tubalan Kamantawa

    Gusau (2007) kwatantawa wata dabara ce wadda ake kwatanta abubuwa biyu dangane da wasu darajoji da za su iya zama na daidaito ko na fifiko ko kuma na kashi. A lokacin da ake wannan za a yi amfani da wasu kalmomi da ke nuna kamancin a fili da ake kira kalmomin Kamantawa ko kalmomi na tsakani Misali kamar da tamkar da awa da kuma da sai kace da daidai da ɗara da kasa da gaza da wane da babu kamar da bai kai da makamantan waɗannan kalmomi da yawa.

    Ɗangambo (2007: 43) Ya bayyana Kamantawa da cewa dabara ce da akan kwatanta abubuwa biyu (ko fiye) masu halaye iri daban, a kwatanta su. Shi kuwa, Abba da Zulydaini (2000: 114) sun bayyana kamantawa da cewa '' wata hanya ce ta jawo hankali da mawaƙan baka suke amfani da ita wajen kwatanta abubuwa biyu mabambanta halaye ko daraja"

    Daga waɗannan bayanai za a fahimci cewa, a dabarar jawo hankali ta kamantawa ana kawo abubuwa biyu ko fiye, masu mabambantan matsayi ko daraja ko halayya sannan sai a gwada su da nufin bayyana matsayin ɗaya a kan ɗan uwansa. A yayin kwatantawar, kamancen na iya zama ɗaya daga cikin ukun nan; kamanci na daidaito ko na fifiko ko kuma na gazawa. Ɗangambo (2007 : 43) Duk Wanda aka ɗauka daga cikin ukun nan za a iya kamanta abubuwa biyu ko fiye a ƙarƙashinsa.

    Misali:

      Jagora: Yaro baya kucciya yai shaho

      : Babbaƙu Iyalan Gwamna

      : Baƙi mai kama da ganyen Shayi

      : Mai son baƙi ya babbaka na sa

      : Kowa ya yi baƙi yai tsoro....

    (Sale Kudo Kirarin Iro Ɗan baiwa)

     

    A wannan diyan kirari Sale Kudo ya yi amfani da dabarar kwatantawa inda ya kamanta sifar jikin Iro da launin ganyen shayi, abunda yake son nunawa anan Iro dan Tauri ne da yake da amfani sosai a fagen tauri ya dubi yadda ganyen shayi yake a ido kamar abun ƙyama ko wani abu na watsarwa amma yana da amfani da cewa shayi baya haɗuwa ya amsa sunan sa sai an haɗa shi da ganyen shayi. Kalmar ''kama'' ita ta fito da wannan kamanci a wannan kirari. Sale Kudo ya bayyana cewa irin yadda Iro yake da ruwa da tsaki a harkar tauri shiyasa ya dubi irin yadda ganyen shayi ke taka rawa a wurin yin shayi a kamanta Iro da shi.

    4.2.1 Tubalan Kamanci Na Daidaito

    Abba da Zulydaini ( 2000:114) Sun ruwaito Gusau (1993) ya bayyana kamantawa ta daidaito da cewa ita ce, kwatanta abubuwa biyu mabambanta, sannan sai a daidaita su ta hanyar nuna cewa, babu wanda ya fi wani. Ke nan, kamanci na daidaito dabara ce ta kwatanta abubuwa biyu domin nuna daidaiton matsayi ko daraja ko halayya ko sifa ko dai wani abu makamancin wannan a tsakaninsu. A irin wannan kamanci na daidaito akwai wasu kalmomi da a kan yi amfani da su, irin su kamar da daidai da shi ne da tamkar da kama da sauransu ( Isah 2021: 212) A kwai dinbin kirari na Sale Kudo da suka zo da irin wannan dabara ta kamanci.

    Misali 1

      Jagora: Faduwa daidai da zama na Amadu

    : Ƙodago sha murza

    : Uban muhamman sani

    ( Sale Kudo kirarin Sarki Gambo)

    A wannan kirarin akwai dabarar kwatantawa ta daidaito kalmar "daidai " ita ta fito da kamancin a cikin kirarin abunda Sale Kudo ke nufi anan dama cen Sarki Gambo bashi da tausayi kuma baya ɗaukar raini to kuma sai ya tsunduma cikin harkar tauri. Shikenan sai ya rikice ya gagara. Kamar yadda kudo ya bayyana Sarki Gambo mutum ne da yake farauta da sana'ar harbi da saida sassan jikin dabbobi kuma sai ya faɗa cikin harkar tauri har ya kai ya shahara ya samu sarauta ta sarkin ƙyarma wannan dalili yasa yake masa kirari da faɗuwa daidai da zama na Amadu uban Tijjani.

    Misali 2

    Jagora: Dan maraƙi baka San galma ba

    : Mai bada magani a ji sauƙi

    : Goga kasan hanya

    : Mai bugu kamar da bakin Wuta.

    (Sale Kudo kirarin Sarkin Dawa Zubairu)

    A wannan kirari ma a kwai kamanci na daidaito kuma kalmar "kamar" ita ta fito da kamancin daidaiton a kirarin abunda Kudo ke nufi anan Hannun sarki Zubairu dafi gare shi tsume yake da asiri muddun yayi duka da shi lallai za a sha wuya shiyasa ya kwantata shi da bakin wuta wato busasshen itace da wuta ta ci ta rage. Ya bayyana cewa hannunsa kamar faskaren itace yake bai taɓa duka ba, ba a kai ƙasa ba ko a ka ji mummunan rauni wannan yasa ya kamanta hannunsa da itace bakin wuta.

    Misali na 3

    Jagora: Irin kumbo irin kayanta

    : Allah ya ji ƙan Sarki

    : Kowa yay bara ya huta

    A wannan kirari na Sale Kudo akwai kamanci na daidaito domin ya kamanta Isihu Auta da Babansa da Allah ya yi wa rasuwa inda yake kamanta Ayyukan sa da na mahaifinsa. A nan ya dubi irin yadda yake tafiyar da sha'aninsa na tauri ya Kira sa da kamar kumbo kamar kayanta kalmar iri anan ita ta fito da kamancin daidaito a cikin kirarin. Kudo ya bayyana cewa gaba ɗaya halayen baban Isihu da yanayin da yake tafiyar da Taurinsa salon iri ɗaya ne da na mahaifinsa.

    Misali na 4

    Jagora: Mai Jan zuga kamar Gwano

    : Na Zainabu Abu

    : Gizago mai ɗamar yaƙi

    A wannan kirari akwai kamanci na daidaito inda makaɗin ya dubi irin yadda gwano ke yin Jeri yana tafiya ya kamanta Iro da shi ganin irin yadda yake shiga gaba sauran 'yan tauri su biyo shi a baya, kalmar kamar anan ita ta fito da kamancin da ake magana. Iro ya kasance uban tafiya ko sarkin zuga duk sadda za a yi tafiya Iro ne a gaba kuma ko gayyata za a yi wurin wasan tauri Iro ake gaya mawa ya tattaro sauran 'yan tauri wannan yasa aka kamanta shi da gwano.

    4.2.2 Tubalan Kamanci Na Fifiko

    Kamanci na fifiko dabarar jawo hankali ce da ake gwada ( kamanta) abubuwa biyu da nufin fitar da Wanda ya fi a tsakanin su.( Auta 2017: 165) wannan fifiko da ake son fitarwa ana kallon sa ne ta fuskar matsayi ko hali ko daraja ko kuma duk wani mizani ko ma'auni da aka ɗora abubuwan biyu akai. A kwai kirare-kiraren Sale Kudo Kusada da suke da irin wannan kamanci.

    Misali 1

    Jagora: Kan kara kafi ɗaka

    : Kowa ya yunƙuro a bar ma shi

    : Na doguwa ɗan mutan Sabarawa

    ( Sale Kudo kirarin Sarki Zubairu)

    A nan an yi amfani da dabarar jawo hankali ta kamancin fifiko abunda makaɗin ke nunawa sarki Zubairu ya shahara a fagen tauri har ta kai ba kowace karamar tawaga yake shiga ba shiyasa ya kamanta shi da kan kara wato damin kara wanda yafi ƙarfin a sa shi cikin ɗaki. Anan shahararsa ce ta sa ya kamanta sa da Kan kara yana nufin ya zarce sauran 'yan tauri. Kudo ya ce ba kowace tafiyar Tauri ba ce ake yinta da Zubairu sai babbar tafiya wacce ba kowa ne ɗan tauri ne za a samu a ciki ba.

    Misali 2

    Jagora: Sarki Gambo ja gabanka su bika

    : Jan mutum na yamma da birni

    : Marga-margan dutse kafi gaban aljihu

    :Kai ke farkewa maza laya.

     

    (Sale Kudo Kirarin Sarki Gambo)

    A wannan kirari na Sarki Gambo an yi amfani da kamancin fifiko ta hanyar kwatanta abubuwa guda biyu wajen bayyana girman wani ɗan Tauri, wato irin shahararsa da ƙarfin maganinsa. In da aka nuna cewa girman sa ya fi ƙarfin wani ƙaramin ɗan Tauri ya tare sa bare ya ce zai ja da shi. Shi yasa aka ce marga-margan dutse kafi gaban aljihu wato yafi ƙarfin ƙananan 'yan Tauri. Daga wannan misalan za a ƙara fahimtar kirarin Tauri su na ɗauke da dabarar jawo hankali ta kwatanta abubuwa biyu tare da fito da wanda ya fi a tsakanin su. ( Kamancin fifiko).

    Misali 3

    Jagora: Sahun Giwa danne na Rakumi

    : Madugu uban tafiya

    : Kai bugu a ce mota ce

     

    (Sale Kudo Kirarin Sarki Gambo)

    A wannan kirari Makaɗin ya kamanta Ɗahiru da cewa shi kamar giwa ne a cikin daji duk yadda ake ganin girman ɗan tauri da ƙoƙarin sa kafin shi ya zo ne, wato shahararsa ta zarce ta sauran 'yan tauri shi yasa ya kamanta sa da sahun giwa Wanda ya danne na rakumi, kalmar dannewa a nan ita ta fito da kamancin fifikon da ake magana. Kudo ya bayyana cewa sihiri irin na ɗahiru ba kowane ɗan tauri ke da shi ba, ko a wurin wasa in ba an nemi sasanci da shi ba ya kan warware taurin wasu 'yan tauri domin nuna ƙarfin na sa.

    Misali 4

    Jagora: Bahago taushe dama

     : Na sabon rafi sai dubu

     : Sai gayya

    (Sale Kudo Kirarin Sarki Gambo)

    A nan ma akwai kamanci na fifiko domin mawaƙin ya kamanta yadda hagun Sarki Zubairu ke taushe dama wato aikin bajintarsa ya fi na ba damen mutum. Irin hatsabibancinsa da taurinsa ya zarce misali domin ba kowa ke tararsa ba a fagen daga wannan dalilin yasa Kude ya Kira sa da Taushe dama. Zubairu da hagu yake aiki amma irin zafin namansa da ƙoƙarin sa ya fi na wanda ke aiki da hannun dama wannan dalili yasa ya kamanta hannunsa na hagu da hannun wasu na dama.

    4.2.3 Tubalan Kamancin Gazawa (Kasawa)

    Dangane da kamancin Gazawa ga abin da Auta ( 2017: 165) ya ce, a kan kwatanta abu biyu a nuna cewa ɗaya bai kai ɗan uwansa ba. Wato abin nufi a nan shi ne kamancin na gazawa dabarar jawo hankali ce da ke gwada abubuwa biyu da nufin fitar da wanda bai kai ɗan uwansa ba a tsakanin su. A ƙarƙashin wannan kamanci na gazawa a kan yi ta ne ta fuskar matsayi ko daraja ko hali da sauran su. Akwai kirare-kiraren Sale Kudo Kusada da suke ɗauke da irin wannan kamanci na gazawa.

    Misali 1

    Jagora: Duk kucciyar da bata da gashi 'ya ce

    : Dogo na Musa Leko

    (Sale Kudo kirarin Bahari Canko)

    A wannan kirari na Canko akwai kamanci na kasawa domin ya bayyana duk kucciya da bata da gashi ɗiya ce! Anan abunda yake nufi duk girman ɗan tauri da ƙoƙarin sa muddun bai tanadi asiri ba to lallai banza ne, kamar yadda komin girman kucciya idan bata da gashi ba zata iya tashi ba tana ji tana gani yara zasu danne ta. Wannan kirari na a matsayin habaici da Kudo ke yi a cikin kirarin Buhari Canko domin ya ƙara ba abokan adawarsa tsoro da sanin cewa Canko a shirye yake kowane lokaci.

    Misali 2

    Jagora: Ɗan titi ba shi fin titi

    : Ruwa matar Ɗwaɗo...

     

    (Sale Kudo kirarin Bahari Canko)

    Wannan kirari yana ɗauke da kamancin gazawa idan aka kamanta tsuntsaye guda biyu ta fuskar girmansu, ta yadda da uwa da 'ya duk girman su ɗaya sai dai gogewa da sanin duniya nan ne uwar tafi ɗiyar, an kamanta waɗannan tsuntsaye ne ta fuskar jikinsu domin a nuna 'yan Tauri cewa duk yadda yaro ya girma ko yake tasowa a fagen Tauri, to ya bi a hankali akwai wani shiri na iyayensa wanda bai sani ba kuma duk yadda zai yi ba zai kai su ba a fagen Daga. Wannan kamanci ne na gazawa. A tare da wannan akwai jan hankali da nuni ga sauran 'yan tauri na su kiyayi manya duk yadda suke ganin sun taso lallai akwai wani shiri da ba su san da shi ba na tsofaffin cikinsu.

    Misali na 3

    Jagora: Audu su barka sai ta Allah

    : Ka zama buhun ƙasa sun gaza ɗauka

    : Na Amadi Mai roba

     

    (Sale Kudo kirarin Bahari Canko)

    Sale Kudo ya kamanta Audu da buhun ƙasa mai nauyi a cikin wannan kirari yana nuna irin yadda yake da ƙarfi da shahara ta yadda sauran 'yan tauri ba su haye mashi bare har su gabza a fagen daga. Wannan kamanci ne na gazawa ta yadda ba su iya tararsa yayi masu zarra.

    Misali na 4

    Jagora: Tafkin barkono baka ratsuwa gun mata

    : Dogo mai raba gardama da takobi

     

    An yi amfani da kamancin gazawa a wannan kirari domin an nuna yadda mata basu iya shiga cikin tafkin barkono. Abun nufi anan shi ne Iro ya kai hatsabibi ta yadda ba kowane mai sana'ar tauri bane zai iya tararsa bare har yace za su buga, Kudo ya kamanta Iro da tafki cike da barkono anan kalmar baka ratsuwa ita ta fito da gazawar da ake magana a cikin aikin.

     

     

     

     

     

    4.3 Tubalan Kambamawa

    Masana da Manazarta da dama sun bada ma'anar salon Kambamawa.

    A Ƙamusun Hausa (2006). Kambamawa ita ce idan mawaƙi ya yi zuƙu cikin magana ko ya ƙara mata gishiri, a taƙaice ya bayyana abu fiye da yadda yake, a nan zamu ce wannan mawaƙi ya yi amfani da salon kambamawa.

    Yahaya, ( 2001:95) Idan muka tattara Waƙoƙin soyayya zamu ga cewa mawallafa waɗannan Waƙoƙi suna amfani da salon kambamawa ne, musamman kambamar zulaƙe domin su bayyana masoyiyarsu tafi ta kowa, haka Sale Kudo yana amfani da irin wannan kambamawar a cikin kirare-kiraren sa.

    Misali na

    Jagora: Sarki Uban Amadu Uban Tijjani

    : Ƙaramin rauni ake rufewa da ɓawon gwanda

    : Kai naka sai lahira ake nunawa

    (Sale Kudo Kirarin Sarki Gambo)

    Wannan mawaƙi a nan ya yi kambamar zulaƙe, don ya bayyana cewa gogan nasa ya fi kowane ɗan tauri domin idan sauran 'yan tauri suka yi sara a daji akan samu ɓawon gwanda a rufe kafin a zo gari ko wurin masanin rauni. Sai ya ce shi saran sarki Gambo muddin ya yi shi to sai mutuwa kawai, shi yasa ya ce sai dai lahira ake nunawa.

    4.3.1 Tubalan Kambamar Zulaƙe

    Ita ce idan mawaƙi ya yi zuƙu cikin magana wato ya ƙara mata gishiri, a takaice za a ce wannan mawaƙi ya yi amfani da kambamar zulaƙi ( Yahaya 2001: 95)

    Sale kudo ya yi amfani da wannan salon na kambamar zulaƙe a cikin wasu kirare-kiraren sa. Bisa ga ƙa'ida bahaushe Allah kaɗai yake cewa Mai duka, Mai bisa, Mai komi, Mai kowa, idan aka yi amfani da ita ga wani bawa daga cikin bayinsa an yi Kambamawar Zulaƙe ( Bunza 2009).

    Misali na 1

    Jagora: Gizako mai ɗamarar yaƙi

    : Zaki mai zarin ƙarfi

    : Uban Amadu Uban Tijjani

     

    ( Sale Kudo: Kirarin Sarki Gambo)

    A wannan kirari akwai kambamar zulaƙe, kamar yadda ya kambama Sarki Gambo ya Kira shi da 'mai zarin ƙarfi' wato ya kambamashi fiye da yadda yake domin ya nuna cewa ya fi kowa ƙarfi a cikin sauran 'yan tauri.

    Misali na 2

    Jagora: Rigimar Duniya Bature da gwado

    : Ibilishin Mutum na Sarki Gambo

    : Dubu jiran Mutum guda

     

    (Sale kudo: kirarin Bahari Canko)

    An yi amfani da salon kambamawar zulaƙe wajen kiran Bahari da Ibilishin mutum, wato an nuna hatsabibancinsa da haɗarinsa fiye da yadda yake a zahiri. Wannan kambamawar zulaƙe ce. Haka a wurin 'Rigimar Duniya Bature da Gwado' nan ma kambamar zulaƙe ce, domin an nuna irin yadda bala'i ya kai kamar yadda ba a Saba ganin Bature lullube da mayafi ba, to duk sadda aka ganshi da shi abun ya kai inda ba a so wannan kambamar zulaƙe ce.

    Misali na 3

    Jagora: Wuya ko da magani ba daɗi

    : Yaro kauce

    : Sama ta rikito ƙasa ta rikito

    : Amadu ya tare da tafin hannu.

     

    (Sale Kudo kirarin Amadu Nijar)

    A wannan kirari akwai Kambamar zulaƙe wurin da makaɗin taurin ke cewa sama ta rikito kasa ta rikito amma Amadu ya tare da tafin hannu. Abinda Kudo ke san nunawa dangane da Amadu shi ne a fagen tauri baya tsoron shiga kowace irin fitina kuma duk yadda za a haɗa tawagar 'yan tauri komi hatsabibancinsu Amadu zai ratsa kuma zai fita cikin salama.

    Misali na 4

    Jagora: Auta baka son faƙo

    : Kafi mota sauri

    : Sai dai tafi ka kukan banza

     

    (Sale Kudo: kirarin Isihu Auta)

    Wannan Kirari ne mai cike da Kamabamar zulaƙe babu yadda za ayi mutum ya fi mota gudu amma kudo cikin kirarin Auta ya yi wannan kambamen. Abun da Kudo ke nufi anan kamar yadda ya ce Isihu ɗan tauri ne mai zafin nama da gaggawa musamman a lokacin da akai kisa. Wani dalilin kuma ya ce baya gajiya a wurin farauta yana da sauri na zuwa wurare da ake farauta.

     

     

    4.3.2 Tubalan Kambamar Yabo

    Dabara ce ta jawo hankali fiye da ƙima. Hanya ce ta kambama abu fiye da yadda hankali zai amince. A kan yi amfani da wannan dabara, musamman domin yin yabo. Ana nuna cewa mutum yayi wani abu, wanda a zahiri ba zai yiwu ba, ko ya mallaki wani abu da zai iya mallaka ba.( Sarbi, 2007).

    Misali 1

    Jagora: Canko mai raba gardama ga mazaje

    : Arne na bayan soro

    : Mai bada magani aji Sauƙi

     

    (Sale Kudo: kirarin Bahari Canko)

    Wannan kalma ta 'Arne' tana nufin zaƙaƙuri ko jajirtacce ko ma 'iyi anan Kudo ya Kambama shi da wannan kalma ta mai taurin zuciya mai ƙwazo anan an yi kambamawar yabo.

    Misali 2

    Jagora: Nomau ne amma ko abun tuwo ba shi da shi

    : Kahiri karen burtu na Leko

    : Yanzu kau Karen Mallam ne

     

    (Sale Kudo: Kirarin Isihu Auta)

    A cikin wani ɗan kirari ana nuna cewa Sale Kudo ya yi amfani da Kambamar yabo inda yake yabon gwarzonsa da kalmar. 'Kahiri ' a addinance tana nufin Wanda bai da addini a kuma wani ƙaulin tana nufin mai ƙarfin zuciya anan Kudo yayi amfani da kambamar Yabo. Wata kila hakan ya faru ne kasancewarsa bakatsine domin zagi na cikin hanyoyin yabo a wurin su.

    Misali na 3

    Jagora: Mai ɗamarar faɗa

    : Na indo A'i

    : Ka tsare gida ka tsare daji

    (Sale Kudo: kirarin Musa Leko)

    A wannan kirari akwai kambamar yabo kamar yadda aka kambama Musa aka nuna yadda ya yi kaka-gida a fagen tauri har ta kai duk abunda za a yi na tauri a cikin garinsa dole su ne a gaba, haka idan gayyata ce aka kawo ta biki ko wasan tauri shi ne ake samu. Saboda haka '' ka tsare gida ka tsare daji '' kambamar yabo ce domin babu yadda za a yi mutum ɗaya ya iya tare gari guda ko kuma daji.

    Misali na 4

    Jagora: Ka ga baƙin mutum

    : Shawara da Burtai soja

    (Sale Kudo: kirarin Manaja)

    A wannan kirari Sale Kudo ya yi amfani da kambamar yabo inda ya kambama Manaja ya nuna cewa shi da Burtai aminan juna ne har shawara suke tare Wanda a zahiri Manaja ko ganin Burtai bai taɓa yi ba, ya yi haka ne domin ya nuna irin yadda Manaja ke da zafi da ƙarfi shi ne ya haɗa shi da soja.

    4.4. Tubalan Alamtarwa

    Ɗangambo (2007) ya bayyana Alamtarwa da cewa dabara ce ta bayyana wani abu ta hanyar ba shi wata alama wadda za ta tsaya a maimakonsa. Makaɗin tauri Sale Kudo kan yi amfani da wannan dabara a cikin kirarinsa ya kalli wasu abubuwa da suke da wata ɗabi'a kamar ƙarfi ko tsoro ko haƙuri a ce wani ɗan tauri ne ko a kawo wata manufa ta abubuwa a ɗorawa ɗan tauri. Lallai Kudo ya kan yi wannan a cikin kirarinsa.

    Misali

    Jagora: Mu duba mu gani

    : Yaro yasan baƙon gidan Barau

    : Awartaki makama zafi

    : Jifa mai watsa mutane

    (Sale Kudo: kirarin Sarkin Ƙyarma)

    A wannan kirarin Kudo ya ɗauko wasu alamomi na ɗabi'ar awartaki da ta jifa ya danganta su da Sarkin ƙyarma, domin ya nuna yadda yake da shahara da bajinta musamman idan an lura da yadda awartaki yake da jure wuta sai ya kira sarki da awartaki. Sannan ya Kira shi da jifa domin irin yadda yake tarwatsa mutane.

    4.4.1 Tubalan Alamtarwa ta Amfani Da Abubuwa Marasa Rai

    Wannan sashe za ya kawo abubuwa waɗanda suka kasance marasa rai amma su ire-iren su ba dabbobi ba ne kuma ba tsuntsaye ba ne. Wato wasu abubuwa ne da ka iya kasancewa sassan jikin dabba ko wani tsiro ko dutse ko wani abu maimakon hakan. Shi ma irin wannan salo hanya ce da makaɗin tauri ke la'akari da halaye ko kwarjini ko martaba ko isa a Alamta ɗan tauri da su. A kan yi hakan ne domin a tsorata abokan gogayya ko tunzura su domin su kawar da tsoro ko shakku su kasance suna iya tunkarar duk wata kwamacala. Aiki sai mai shi bari mu duba wasu kirari na Sale Kudo domin mu ga ko za a samu abun guzuri.

     

    Misali

    Jagora: Audu kai mai roƙo

    : Mu duba mu gani

    : Yaro yasan Baƙon gidan Barau

    : Awartaki makama zafi

    : Jifa mai watsa mutane

    : Gudu hana kaya

     

    (Sale Kudo: kirarin Sarkin Ƙyarma)

    A wannan kirari Kudo ya ɗauko wasu alamomi na ɗabi'ar awartaki da ta jifa ya danganta su da Sarkin ƙyarma, domin ya nuna yadda yake da shahara da bajinta musamman idan aka yi lura da yadda awartaki ke jure wuta sai ya Kira Sarki da Awartaki. Sannan a wani wurin sai ya kalli yadda jifa ke watsa mutane ya ba Sarki wannan alama don ya ƙara fito da ƙoƙarin sa a fannin Tauri.

    Misali 2

    Jagora: Ba kura bin kare ɗan Audu

    : Mai gidan mutanen kanya

    : Ƙodago a taka a kare

    : Tsohon Biri na bakin Kogi

     

    (Sale Kudo: kirarin Sarkin Ƙyarma)

    A nan ma ya kalli wata alama da Ƙodago yake da ita na ƙarfi da ƙin fasuwa da ganin duk Wanda ya taka shi ba daidai ba ya gulle, yana iya yin rauni. Sai ya ba Sarki wannan alama domin ya nuna ƙarfin maganinsa. Kudo ya bayyana cewa Sarkin ƙyarma ɗan tauri ne mai wahalar kai ba kowane ɗan tauri ba ne ke da tambaya irin ta shi duk yadda ka kai ga tauri muddun kuma gauraya zai iya yin kaca-kaca da mutum.

     

    Misali na 3

    Jagora: Ƙasar Kabari kowa ya gan ta ya tuna Allah

    : Goga kasan hanya

    : Na ɗan isan katsina

     

    ( Sale Kudo: kirarin Muntari)

    A wannan kirari akwai Alamtarwa ya kalli irin yadda Muntari yake da firgitarwa da bada tsoro a wurin sauran 'yan tauri ya alamta shi da ƙasar kabari domin duk mai imani ya ganta zai tuna Allah kamar yadda duk ɗan tauri in ya haɗo da Muntari ko ba a cikin shirin farauta ba yasan lallai ɗan tauri ya gani.

    Misali na 4

    Jagora: Sahun keke ba a gane gabanka

    : Yaro kauce maza a gabanka

    (Sale Kudo: kirarin Bahari)

    A nan Kudo ya kalli yadda sahun keke yake ya ba Bahari wannan alama ganin yadda yake mishau badda musulmi wato bai da abokin faɗa a fagen tauri ya na zaune da kowa lafiya. Babu wata daba ko tawagar da bai shiga a yi hira da shi in ma farauta ta kama sai a tafi da shi ganin yadda aikin tauri yake da wuya a samu ɗan tauri da bai da abokin hamayya amma shi bai da shi yasa Kudo ya Kira shi da sahun keke ba a gane gabanka.

    4.4.2 Tubalan Alamtarwa ta Abu Mai Rai

    Alamtarwa ta hanyar amfani da abubuwa masu rai wata dabara ce da makaɗan tauri ke amfani da ita wurin gurza ɗan tauri da nuna shaharar sa da ƙoƙarin sa a cikin sana'ar tauri. Irin wannan Alamtarwa na iya zama itatuwa ko dabbobi dasauransu su tsaya a matsayin mutum ko wani abu domin a nuna shahara ko ƙarfin magani. Ita ma takan zo cikin sigar kwatantawa dabara ce ta bayyana wani abu ta hanyar ba shi wata alama wadda za ta tsaya maimakonsa.

    Misali

    Jagora: Ba kare bin kura

    : Amadu uban Tijjani

    (Sale Kudo: kirarin Amadu Nijar)

    A nan kare da kura wakilai ne na wata manufa, ana iya ɗaukar kare da tsoratarwa da kuma hargagin kura. Kare yana da Haushi da kuka ga baƙon da bai sani ba. Kura ba da firgitarwa ga mutane.

    Misali na 1

    Jagora: Samarin biri masu ɓarnar raini

    : Ɗan gidan Idi sai ta Allah ta yi

    : Mai ƙahon busa

     

    (Sale Kudo: kirarin Manaja)

    A wannan kirari Kudo ya amfani da Alamtarwa da Abu mai rai ya kalli irin yadda biri ke ɓarna ga kayan gona ya ba Manaja wannan alama ganin yadda yake buge maza a fagen wasan tauri musamman idan wasan sanda ne Manaja ya kan ji wa mutane rauni sosai har ta kai ba kasafai ake tararsa ba a wurin wasan.

    Misali na 2

    Jagora: Gizaka babbar tsutsa

    : Ɗan Audu na iro

    : Bawan gidan kado

    (Sale Kudo:)

    A wannan kirari an yi amfani da Alamtarwa ta hanyar kawo abu mai rai Kudo ya kalli yadda Gizaka take da haɗari musamman idan mutum ya taɓa ta ko ya taka ta irin yadda take sakarwa mutum gashi tasa masa ƙuraje a jiki. Sai ya yi La'akari da wannan ya danganta Amadu da ita ganin irin yadda yake da rashin shaga cikin shirgin 'yan tauri sai dai in aka taɓo shi fa lallai zai haifarwa mutum da matsala.

    Misali na 3

    Jagora: Gawar kura ko kin mutu kin wuce Allah sarki

    : Sharna tuyar Hajiya

    : Ruwa matar Ƙwaɗo

    (Sale Kudo: kirarin Lawai)

    A wannan kirari ma an yi amfani da hikimar zance ta Alamtarwa wato an ɗauki lawai an bashi alama ta yadda gawar kura take a bisa yanayi idan aka ga kura ta mutu daɗi za aji musamman masu dabbobi da kuma mutane wannan kuma a dalilin ɓarna ne da take masu. Shi ne Kudo ya dubi irin yadda Lawai ya tsone idon 'yan tauri da yawa ya zame masu annoba ya hana wasu sakewa sai ya kira shi da gawar kura.

    Misali na 4

    Jagora: Ƙadangaren Bakin tulu

    : Gangare saka sauri

    : Na salisu hamza

    (Sale Kudo: kirarin Haruna Oga)

    An yi amfani da Alamtarwa da abu mai rai anan idan aka nazarci ƙadangaren baki tulu anan kudi ya kalli yadda irin yadda yake da haɗari kamar yadda ake cewa a jefe shi ƙ kashe tukunya a barshi ya ɓata ruwa. Sai Kudo ya kira Oga da wannan ganin yadda yake ɗan tauri Wanda yake tare da sarakan gari wato bafade ne ka ji mashi rauni ana iya kiranka fada ka ƙyale shi kuma shi ya yi ma rauni.

    4.5 Tubalan Siffantawa

    Wannan ya shafi irin yadda makaɗan Tauri Sale Kudo ke siffanta ɗan Tauri a cikin kirarin sa da wasu abubuwa da suka danganci dabbobi da tsuntsaye ta hanyar ɗauko matsayinsu ko ƙimarsu ko kuma wata baiwa ta su ya ɗorawa ɗan tauri domin ya nuna irin shaharar da wannan ɗan tauri yake da ita.

    Ɗangambo (2007) Siffantawa kamar kwatantawa ce, sai dai ita kwatance ne na kai tsaye; a kan ɗauki darajar wani abu ko halayyarsa a ɗora wa wani abu kai tsaye wato ace "kaza" ko kaza shi ne "kaza".

    Salon kwatance, salo ne na babban salon siffantawa wanda ke bayyana wani abu daban wato siffanta mutum da cewa ya yi kama da wani abu, amma ba shi ne abin ba. Yahya (2001: 67). Shi kuwa Gusau (2003 : 57) cewa ya yi siffantawa ''wata dabara ce inda makaɗi yake ɗaukar siffar wani abu ya ba wa wani abu ba tare da amfani da wani tsakani ba.

    Makaɗin tauri Sale kudo gwani ne na amfani da irin wannan salo na siffantawa a cikin kirare-kiraren sa na 'yan tauri.

    Misali

    Jagora: Tunkiya uwar tamɓele

    : Sadda kai ki mance gidanku

    : Ikon Allah ya kai mu Dokoki

    (Sale Kudo: kirarin Haruna Oga)

    A wannan kirari Kudo ya siffanta Iro da Tunkiya wadda aka sani da ɗanyen kai, domin ya nuna irin yadda yake da kutsa-kutsa cikin sauran tawagar 'yan tauri da irin yadda bai da wani takamaiman abokin adawa, ko'ina zai iya kunna kai ba tare da ya samu wata matsala ba a inda ya shiga.

    4.5.1 Tubalan Gajeriyar Siffantawa

    Ɗangambo (2007: 44) gajeriyar siffantawa kwatance ne na kai tsaye da akan ɗauki halayyar wani abu ko darajar sa a ɗorawa wani abun na daban kai tsaye, wato ace wannan abu na farko shi ne abu na biyu da aka siffanta da shi. A wannan salo Sale Kudo ya na Siffanta Ɗan tauri kai tsaye da wasu halittu kamar dabbobi ko tsuntsaye ko sauran abubuwa ya ce su ne ɗan tauri ko ya ce ɗan tauri ne su.

    Misali 1

    Jagora: Baƙin sa mai taka mutane

    : Mijin 'yar Gambo

    : Ƙulli maganin bajewar kaya

     

    (Sale Kudo: kirarin Na'aba)

    A wannan kirari kudo ya siffanta Na'aba da Sa, kasancewar yadda ba a raba Sa da ɓarna, dole sai ana tarbe shi. Sannan gashi da saurin fushi ko da yaushe fuskarsa a murtuke wannan ya sa Makaɗin ya siffanta shi da Sa saboda bai da tsoron afkawa cikin gungun 'yan tauri duk yadda suke da yawa.

    Misali 2

    Jagora: Allah ji ƙan maza na bakin layi

    : Tumbin shaho baka cika da halak

    : Uban Najibu baban Sada

    (Sale Kudo: kirarin Bahari)

    A nan ya kira Bahari da Tumbin Shaho domin ya nuna irin yadda yake takurawa sauran 'yan tauri a fagen daga ta fuskar hanzari da zafin nama, wurin ƙwace abunda aka farauto. Ya kalli yadda Shawo yake ya siffanta Bahari da shi domin ya nuna yadda yake da zarra a wurin farauta na abunda aka kashe ko da ba shi yayi kisan ba.

    Misali na 3

    Jagora: Giwa karya itace

    : Mai gidan mutanen kanya

    : Dogo ɗan yalwa

     

    (Sale Kudo kirarin Bahari)

    A wannan kirari akwai dabarar siffantawa domin an siffanta Bahari da Giwa wato yadda take da ƙarfi wajen karya itace sai aka dubi yadda Bahari ke karya maza yake yin kaca-kaca da su a wurin wasan tauri sai ya kwatanta sa da Giwa. Kudo ya bayyana cewa Bahari mutum ne mai ƙarfi yana da ƙoƙari wajen baza taro sai ya siffanta sa da Giwa da itace.

    Misali na 4

    Jagora: Zaki mai wawar kora

    : Ɗan shehu garkuwa

    : Ga kudi ga tauri

    (Sale Kudo kirarin Zubairu)

    Sale Kudo ya amfani da fasahar siffantawa a cikin wannan kirari domin ya siffanta Zubairu da yadda zaki ke yo kora a cikin daji ya kalli irin yadda yake baza namun daji komin yawansu sai yai duba da yadda Zubairu ke yi a wurin wasan tauri ko farauta musamman idan ana wasan tauri da sanda duk inda ya juya sai kowa ya ruga yana gudun kada ya iske shi domin haɗuwar bata kyau.

    4.5.2 Tubalan Doguwar Siffantawa

    Doguwar siffantawa kwatance ce mai rassa ko mai yaɗo. Za a iya kiranta hoto cikin bayani, wani lokaci lokaci da ya ƙunshi iwatantawa.( Ɗangambo 2007: 44-45). Makaɗin tauri Sale Kudo yana siffanta 'yan tauri da abubuwan halitta iri-iri.

    Misali

    Jagora: Rigi-rigi tambarin makiyaya

    : Kai ba kai ruwa ba

    : Ka hana makiyaya kiwo

     

    (Sale Kudo: kirarin Manaja mai nama)

    A wannan kirari Kudo ya siffanta Manaja da Hadari, ya kuma siffanta shi da ruwan damuna wato irin mamakon ruwa da yake hana sukuni. Wannan Doguwar siffantawa ce domin ta na ɗaukar hoto ne cikin bayani anan mai sauraro zai yi duba ne da irin yadda hadari ke haɗuwa ya mamaye gari ta yadda kowa zai nemi wuri ya natsu har sai ya wuce, shi ne ya siffanta Manaja da haka domin ya nuna irin yadda yake hatsabibi a fagen wasan tauri.

    Misali 2

    Jagora: A buga a tunkuɗa sai Jaki

    : Ruwa matar Ɗwaɗo

    : Matar ƙadangare sai bunu

    : Nisan kiwo sai Tunku

     

    (Sale Kudo: kirarin Manaja)

    A nan ma Kudo ya yi amfani da fasahar Doguwar siffantawa domin ya siffanta Manaja da Jaki da Ruwa da Ƙwaɗo da Ƙadangare da bunu. Domin ya nuna irin taurin kan Manaja da kafiyarsa da tsayuwa akan Tauri. Wannan ya nuna ba shi da tsoro ko shakku akan abunda yasa a gaba.

    Misali na 3

    Jagora: Tulu mai santsin baya

    : Dattijo baka kukan aski

    : Ka tsare birni ka tsare kauye

    (Sale Kudo kirarin Leko)

    Wannan kirari yana ɗauke da doguwar siffantawa domin Kudo ya kalli irin yadda Tulu yake da wuyar ɗauka da yanayinsa sai ya siffanta Leko da shi domin a nuna irin yadda yake da wuyar sha'ani a fagen tauri ba kowa bane ke iya tarar sa ko ya haye masa kai tsaye duk yadda ɗan tauri ya shahara Leko na iya bashi matsala wato ba shi da tabbas a wurin tauri sai ya siffanta shi da Tulu.

    Misali na 4

    Jagora: Gangare mai sa maza su ruga da gudu

    : Jirgin sama ko macen tsari ta sanka

    (Sale Kudo kirarin Na'aba)

    A wannan kirari Kudo ya yi amfani da salon siffantawa domin ya siffanta Na'aba da gangare kuma ya siffanta sa da jirgin sama ganin irin yadda gangare yake cewa duk yadda ka taho sai ka ruga ko kana so ko baka so sai ya ba sa wannan sifa domin ya nuna yadda yake tursasa 'yan tauri su gudu ko dan dole. Haka sai ya sake siffanta shi da jirgin sama wanda baya fakuwa duk inda ya gitta sai kowa ya gansa shi ne ya ke nuna cewa Na'aba sananne ne a harkar tauri kowane ɗan tauri tsoronsa yake ko shakkar haɗuwa da shi yake.

    4.6 Tubalan Dabbantarwa

    Dabbantarwa ita ce mayar da mutum ko wani abu dabba, kamar yadda Ɗangambo ya ce a cikin littafin sa ɗaurayar gadon feɗe waƙa sabon tsari. Da yawa mawaƙa da makaɗan tauri sukan yi amfani da wannan dabara wajen zuga ɗan tauri. Za a iya cewa salon Dabbantarwa yana daga cikin muhimman salon aiwatarwa na Waƙoƙin Maza. Domin da yawan dabbobi an san su da shahara da ƙarfi da kwarjini da baiwa da isa da tunƙaho, wannan dalili ya sa da wuya a samu wani shahararren ɗan tauri da wannan salo bai je kansa ba. Sale Kudo gwani ne wurin amfani da Dabbantarwa wurin zuga da kururuta ɗan tauri domin ya fito ya ɗebe tababan abunda ake faɗa a kansa. A lokacin da yake wannan zuga yakan lura da halayen wasu dabbobi na gida irinsu Rago, Tunkiya, Akuya, Sa, ko Saniya da sauran dabbobi. Sannan yakan duba halaye da ƙoƙari tare da ƙwarjinin wasu Dabbobin na daji irinsu Zaki, Damisa, Ayu, Raƙumi, Ɓauna, Giwa da sauransu. Sai ya Kira Ɗan tauri da irin halayensu domin ya zuga shi ko ya kururuta sa ta yadda zai fito ya bayyana irin shahararsa.

    Misali.

    Jagora: Ɗan maraƙi baka san galma ba
       : Mai bada magani a ji sau
    ƙi
       : Goga kasan hanya

    (Sale Kudo kusada kirarin Iro Ɗan baiwa)

    A wannan kirari Kudo ya Dabbantar da Iro Ɗan baiwa ya Kira sa da Ɗan maraƙi domin ya nuna irin yadda yake da ƙarfi a jika da kuma yadda yake da zafin nama a cikin huɗɗar tauri. Ya ce masa nai san galma ba duba da yadda bai taɓa haɗuwa da wata matsala ba ko ƙalubale. Wato dai yana cikin ganiyarsa kuma yana cin lokacin sa. Wannan zuga ce domin Iro ya ƙara dagewa ya fito ya bigi gaba a cikin tawagar 'yan tauri.

    4.6.1 Tubalan Amfani Da Dabbobin Daji

    Amfani da Dabbobin daji, wani babban ɓangare ne da Makaɗan tauri kan yi amfani da shi a cikin kiɗan domin zuga da kururuta ɗan tauri domin ya fito ya ɓarje guminsa ko ya fashe ƙududun dake a zuciyarsa a gaban sauran 'yan tauri. Kowane ɗan tauri ya na so a Kira sa da jarumi wannan yasa makaɗan tauri kan kalli shahara ta dabbobi sai su Kira ɗan tauri da sunan wannan dabba a cikin kiɗan su domin su ƙara wartsakewa da yin tunƙaho da alfahari wajen bayyana ƙarfin magani. Wannan yana a matsayin zuga.

    Misali 1

    Jagora: Zalɓe uban kasada
         : Mai tura
    ƙafa rami
         : Ga yaron da bai jira a ba shi bayani.


    (Sale Kudo kusada kirarin Iro)

     

    A cikin kiɗan akwai zuga domin kuwa Kudo ya Kira Iro da Zalɓe uban kasada wato yana nunawa cewa duk abunda Iro zai yi ko zai aikata a harkar tauri daidai da shi ne domin shi sakakke ne bai da wata doka ko ƙa'ida akansa shi yasa ya danganta shi da zalɓe wanda bisaal'adarshi yakan yi abunda yake so ne ba kamar sauran tsuntsaye ba. Wannan yana a matsayin zuga a cikin kiɗan Iro mai kare.

    Misali 2

    Jagora: Kura kin ci da gashi

    : Tarkon sama mai kama aljani
       : Na sarki Gambo

     

    (Sale Kudo kirarin Sani Na'aba)

    Akwai dabarar Zuga da akai amfani da Dabbantarwa a cikin wannan waƙa domin kuwa Kudo ya Kira Sani Na'aba da kura ganin irin yadda yake da hargagi da kururuwa sai ya bashi sunan kura domin ya kururuta sa ya kambama sa ta yadda zai cire tsoro ko shakku ya yi abunda ya ke so a fagen daga.

    Misali na 3

    Jagora: Ɓauna Saniyar sake
       : Jan Zaki na Jummai
      : Uban Faruku


    (Sale Kudo kirarin Auta)

    A cikin wannan kirarin akwai fasahar Zuga da kururutawa domin a nuna ƙarfin magani da ƙwarewa a cikin harkar tauri. Sale Kudo ya Kira Isihu da Ɓauna Saniyar sake domin ya nuna irin yadda yake da 'yanci a cikin huɗɗar tauri wato yana iya yin duk abunda yake so ko ya ga dama a lokacin da ya ga dama. Wannan na amatsayin zugawa domin ya ƙara ƙwazo da miƙewa akan sha'anin tauri.

    Misali 4

     Jagora: Gizaka babbar tsutsa
      : Auta amanar Manu

    : Ɗan mutun Ɓauranya

     

    (Sale Kudo kusada kirarin Auta)

     

    A nan ma akwai Dabarar zuga a cikin wannan waƙa ta Auta domin Kudo ya nuna irin yadda gogan nasa ya ke da haɗari da dafi a wurin sana'ar tauri ya Kira shi da Gizaka domin ya fito ya wartsake ya bugi-gaba wajen bayyana shahara da ƙarfin magani a tsakanin 'yan tauri.

    4.6.2 Tubalan Amfani da Dabbobin Gida.

    Wannan ma kamar amfani da Dabbobin daji ne Mawaƙin Tauri kan dubi wata dabba daga cikin Dabbobin gida sai ya kalli yanayinta da halinta da ɗabi'unta sai ya Kira wani Ɗan Tauri da wannan suna domin ya zuga shi ko ya kururuta sa ta yadda zai ji tsiminsa ya motsa ya fito cikin fage domin a debe tababan abunda ake faɗa akansa. Waɗannan dabbobi suna da yawa sosai akwai masu haƙuri da kuma masu fushi da waɗanda ba ruwansu dukkan su Sale Kudo kan yi amfani da su a cikin Waƙoƙin sa domin zuga Ɗan tauri.

    Misali 1

    Jagora: Tunkiya Uwar Tamɓele
          : Sadda kai ki manta gidanku
           : Ga mai shawara da Oga Audu.

     

    (Sale Kudo kirarin Auta)

    A wannan ɗiyan waƙa Kudo ya Kira Auta da Tunkiya domin ya nuna irin yadda yake da ɗanyen kai wajen rashin tsoro da shiga cikin tawagar 'yan tauri tare da nuna cewa shi ko'ina yana iya shiga kuma a dama da shi matuƙar akwai wasan tauri a wurin.

    Misali na 2

    Jagora: Baƙin Sa Mai taka mutane
      : Mijin 'yar Gambo
      : Hadari malafar Duniya

    (Sale Kudo kirarin Leko)

    A wannan waƙa ta Musa Leko akwai fasahar Dabbantarwa wadda aka yi amfani da Dabbobin gida inda ya kira Leko da Baƙin Sa. Anan ya zuga Leko ya danganta shi da sa ganin yadda Sa yake da Ƙarfi da Saurin Fushi da Rashin yadda sai ya ɗauki waɗannan Halaye ya ɗorawa Leko domin ya sashi dagewa da ƙoƙari wajen tafiyar da aikin Taurin sa.

    Misali na 3

    Jagora: Ɗan maraki baka San Galma ba.
          : Dan wuya Maza basu gudu

     

     (Sale Kudo kirarin Iro)

    A wannan waƙa akwai fasahar Dabbantarwa da aka yi amfani da Dabbobin gida ya kira Iro da Ɗan maraƙi domin ya zuga shi ya yi aiki irin na ɗan maraƙi wato yadda aka San ɗan maraƙi da ƙarfi da lafiya ga shi bai san wuya ba tunda ba a huda shi ba bare ya fara huɗa sai ya danganta Iro da shi domin ya nuna irin yadda yake da ƙarfi da ƙoƙari wajen aikin tauri. Wannan zuga ce kai tsaye 

    4.7. Tubalan Alamtarwa

    Wannan shi ne mayar da mutum ko dabba ko tsuntsaye ko wani abu mai rai, ya zama mara rai (Ɗangambo 2007). Kenan Abuntarwa na nufin ƙin kiran mutum ko wani abu da sunansa da aka san shi da shi maimakon haka sai a samu wani abu maras rai a kira shi da wannan suna, ta yadda sunan zai yi tasiri a kansa da kuma zuga shi ko ƙara masa ƙaimi da karsashi domin fitowa cikin fage domin a ɗebe tababar abunda ake faɗa a kansa. Makaɗan tauri sukan yi amfani da irin wannan salo na Abuntarwa wajen kiran jaruman tauri da waɗansu shahararrun abubuwa masu wata buwaya ko ɗaukaka ta musamman domin su kwarzanta ɗan tauri da ƙara masa ƙwarin gwiwa a kan zama namiji. Wannan dalilin ya sa da yawan 'yan tauri sunayen su na asali ke ɓacewa sai a dinga kiransu da ire-iren waɗannan sunaye da suka samu daga masu kiɗan tauri. Makaɗan tauri na kallon hali da ɗabi'un ɗan tauri ko yanayin sa ko bajintarsa ko wata dabara ko taurin kai sai su abunta shi da wannan abubuwa irin wannan abubuwa suna da yawa sosai musamman masu motsi irin su Jirgin sama da Mota da Keke da Wata da Rana da sauransu, akwai kuma wasu da basu motsawa wato kafaffu irin su Duwatsu da Tsauni da Titi da Bishiyoyi da Bango da Rami da sauransu. Wannan ya sa ake samun sunayen wasu 'yan tauri irin su Gora da Tulu da Jirgi da Gangare da Katako da Dutse da Faƙo da Bango da makamantansu.

    Misali

    Jagora: Jirgin sama ko macen tsari ta sanka

    : Ikon Allah ya maida mu Dokoki

    : Wurin Musa Leko

     

    (Sale Kudo kirarin Iro)

    A wannan ɗiyan waƙa akai dabar zuga ta amfani da abu mai motsi domin Kudo ya Kira Iro da Jirgin sama domin ya zuga shi ta yadda zai ɗauka ya kai duk inda ake so a huɗɗar tauri, ya kalli yadda Jirgin sama yake da ɗaukaka ta musamman da ƙwarjini da kuma irin yadda yake ratsa ko'ina a cikin Duniya sai ya nuna cewa Iro ya kai wannan matsayi hakan zai ƙara tunzura sa wurin fitowa fagen daga da nuna ƙwazo da ƙarfin maganinsa ba tare da jin tsoro ko tababa ba.

     

    4.7.1 Tubalan Abubuwa Kafaffu

    Wannan ya danganci sauran abubuwa da za a iya kira da marasa motsi waɗanda a ko da yaushe suna a wurin da aka san su kuma ba su canzawa daga yadda aka san su, sannan suna da wata baiwa da buwaya da aka san su da ita. Ire-iren waɗannan sun haɗa da Duwatsu da Daji da Rafuka da Tsaunika da Itatuwa da Gonaki da makamantansu.

    Sale Kudo yakan lura da irin baiwar waɗannan abubuwa ya abunta wani ɗan tauri da su a lokacin yake masa kiɗa domin ya nuna irin ƙarfin maganinsa. Akwai misalan irin wannan salo da dama a cikin kiɗan tauri na Kudo sai dai mu kalli wasu daga ciki kamar waɗannan.

    Misali 1

    Jagora: Hayaƙi fidda na Kogo

    : Daji ba a maka ƙyaure

    : Uban Halimatussadiya

     

    (Sale Kudo kirarin Zubairu)

    A nan Daji da Hayaki da Kogo duka Abuntarwa ce domin Kudo ya yi amfani da su ya kira wani kuma ya amsa wannan kira. Har taka wasu na kiransu da waɗannan abubuwa kenan sunan ya yi tasiri akan su da kuma sana'arsu ya Kira sa da Daji domin ya zuga sa ya bayyana girma da ƙarfi da yake da shi Wanda hakan yasa yake jin cewa ya kai zaƙaƙuri kuma yake tutiya da bugun gaba a ko'ina a fagen tauri.

    Misali na 2

    Jagora: Kibiya ratsa Maza

    : Gangare mai sa a ruga da gudu

    : Na sarki Gambo

     

    (Sale Kudo kirarin Haruna Oga)

    Gangare da Kibiya dukan su abubuwa ne da Sale Kudo ya kalla ya Zuga Haruna Oga da su domin ya Kira sa da Gangare ne domin ya nuna irin yadda yake tursasa 'yan tauri yin abunda ba su yi niyya ba, shi yasa yace mai sa maza su ruga da gudu lallai wannan yasa Haruna ya ji dadi har takai yana alfahari da bugun gaba a gaban 'yan tauri. Wannan zuga ce da ta ƙarawa Haruna ƙwazo kuma tasa ya cire tsoro a fagen tauri.

    Misali na 3

    Jagora: Bango a jingina da kai ko dole

    : Tuntu mai dira ta ka Dan kusada

    : Ɓaleru bawan sarki

    (Sale Kudo kirarin Sarki Gambo)

    A cikin wannan waƙa ta Sarki Gambo akwai Abuntarwa domin Kudo ya Kira sa da Bango abun jingina anan ya nuna cewa Sarki ya kai shugaba har takai duk Wanda ya kwaso matsalar sa wurinsa ake zuwa a raɓu da shi don a samu warwara. Kudo ya zuga Sarki Sosai a wannan ɗiyan waƙa har takai sarki na jin shahararsa ta zarce a iya Tauri kadai.

    Misali na 4

    Jagora: Ƙarfe maci ƙarafa

    : Gizako mai ɗamarar yaƙi

     

    (Sale Kudo kirarin sarki Zubairu)

    A nan ma Kudo ya yi amfani da dabarar Abuntarwa inda ya maida Zubairu Ƙarfe Wanda an San cewa ƙarfe ba mutum bane wani abu ne da ake sarrafawa domin yin mabambantan kayan amfani na gida da na gona amma anan sai Kudo ya Kira Zubairu da Ƙarfe domin ya nuna irin taurin hali da ƙarfi da ƙin sarrafuwa da yake da ita cikin sauƙi ya Kira sa da ƙarfe wannan abu yayi wa Zubairu daɗi sosai domin a duk sadda yake kirari yakan ce ''sai ni ƙarfe uban ƙarafa'' wannan yana a matsayin zuga da kururutawa domin fitowa da nuna ƙoƙari da bajinta.

    4.7.2 Tubalan Abubuwa Masu Motsi

    Abubuwa masu motsi, anan na iya zama ƙirƙirarru daga Mutane kamar kayan amfani da ake ƙerawa domin biyan buƙatu na rayuwa irin su: Mota da Jirgi da Keke da kuma sauran kayan aiki irinsu Fanka da Kujera da makamantansu. Haka kuma za su iya zama halittattun abubuwa irin su Gangen bishiya da Wata da Rana da Ruwa da makamantansu.

    Makaɗan tauri kan ɗauki wannan salo su bai wa ɗan tauri domin nuna irin shahararsa, kuma a mafi yawancin lokaci waɗannan sunaye Kan yi tasiri a kan ɗan tauri har ya kai wannan suna ya bi shi, ya nashe wanda aka san shi da shi. Zamu ga wannan a zahiri cikin kiɗan tauri na Sale Kudo, musamman idan muka duba waɗannan misali dake zuwa.

    Misali na 1

    Jagora: Sahun keke ba a gane gabanka

    : Ɗan na gada da yafi ɗan na koya

     

    (Sale Kudo kirarin Auta)

    A wannan kirari akwai zuga inda Kudo ya Kira Auta da Sahun Keke wato anan yana nuna cewa Auta ya iya tauri sosai har ta kai sauran 'yan tauri ba su iya gane irin shirin da yake da shi a fagen tauri bare har wani yace zai tunkare sa ko ya ja da shi. Wannan ba ƙaramin tasiri yayi ba a wurin Auta domin ya ji dadi sosai har takai yana bugun gaba da yin tutiya cewa shi sahun keke ne Wanda ba a gane gabansa.

    Misali na 2

    Jagora: Awartaki makama zafi

    : Jifa zubda maza

    : Na indo A'i

     

    (Sale Kudo kirarin Auta)

    A wannan kiɗan ma akwai Abuntarwa a ciki domin Kudo ya Kira gwanin nasa da awartaki Wanda ake cewa makama zafi yayi haka ne domin ya nuna irin yadda yake da dauriya da jumuri a wurin wasan tauri. Wannan ya zama kamar zuga da kambamawa ta yadda zai ƙara zabura ya zage damtse akan abunda ya sa gaba na harkar tauri.

    Misali na 3

    Jagora: Shantu abun kiɗan 'yan mata

    : Dole a bar kare ya bi karya

    : In yabi Tunkiya ku kashe shi.

    (Sale Kudo kirarin Sani Na'aba)

    Shantu abu ne da ake kiɗan 'yan mata da shi ko Amarya wato yana da matuƙar muhimmanci a wurin mata yana sa su nishaɗi da annashuwa. Kudo ya yi amfani da shi ya Kira Sani da Shantu domin ya nuna irin yadda yake da farin jini da burge murane wannan yasa ya ji daɗi sosai har yana alfahari da hakan. Za a iya kallon wannan a matsayin zuga wadda ta sa shi bugun gaba da tunƙaho a tsakanin 'yan tauri.

    Misali na 4

    Jagora: Tulu mai santsin baya

    : Mijin Yar Gambo

    : Baka gudu ka bar abokan gaba

    (Sale Kudo kirarin Bahari)

    Kudo anan ya abuntar da Na'aba inda ya kira sa da tulu. Anan ya kalli irin yadda tulu yake sai ya danganta shi da shi domin ya nuna irin yadda yake da wahalar sarrafuwa a wurin wasan tauri ko a lokacin farauta. Na'aba yana jin daɗin wannan kiɗa sosai domin har ta kai yana furta wannan da kan sa a lokacin da yake kirari. 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.