Ticker

6/recent/ticker-posts

Miyar Guro Ko Kubewa

Miyar guro/ kuɓewa tana daga cikin ’ya’yan wani nau’in tsiro da Hausawa ke shukawa a gida ko a gona da nufin amfani da ita a lokacin da aka buƙaci gudanar wannan nau’i na miya. Akan yi miyar da ɗanyar kuɓewa ko kuma busasshiya. Yayin miyar ta ɗanyar kuɓewa, to sai an yayyanka ta tukuna. Haka ma yayin busar da kuɓewar, ana yayyanka ta ne, a shanya ta har sai ta bushe, sannan kuma a dake ta a mai da ita gari.

Ɗanyar kuɓewa na iya kasancewa mai laushi, wadda ita ce ta fi kyau da tagomashi a wajen samar da nau’in miyar ɗanyar kuɓewa. Amma wadda ta riƙa ta yi tauri, akan yanka-yanka ta ne a shanya domin sarrafa ta a wurin samar da nau’in miyar busasshiyar kuɓewa.

Mahaɗin Miyar Kuɓewa

Abubuwan da ake tanada yayin miyar kuɓewa sun haɗa da:

i. Albasa          

ii. Daddawa    

iii. Guro           

iv. Kayan Yaji

v. Mai              

vi. Ruwa        

 vii. Tarugu      

viii. Tattasai

ix. Nama ko kaza ko kifi (idan da hali)

Yadda Ake Miyar Guro (Kuɓewa)

Abu na farko da za a yi shi ne a wanke guro sosai a yanka ta da wuƙa. Sannan idan da nama za a yi, ana iya tafasa shi tare da albasa da magi da gishiri kaɗan. A gefe guda kuma, za a daka daddawa da kayan yaji a aje gefe ɗaya. Sannan a soya kayan miya kamar yadda aka yi a miyar kuka. Daga nan za a ɗora sanwa, tamkar dai yadda aka bayyana a nau’o’in miya da aka bayyana a baya.

Bayan sanwa ta dahu, za a kawo kuɓewa a sanya. Idan miyar da kifi za a yi, to ba a sanya kifin har sai bayan an sanya kuɓewa. Sai a ɗan saka kanwa kaɗan ba da yawa ba, kuma za a buɗe marfin tukunya kaɗan. Buɗe tukunyar zai hana miyar zubewa, domin da zarar kuɓewar ta fara nuna, za ta riƙa kumfa da cika tukunya. Sau da dama akan yi amfani da ludayi domin motsa miyar gudun kada ta zuba.

Tsokaci 

Za a iya cewa, babu wani gari a ƙasar Hausa da ba a shan miyar kuɓewa. Duk da haka, shan miyar guro yana kawo illa musamman ga mata masu jego, masu bayar da nono ga jarirai (masu shayarwa). Shan miyar guru ga mai jego na tsinkar da kaurin nono tare da rage yawansa. A shawarce, ya kamata mai jego ta nisanci miyar guro, har sai jaririnta ya yi wayo. 

The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology. Data is collected from interviews with different categories of people including: i.          Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets. ii.         People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas. iii.        Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets. Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas. The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.). Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes. Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food. 7th November 2022
Citation: Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments