𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne hukuncin Azumin wanda yayi
mafarki da rana har Maniyyi yafito masa??
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Dangane da hukuncin Fitar Maniyyi
ga wanda yake azumi mafi yawan Malamai cikinsu harda Mazhabobin nan guda huɗu wato
1. Malikiyya
2. Shafi'iyya
3. Hanafiyya
4. Hanabila
Dukkansu suntafine akan cewa
fitar da Maniyyi da gangan ta hanyar da ba jima'i ba yana lalata azumi, danhaka
idan Mai-Azumi yayi Istimna'i, ko ya rungumi Matarsa, ko yayi wasa da'ita,
hartakai ga yafitar da Maniyyi to azuminsa ya lalace, danhaka Malamai sukace
dukkan Mutumin da yasan cewa Sha'awarsa tana da ƙarfin da indai zaiyi wasa da Matarsa
Maniyyi zaifito masa to haramunne agareshi yayi hakan da'ita, idan kuwa yayi
har Maniyyi yafita to wajibine sai yarama wannan azumin, amma idan yakasance
Maniyyin yafitane ta hanyar mafarki kokuma tunani ko kallon Mace batare da yayi
wasa da'itaba, mafi yawan Malamai sukace azuminsa bai lalace ba saidai wajibine
yayi wankan janaba, amma Mazhabin MALIKIYYA sukace koda mafarki yayi dolene sai
yarama wannan azumin.
Danhaka Malamai sunyi Saɓani dangane da yanayin
ramuwar azumin da Mutum zaiyi, Mafi yawan Malamai suntafine akancewa zai rama
azumi guda ɗayane
kawai batare da yayi wata Kaffara ba, domin Nassin yin Kaffara yazone akan
wanda yayi Jima'i da Matarsa da rana, Saidai Mazhabin MALIKIYYA suntafine
akancewa idan Mutum yayi Mafarki har yafitar da Maniyyi to azuminsa ya lalace
kuma dolene sai ya rama batare da kaffaraba, amma idan wasa yayi da Mace ya
rungumeta ko ya Shafata ko yayi Istimna'i har yafitar da Maniyyi, to wajibine
sai yayi ramuwa tare da Kaffara, domin sunyi Ƙiyasine akan hukuncin wanda yayi Jima'i
da Matarsa da gangan da rana.
Amma. Mazhabin ZAHIRIYYA
suntafine akan cewa wanda yafitar da Maniyyi da gangan ta dukkan wata hanyar da
ba Jima'i yayi da Matarsa ba, sukace azuminsa yana nan bai lalace ba, domin
babu wata Hujja afili Ƙarara daga cikin Al-Ƙur'ani ko Hadisi datace azuminsa ya
lalace, to amma Saidai maganar Malaman da sukace azuminsa ya lalace tafi Ƙarfi.
Amma maganar da tafi inganci
wacce mafi yawan Malamai sukafi rinjayar da'ita shine, fitar Maniyyi ta hanyar
mafarki baya karya azumi, domin Ɗan-Adam bashi da wani iko na ya'iya hana
kansa yin mafarki alokacin da yake barci ba, hakanan magana mafi inganci fitar
Maniyyi ta hanyar tunani ko kallo shima baya karya azumi, amma duk dahaka
ba'ace Mutum yarika sanya irin wannan tunanin acikin Zuciyarsa ba, amma fitar
Maniyyi dagangan tahanyar wasa tsakanin Ma'aurata, ko tahanyar Istimna'i,
wannan kam yana lalata azumi, kuma za'ayi ramuwane kaɗai batare da Kaffaraba, amma idan Mutum yayi
jima'i da Matarsa da gangan da rana, tofa koda baikawo Maniyyiba ramuwa da
Kaffara sunhau kansa.
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ
Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı
αdυвα шαɗαппαп
ʟıтαттαғαı καмαя нακα:
"المغني لإبن قدامة"
الشرح الممتع"
(6/234)
"المجموع للنووي"
(6/349)
AMSAWA
Mυѕтαρнα Uѕмαи
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.