Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Tubalan Turken Zuga A Wakokin 'Yan Tauri Na Sale Kudo Kusada - Kashi Na Daya

Kundin Digiri Na Biyu (M.A Hausa Culture) Da Aka Gabatar A Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero Kano (Maris, 2024)

Nazarin Tubalan Turken Zuga A Waƙoƙin 'Yan Tauri Na Sale Kudo Kusada

Aminu Musa
07036420021
ameenumusa12@gmail.com

SADAUKARWA

wannan aiki nawa sadaukarwa ne ga Mahaifina Marigayi Musa Ibrahim Dansarai da Mahaifiyata da Matana Kursiya Abdullahi da Rahanatu Yahaya. Haka kuma sadaukarwa ne ga yara na Jafar da Aminatu da Aisha(mimi) da Asma'u (Husnah) da Al-Ameen (little) Aminu Musa. Allah ya ji ƙan Baba da Rahama ya yi wa zuriya ta da ta sauran al'ummar Musulmi Albarka baki ɗaya.

GODIYA

Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, tsira da Amincinsa su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta cika makin Annabawa ɗan gata Muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wassalam.

Ina miƙa godiya ta ga Malamina jagoran wannan aiki Dr. Murtala Garba Yakasai wanda cikin ƙaddarawar ubangiji da taimakon sa da shawarwarinsa da goyon bayansa wannan aiki ya kammala, ina godiya da irin karɓa da kulawar dana samu gare sa. Allah ya ƙara masa lafiya da yalwar arziki. Haka kuma ina godiya ga dukkan malamaina na sashe bisa irin taimako da haƙuri da jajircewa da su kai wajen koyar da mu muhimman Al'amura na ilimi da zasu tallafi rayuwar mu ta duniya da kuma lahira, Muna godiya Allah ya saka masu da mafificin alkhairi Amin.

Sannan ina godiya ga iyalaina da dangina da sauran abokan aikina da na karatu na a matakai mabambanta tun daga na secondary dana NCE da na Digirin Farko dana wannan Digiri na biyu dana gabatar Allah ya tallafi ƙoƙarin kowa ya biya wa kowa bukatu na alheri Amin.

TSAKURE

Wannan bincike ya yi bayani a game da tubalan turken zuga ne a waƙar Tauri ta Sale Kudo Kusada. Tubalan turken zuga na nufin yadda mawaƙa suke bin wasu hanyoyi daban-daban wajen kambama ko kururuta ko zuga kansu ko iyayen gidansu ko kuma wasu makusantansu. Mawaƙan Tauri suna amfani da tubalan turken zuga wajen fito da martaban ɗan Tauri da wasu iyayen gidansu, kamar yadda aka sami hakan a wasu waƙoƙin Sale Kudo kusada wanda hakan ya haifar masu da wani tasirin da kwarjini da kuma tabbatar da irin sunan da suka yi a idon duniya. An yi amfani da ra'in waƙar baka Bahaushiya wadda Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau ya samar a shekara 1993. Binciken yabi hanyoyin tattara bayanai kamar shiga ɗakunan karatu inda aka dubi ayyukan magabata da suke da alaƙa da wannan aikin. An kuma saurari waƙoƙin Sale Kudo tun daga na kaset da waɗanda ya yi a fili wurin wasan tauri da wasu da ya rera a lokacin da ake hira da shi wurin tattara bayayanan wannan aiki. Binciken ya tabbatar da cewa Sale Kudo Kusada ya bayar da gudummuwa musamman wajen kare martaban harshen Hausa da kuma adana wa harshen wasu hikimomi da Mai duka ya hore masa.

Wannan bincike ya gano 'yan tauri suna amfani da maganganun masu yi masu kiɗa domin samun nishaɗi da ƙara masu ƙaimi da zuga su domin cire tsoro wajen shiga daji da kuma tunkarar abokan adawa musamman ta ɓoye sunayensu na ainihi da alaƙanta su da wasu shahararrun abubuwa masu buwaya ta musamman. Daga ƙarshe binciken ya bada shawarwari domin samun nasara da ci gaba a cikin aikin sana'ar tauri da wasannin da ake aiwatarwa na Tauri na yau da kullum.

Muhimman kalmomi: nazari da tubala da turke da zuga da waƙoƙi

 

 

ABSTRACT

This study eɗplains about the song Tauri by Sale Kudo Kusada. Zuga refers to how singers follow different ways in kambam or kukuruta or zuga themselɓes or their parents or some of their close ones. The Tauri singers use the Zuga bring out the dignity of the Tauri people and some of their family members, as it was found in some songs of Sale Kudo Kusada, which caused them to haɓe a certain influence and charisma and to confirm the reputation they haɓe made in the eye of the world. The idea of the Bahaushiya oral poetry was used which was deɓeloped by Professor Sa'idu Muhammad Gusau in 1993. The research praised the methods of data collection such as entering the libraries where the works of the ancestors related to this work were looked at. Sale Kudo's songs were also listened to from the tapes and the ones he made in public at the tough game and others that he sang during the interɓiew at the gathering of information for this project. The inɓestigation confirmed that Sale Kudo Kusada has contributed especially in protecting the reputation of the Hausa language and preserɓing the language some of the wisdom taught to him by Mai Duka. This study found out that the hardliners use the words of eɗtremists to entertain and motiɓate them to remoɓe their fear of going into the forest and confronting opponents, especially by using their real names and associating them with popular things. a special buffalo. At the end of the study, it proɓides recommendations for success and progress in the work of the tauri profession and the daily tauri games.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ABUBUWAN DA KE CIKI

Shaidarwa - i

Tabbatarwa - ii

Shafin Amincewa - - iii

Shafin Shaidarwa - - iv

Sadaukarwa - v

Godiya - vi

Tsakure - - - vii

Abstract - viii

Abubuwan Da Ke Ciki - ix

 

 

BABI NA ƊAYA

1.0 Shinfiɗa - 1

1.1 Dalilin bincike - - 1

1.2 Manufar bincike - 1

1.3 Muradin Bincike - 2

1.4 Tambayoyin bincike - 2

1.5 Iyakancewar bincike  - 3

1.6 Gudummuwar bincike - 3

1.7 Turken Zuga - - 3

1.7.1 Sarrafa Harshe - 4

1.7.2 Ma'anar Kirari - 5

1.7.3 Ma'anar Tauri - - 6

1.7.4 Waƙoƙin Tauri - 7

1.8 Taƙaitaccen Tarihin Sale kudo Makaɗin Tauri - 8

1.8.1 Asalin Inkiyar Kudo - 8

1.8.2 Yanayin Sale Kudo - 8

1.8.3 Sana'o'in Sale Kudo - 9

1.8.4 Sana'ar Kiɗan Tauri - 9

1.9 Garin kusada - - 10

1.15 Naɗewa - - 11

BABI NA BIYU

2.0 Shinfiɗa - 12

2.1 Ayyukan Da Suka Gabata - 13

2.1.1 Kundayen bincike - 13

2.2 Mujallu Da Maƙalu - 17

2.3 Bugaggun Littattafai - 22

2.4 Ra'in Da Za A Ɗora Bincike - 24

2.5 Dangantakar Ra'in Da Bincike. - 25

2.6 Naɗewa - 25

BABI NA UKU

3.0 Shinfiɗa - 26

3.1 Nau'in bincike - - 26

3.2 Sigar bincike - - 26

3.3 Kayan Aikin bincike - 27

3.4 Ginshiƙan Bayanai - 27

3.4.1 Karanta Ayyuka A Ɗakunan Karatu - 27

3.4.2 Tattaunawa da Wasu 'Yan Tauri  - 28

3.4.3 Tattaunawa da Masana Da Manazarta A Kan Tauri  - 30

3.4.4 Tattaunawa da Masana ilimin tauri  - 31

3.4.5 Juyowa da Sauraren Hira da Aka Yi da Makaɗin Tauri Sale kudo - 33

3.5 Ɗa'ar Gudanar da bincike - 33

3.6 Naɗewa  - 34

BABI NA HUƊU

4.0 Shinfiɗa - 35

4.1 Tubalan Gina Turken Zuga A Waƙoƙin Tauri Na Sale Kudo Kusada - 35

4.2 Tubalan Kamantawa - 35

4.2.1 Tubalan Kamantawa ta Daidaito  - 37

4.2.2 Tubalan Kamantawa Ta Fifiko  - 39

4.2.3 Tubalan Kamantawa Ta Gazawa (Kasawa) - 41

4.3 Tubalan Kambamawa - 44

4.3.1 Tubalan Kambamar Zulaƙe - 44

4.3.2 Tubalan Kambamar Yabo - 47

4.4 Tubalan Alamtarwa - 48

4.4.1 Tubalan Alamtarwar Amfani Da Abu Marasa Rai  - 49

4.3.2 Tubalan Amfani Da Abu Masu Rai  - 51

4.5 Tubalan Siffantawa - 54

4.5.1 Tubalan Gajeriyar siffantawa  - 55

4.5.2 Tubalan Doguwar siffantawa  - 57

4.6 Tubalan Dabbantarwa - 59

4.6.1 Tubalan Amfani Da Dabbobin Gida - 60

4.6.2 Tubalan Amfani Da Dabbobin Daji - 62

4.7 Tubalan Abuntarwa - 63

4.7.1 Tubalan Abubuwa Masu Motsi  - 65

4.7.2 Tubalan Abubuwa Kafaffu - 67

BABI NA BIYAR

5.0 Shinfiɗa - 70

5.1 Taƙaita Bincike - - 70

5.2 Sakamakon Bincike - 71

5.3 Gudummuwar Bincike - 72

5.4 Shawarwarin Bincike - 72

5.5 Naɗewa - 73

Manazarta - 74

Rataye - 77

Rataye - 80

BABI NA ƊAYA

1.0 Shinfiɗa

Wannan babi zai yi bayani ne a kan dalilin bincike da manufar bincike da muradan bincike da tambayoyin bincike da kuma iyakancewar bincike da gudummuwar bincike.

Duk a cikin babin za a kawo ma'anar adon harshe da ta kirari sannan za a yi bayanin ma'anar Tauri da kuma tarihin makaɗin Tauri Sale Kudo a dunƙule.

1.1 Dalilin Bincike

Bincike ne da aka gabatar domin ƙara samar da abun bita ga ɗalibai da masu Nazarin Harshen Hausa, musamman a ɓangaren Al'ada da Adabi, sannan an gabatar da binciken ne domin cikasa wata ƙa'ida ta samun takardar digiri na biyu. Haka kuma binciken zai ƙara fito da waɗansu hikimomi na azancin magana da ke ƙunshe cikin Kirarin makaɗan Tauri domin nusar da mai karatu ko nazari. Duk yana daga cikin dalilin wannan bincike nazartar waɗansu ɓangarori da suka haɗa wasu turakun zuga da ya ƙunshi kanantawa wadda ta haɗo da kamance na daidaito da na fifiko da kuma na gazawa, sannan kambamawa da jinsintarwa da abuntarwa da Dabbantarwa da Alamtarwa da kuma kinaya a matsayin matakan zuga 'yan tauri a cikin kiɗa.

1.2 Manufar Bincike

Manufar wannan bincike an gina shi ne a kan fito da wasu abubuwa da suka shafi wasu sifofi da halaye na rayuwar al'ummar Hausawa kamar yadda makaɗin Tauri Sale Kudo yake kawo wa a cikin kiɗansa, haka kuma za a fito da yanayin Zugar kuma za a yi sharhi da bayanin maƙunshiya na zugar da ya ke furtawa a lokacin da ya ke yi wa Ɗan Tauri kiɗa.

1.3 Muradin Bincike

  1. Binciko ire-iren hikimomin zance masu alaƙa da zuga da makaɗin Tauri yake amfani da su a lokacin da ya ke wa 'yan Tauri kiɗa
  2. Fito da yadda ya ke sarrafa harshe a cikin kaɗe-kaɗen 'yan Tauri da nuna ƙarfin maganinsa ta hanyar danganta shi da wasu halittu.
  3. Taskace halayen abubuwan da ya ke alaƙanta 'yan Tauri da su.
  4. Zayyano ire-iren abubuwan da ya ke lissafowa domin kambama ɗan Tauri
  5. Tantance yadda makaɗin ke duba halayyar wasu abubuwa cikin Waƙoƙin nasa.

1.4 Tambayoyin Bincike

Dukkanin binciken ilimi yana da wasu keɓantattun tambayoyi da ake sa ran zai amsa su, saboda haka shi ma wannan bincike ya zo da waɗansu tambayoyi kamar haka:

(I)                Yaya Makaɗin Tauri yake sarrafa harshe cikin Waƙoƙin Tauri?

(II)     Waɗanne abubuwa ne makaɗin Tauri ya fi mayar da hankali a kansu lokacin da ya ke wa ɗan Tauri Zuga?

(III)  Ta wace hanya makaɗin Taurin yake gina maganganun zuge-zugensa?

(IV) Ta ya Ma'anar kalmomin da makaɗin Taurin ke faɗi ke juyawa zuwa ga ɗan Taurin da ya ambata da wannan kalma?

1.5 Iyakancewar Bincike

Wannan Bincike zai samu iyakancewar Nazarin turken zuga a Waƙoƙin tauri na Sale Kudo Kusada, a cikin kiɗansa da yake wa 'yan Tauri, Maza da suke a kewayen ƙaramar Hukumar Kusada ta Jahar Katsina.

1.6 Gudummuwar Bincike.

Wannan Bincike ya zo da waɗansu gudummuwa kamar haka;

I.                    Haskawa manazarta da sauran ɗaliban ilimi irin yadda ake amfani da Halayen dabbobi da sifofinsu domin tsoratar da abokan hamayya.

II.                 Samar da abun bita ga ɗaliban ilimi masu sha'awar nazari a harshen Hausa domin cikasa wani giɓi da kila binciken bai rufe ba.

III.              Karawa rubuce-rubucen fannin 'yan tauri yawa ta hanyar fayyace Ma'anoni na abubuwan da suka shafi Waƙoƙin tauri.

IV.              Adana salon sarrafawa harshe na wasu 'yan tauri ta yadda ba za su salwance ba.

1.7 Turken Zuga

Newman (2007) ya bayyana koɗa kai da nufin wasa ko kururuta wani.

Bargery (1934) a nasa ya bayyana koɗa da wasa kai ko nuna fifiko.

Gusau, (2008) ya yi bayani a kan turken Zuga

Koɗa kai (wasa kai) a waƙar baka a inda tun a farko ya fara da cewa „magori wasa kanka da kanka, koɗa kai ko wasa kai na nufin mutum yafaɗi wata shahara ko ƙasaita ko ɗaukaka da yake ganin yana da ita. Wato ambato ne na abubuwan ƙasaita ko burgewa da mutum yake da su ko yake aiwatarwa. Wani bi akan haɗa da wuce gona da iri inda mutum zai bayyana fifikonsa a kan sauran jamaa, ko ya nuna wata zalaƙarsa ko basirarsa wasu da sauran hanyoyin fifitawa.

A irin wannan hali mutum yakan zuga kansa da kansa ne. Masanan sun yi bayani gwargwadon fahimtarsu a kan koɗa kai kuma sun yi tararraya don gane da abin da koɗa kai yake nufi, wato fito da wata shahara ko isa ko fifiko da wani mutum yake da shi. Kodayake, Gusau ya yi nazari a kan turken koɗa kai a waƙar baka ya fito da misalan ire-iren wasu waƙoƙin baka ne da ake samu mawaƙa sun koɗa kansu a ciki amma shi wannan bincike zai kalli wasu ɗiya ne daga cikin Waƙoƙin Sale Kudo kusada da kuma irin yadda ya yi amfani da wasu kalmomi domin nuna zuga ko koɗa wani ko wasu jamaa ko kuma kansa.

1.7.1 Sarrafa Harshe

Sarrafa Harshe ɗaya ne daga cikin rassan adabin baka. Masana Harshen Hausa sun bambanta wajen ambatom wannan reshe na Adabin Baka. Farfesa Ɗangambo (1984), ya ambace shi da Hikima da sarrafa Harshe, wanda daga nan muka ciro wannan suna. Sai kuma Yahaya, Zariya, Gusau da 'Yar adua (1992), suka kira shi da ''Azancin Magana".

Zarruk, Kafin Hausa da Alhassan (1987), sun ambace shi da ''salon Magana". Amma dukkan su sun yarda da zamowar: Kinaya da Siffantawa da Jinsintarwa da Abuntarwa da Kambamawa da kuma Dabbantarwa a matsayin rassan Sarrafa Harshe.

Sarrafa Harshe Salo ne da Bahaushe yake amfani da shi wajen sarrafa magana ta sigogi mabambanta da ke ƙayatar da zance ko isar da wani babban saƙo ta cikin hikima kuma a wasu 'yan kalmomi dunƙulallu. Da su ake yi wa zance ( na baka ko rubutacce) ado; Adon Harshe.

Adon Harshe dabara ce ta yi wa magana (kirari) kwalliya domin ƙara ma shi armashi da daɗi wanda shi ne ma'auni na gwada iya zance da balagar ɗan Adam ke da ita ga Harshensa da kuma sauran abubuwan da ke kewaye da shi. Adon Harshe dai a taƙaice yana nufin wasu hikimomi ne ko dabaru da ake bi wajen kauce wa miƙaƙƙiyar hanyar faɗar magana a rubuce ko a baka.

1.7.2 Ma'anar Kirari

Zarruƙ da Alhassan (1982 : 45), sun bayyana cewa kirari na ɗaya daga cikin wani ginshiƙi ko ɓangare da ake bayyana al'adar al'umma kuma ya ke adana tarihi da taimaka wa al'umma wajen ci gaba kamar kuma yadda ya ke taimakawa wajen nishaɗantarwa, ilimantarwa, da faɗakarwa.

Yahaya (1992) yace kirari maganganu ne na kambamawa da ake yi wa mutum ko kuma shi ya yi ma kansa, kirari kan ƙara kwarzanta wanda ake yi wa. Ana amfani da ƙwarewar zance wurin yin kirari.

Sayaya (2013: 41) yana ganin cewa kirari kalma ce wadda ta samo asali daga kira wato makaɗi ne zai sa ganga ya Kira gwarzonsa ko kuma wani lokaci a busa masa ƙaho. Wato a busa ƙaho a Kira shi.

Bunza (2009) Asalin kalmar daga Kira take a sa kalangu ko ganga ko murya a kira wani da ƙarfi don ya fito a ɗebe tababan abunda ake faɗa a kansa.

Dunfawa (2004 : 38) yana da ra'ayin cewa kirari shi ne jera jimlolin Adabi masu amfani da kalmomi waɗanda ko dai su kasance masu kaifin ma'ana ko masu zurfin ma'ana kuma waɗanda aka tsara salon siffantawa domin wasa ko kambamawa ko ingiza mutum ko wani Abu.

Junaidu da 'Yar'adua (2007) sun bayyana kirari da cewa ''wani rukuni ne na salon sarrafa harshe da Hausawa kan yi amfani da shi wajen nuna gwaninta da ƙimar harshe, ta hanyar tsara kalmomi da suka dace da halayyan abubuwa a cikin lugga mai ban sha'awa.

A tawa fahimtar ina ganin Kirari zantuka ne na hikima da ake furtawa cikin zaɓaɓɓun jimloli domin kwarzanta kai ko fito da ƙima ko matsayi domin burgewa da tsoratar da abokan hamayya.

1.7.3 Ma'anar Tauri

Sayaya (2009 : 40) Ya bayyana Tauri da cewa kalmar tauri na nufin gagara ko ƙin sarrafuwar wani abu a sakamakon wasu dalilai na musamman da suke bambanta yanayin abubuwa. Ire-iren waɗannan dalilai sun haɗa da sinadarai da mutum ke samu daga itatuwa. Ko tsirrai, ko wasu abubuwa ya yi amfani da su domin kare kansa daga rauni da wani makami da ka iya yi masa.

Bunza (1995) yana mai ra'ayin cewa Tauri yana nufin abu yaƙi bari a sarrafa shi ta yadda ake so. ko mutum ya faye ƙin karɓar shawara a kan ce wane taurin kai gare shi. Mai irin wannan asiri na maganin ƙarfe ana kyautata zaton wuƙa da takobi da mashi da duk wani makami na ƙarfe ba su fasa jikinsa ba. Haka kuma yana iya sarrafa ƙarfe yadda yake so, ba tare da wata wahala ba.

Buhari (2022 : 12) Tauri tsumi ne na itatuwa da mutum kan sha ya yi wanka domin samun kariya daga kowane irin kaifi ko tsini da ƙarfe ke da shi. Irin waɗannan itatuwa akan sarrafa su wani lokacin har da sassan jikin dabbobi domin bayar da irin wannan kariya ta rauni da ƙarfe kan iya yi wa mutum.

1.7.4 Waƙoƙin Tauri

Waƙar Tauri tana daga cikin rukunin waƙoƙin baka na maza da suka keɓanta ga masu aiwatar da wata sana'a ta musamman. Waƙoƙi ne da ake shiryawa cikin sigar kirari tare da kiɗa da take a lokaci guda.

Makaɗin tauri kan ɗauki turken wani makaɗi ya gina nasa turken, kasancewar su babu wani makaɗin tauri da ya yi wa kiɗan haye sai ya bi wani makaɗi kafin ya fara nasa kiɗan, duk da cewa da yawansu sukan yi gado ne a gida wurin mahaifansu.

Kiɗan tauri yana bambanta dangane da yankin da makaɗan taurin suka fito, kamar a ƙasar katsina makaɗan tauri sukan yi amfani da Bishi ne wurin kiɗan tauri Saɓanin ƙasar Kano da suke amfani da Gangi domin aiwatar da kiɗan nasu. Haka kuma waɗanda suka fito shiyyar Zamfara suna amfani da Kalangu, makaɗan yankin Kebbi sukan yi amfani da Duma ko Ganga da kuma Kalangu a wurin kiɗan tauri, su kuwa na Katsina ta kudu da wani yanki na Nijar sukan yi amfani da Kurya wajen kiɗan tauri. Wato dai kiɗan yakan bambanta da shiyyoyin da makaɗan suka fito duk da cewa abu ɗaya ne suke kiɗa a kansa.

1.8 Tarihin Makaɗin Tauri Sale Kudo A Dunƙule

An Haifi Malam Sale Kudo a Ƙauyen Magami cikin ƙaramar Hukumar kusada dake a Jahar Katsina kimanin shekaru sittin da suka wuce. sunan mahaifinsa Malam Audu, sunnan mahaifiyarsa Maimuna mutumiyar ƙauyen Magami ce. Anan ya tashi ya girma kuma ya fara karatun Allo a hannun abokin Babansa sai dai daga bisani mahaifin nasa ya miƙa sa hannun wani Malam Adamu, wanda ya tafi da shi ƙasar Zazzau domin yin karatu, Sale Kudo ya samo karatu sosai sai dai bai sauke ba suka dawo gida, daga nan ya ci gaba da karatu a wurin Malaminsa na farko har zuwa wani lokaci.

Sale Kudo bai yi karatun zamani ba sai dai ya yi yawon neman abinci a kudancin Najeriya kamar su Lagos da Abuja inda ya yi sana'o'i daban-daban waɗanda suka haɗa da gyaran takalmi (shoe maker) da yankan farce da sayar da rake da sauransu.

1.8.1 Asalin Inkiyar Kudo

Sunansa na Asali Salisu, sai dai mutane na ce masa Kudo saboda tun yana ƙarami abokan wasa suka sa masa Kudo kuma yake amsa sunan, bayan da ya shahara a kiɗan tauri sai sunan ya ƙara fitowa sosai ta yadda in ba an haɗa da kudo ba sunan ba ya tasiri akansa.

1.8.2 Yanayin Sale Kudo

Sale Kudo baƙi ne dogo mara jiki ya ɗan duƙa ya yi doro, yana da gashi a bisa kansa sannan ba ya barin gemu a haɓarsa, yana ajiye gashin baki, ga iya magana sai dai ba shi da murya sosai ko waƙa yake bakasafai muryar ke fita ba, yana yawan sa riga kwot kuma duk kayan da zai sa zai ɗora wannan kwot a sama. Mutum ne mai fara'a ma'abocin cin goro.

1.8.3 Sana'oin Sale Kudo

Bayan Sale Kudo ya bar karatun allo, ya fara bin abokan sa zuwa daji da nufin yin farauta da kuma saro itace suna kawo wa zuwa cikin garin Kusada suna sayarwa, daga nan suke kamo namun daji su yanka su babbake suna sayarwa a kasuwannin Rimaye da Kankiya da kuma Kusada.

Wannan ya yi sanadin faɗawarsu cikin farauta ka-in-da-na-in wannan sana'a ta sanya shi jarunta ya kasance ba shi da tsoro, har mahaifinsa ya lura da irin yadda ya mayar da hankali a Kan harkar farauta ya fara ba shi laƙani na kariyar jiki da sauran tambaya.

Bayan farauta Sale Kudo ya fara sana'ar noma, tun lokacin da yana taya mahaifinsa aiki, har bayan da ya yi iyali ya ci gaba da wannan harka ta noma inda ya ware gonar kansa, haka kuma bayan noman damina Kudo yana yin noman rani, tun a baya Sale Kudo ya yi sana'oi daban-daban.

1.8.4 Sana'ar Kiɗan Tauri

Sale Kudo ya gaji sana'ar kiɗan tauri a wurin mahaifinsa sai dai kafin ya fara kiɗan bishi da can kiɗan kalangu ya ke yi, Sannu a hankali ya fara amfani da bishi har ta kai ya jingine kalangu ya kama kiɗan tauri.

Ya tsunduma cikin kiɗan sosai lokacin da Hakimin Kankiya ya bukaci Babansa da ya je su tafi Katsina hawan sallah, sai mahaifinsa ya umarce shi da ya ɗauki ganga ɗaya ya bi tawagar Kankiyan Katsina su tafi domin shi ba zai iya barin tawagar Bebeji ba Hakimin Kusada kasancewarsa a ƙarƙashin gundumarsa. Haka Sale ya je Katsina aka yi wasan sallah lafiya a ka gama, ganin haka sai Babansa ya bashi ganga guda ta sa ta kansa kuma ya ci gaba da ba shi dabarun kiɗan har zuwa lokacin da ya haƙura da kiɗan taurin ya kasance salen ya mamaye duka ƙasar Hakimin Kankiya da kuma ta Kusada a matsayin shahararren makaɗin taurin yankunan.

Sale kudo ya yi kiɗe-kiɗen tauri da yawa ciki hadda irin su:

• Kiɗan Sarkin ƙyarma Yarima

• Kiɗan ɗan Sarauta

• Kiɗan Sarki Gambo

• Kiɗan Sarkin Dawa Zubairu

• Kiɗan Bahago Taushe Dama Badamasi

• Kiɗan Saminu Kan Kara Kafi Ɗaka

• Kiɗan Musa ba ka san faƙo

• Kiɗan kwangi

• Kidan kwakyara

Da sauransu.

1.9 Garin kusada

Garin Kusada yana daga cikin ƙananan Hukumomin Jahar Katsina, wadda a ka ƙirƙira a shekar 1996. Gari ne na Malamai da ake wa kirari da ''Kusada kusa da Kano nesa da Birnin Katsina'' Al'ummar wannan gari mafi yawansu Manoma ne da makiyaya kuma garin ya albarkatu da 'yan kasuwa da ma'aikatan gwamnati, in aka duba taswira garin ya yi iyaka da ƙaramar Hukumar Kankiya daga yamma, daga gabas kuma ya yi iyaka daTsanyawa ta jahar Kano, a ɓangaren kudu garin na Kusada ya yi iyaka da ƙaramar Hukumar Ingawa.

A ƙididdigar mutane da aka yi a shekarar 2006 garin yana da kimanin adadin mutane miliyan ɗaya da ɗari tara da tisi'in da biyu da ɗari biyu da bakwai (1992, 267). Garin yana da ƙauyuka da suke kewaye da shi, Alhaji Nuhu Sada shi ne Bebejin Katsina Hakimin Kusada na yanzu a ƙarƙashin ikonsa akwai Dagattai guda goma sha uku da suka hada da: kofa da Tufani da Magami da Yashe da Ɓauranya da Kusada da Kafarda da Aganta da Mawashi da Dudunni da Boko da kuma Kaikai. Haka kuma kowane Dagaci yana da masu Unguwanni kamar yadda tsarin Sarautar gargajiya ya shinfiɗa.

1.10 Naɗewa

Wannan babi an bayyana abubuwa kamar haka gabatar da babin wadda a cikinta ne aka bayyana abinda wannan binciken ya ƙunsa da kuma abubuwan da babi suka yi magana . Haka kuma bayan gabatarwa babin ya bayyana abubuwa kamar haka, muhimmancin bincike da manufar Bincike da farfajiyar bincike da dalilin ci gaba da bincike da tambayoyi da taƙaitaccen tarihin makaɗin Tauri da kuma garin Kusada. 

Post a Comment

0 Comments