Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Tubalan Turken Zuga A Wakokin 'Yan Tauri Na Sale Kudo Kusada – Kashi Na Biyar

Kundin Digiri Na Biyu (M.A Hausa Culture) Da Aka Gabatar A Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero Kano (Maris, 2024)

Nazarin Tubalan Turken Zuga A Waƙoƙin 'Yan Tauri Na Sale Kudo Kusada

Aminu Musa
07036420021
ameenumusa12@gmail.com

BABI NA BIYAR

5.0 Shinfiɗa

A wannan babi an kawo bayanin kammalawa ne na wannan bincike da aka gabatar ta hanyar kawo taƙaitattun bayanan abubuwan da wannan nazari ya ƙunsa da kuma abubuwan da wannan bincike ya gano da tasirin maganganun azanci na salon sarrafa harshe da makaɗan Tauri Sale kudo ke yi a cikin kiɗansa. Sai kuma shawararwari da wannan bincike ya bayar.

5.1 Taƙaita Bayanin Bincike

Wannan bincike ne Wanda aka sa wa suna ''Nazarin Tubalan Turken Zuga A Waƙoƙin 'Yan Tauri Na Sale Kudo Kusada' A wannan bincike da aka gabatar an kawo bayanan dalilin bincike da manufar bincike da iyakancewar bincike da kuma gudummuwar bincike.

Sannan an kawo tarihin Sale Kudo da tarihin garin Kusada, sannan an kawo ma'anar salo da ma'anar sarrafa harshe da ma'anar Tauri. Haka kuma an yi bitar ayyukan da suka gabata waɗanda suka haɗa da kundayen bincike da Bugaggun Littattafai da Maƙalu da sauran takardun ilimi da aka gabatar waɗanda suka tallafi wannan aiki da haska min hanya da na bi wajen kammaluwar wannan kundin bincike

Sannan an kawo ra'i da aka yi amfani da shi wajen gudanar da wannan aiki wato ra'in mazahabar waƙar baka wadda Farfesa sa'idu Muhammad Gusau ya samar a shekarar 1993, an kawo bayani akan ayyukan wannan masani da bayanin abinda ra'insa ya ƙunsa. Sannan an kawo bayanin hanyoyin da aka bi wajen tattaro bayanan da aka yi amfani da su wajen gudanar da wannan bincike nawa, an kawo sunayen ɗakunan karatu da aka ziyarta domin yin wannan bita da kuma samo bayanai, an kawo sunayen tsofaffi 'yan Tauri waɗanda aka tattauna da su a garin Rimaye da Kusada da Ɗanƙawari da Naƙawa da Sabarawa tare da kawo tambayoyin da aka yi masu, haka kuma an kawo sunayen malamai masana waɗanda aka yi masu tambayoyi tare da kawo jerin tambayoyin da aka yi masu.

Har ila yau an binciko masana ilimin Tauri a aikace wato 'yan Tauri masu yanka wuƙa, an kawo sunayen su an bayyana tambayoyin da aka yi masu waɗanda aka samu amsoshinsu, kuma amsoshin suka tallafi wannan bincike sosai har ya kammalu cikin nasara.

Sannan an kawo bayanin abinda aikin ya ƙunsa gaba ɗaya a babi na huɗu a inda aka kawo tarin wasu abubuwa da Sale Kudo ke la'akari da su a lokacin da yake Waƙoƙin Tauri da suka haɗa da siffantawa da kambamawa da Abuntarwa da Alamtarwa da Dabbantarwa daga ƙarshe aka kawo bayanin kammalawa na wannan babi na biyar.

5.2 Sakamakon Bincike

A wannan bincike an gano makaɗin Tauri Sale Kudo yana amfani da wasu ginshiƙai wajen gina Waƙoƙin Taurinsa.

Haka kuma wannan bincike ya gano Tasirin siffanta ɗan Tauri da wata halitta domin irin yadda yake samun ƙarin ƙarfin gwiwa da juriya a fagen daga.

Sannan wannan bincike ya fahimci cewa makaɗan Tauri na jin kunyar faɗar waɗansu maganganu kai tsaye a lokacin da suke wa ɗan Tauri Kirari, sai su yi amfani da salon Sakayawa domin su kauce wa faɗar batsa a cikin kirarin nasu.

Har ila yau wannan bincike ya gano cewa Sale kudo mutum ne mai fasaha wajen Waƙoƙin sa na Tauri irin yadda yake amfani da hikimar magana yana gina Waƙoƙin sa.

Muhimmin abun da wannan bincike ya gano shi ne cewa 'yan tauri sukan samu nishaɗi da ƙarfi a lokacin da makaɗin tauri ya Kira su da sunan wata shahararriyar dabba mai ƙarfi da kwarjini.

Su kuwa 'yan Tauri wannan bincike ya gano suna amfani da maganganun da makaɗan Tauri ke furta wa a kansu.

Haka kuma wannan bincike ya gano makaɗin Tauri Sale Kudo kan yi duba da hali ko ɗabi'ar ɗan Tauri sannan ya bashi wata alama da zata riƙa bayyana shi a cikin taro.

5.4 Shawarwarin Bincike

Wannan bincike da aka gabatar ya bayar da Shawarwari ga Manazarta kamar haka:

-                      Yana da kyau a riƙa bibiyar fasahohin makaɗan Tauri domin adana salon da suke amfani da shi wajen kiɗa a cikin kundi ta yadda za su zama abun nazari.

-                      Har ila yau zai yi kyau a bibiyi waƙe-waƙen makaɗan Tauri domin fito da hikimomin zance irinsu dabarun sarrafa harshe sannan a fayyace su daki-daki domin 'yan baya su samu abin bita.

-                      Haka kuma zai yi kyau Manazarta su samar da wani tsari da zai tattaro salon sarrafawa dake cikin waƙoƙin Tauri da shirya su cikin wani tsari na musamman domin su zama abin dogaro nan gaba.

5.5 Naɗewa

A nan wannan babi ya zo ƙarshe wannan babi shi ne ya zama gaɓa ta ƙarshe na wannan bincike. A cikin babin ne aka yi bayanin gabatar da babin da kuma kawo cikakken bayani game da Shawarwarin bincike da kuma irin gudummuwar da binciken ya bayar ga ɗaliban ilimi da Manazarta domin yin dogoro zuwa ga mataki na gaba daga ƙarshe an naɗe babin da wannan bayani na kammalawa. 

Post a Comment

0 Comments