Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Ya Sumbace Ni Na Fitar Da Maziyyi Alhalin Ina Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam mace ce ta yi kitso alhalin tana azumi sai mijinta yaga kitson ya basa sha'awa saiya sumbacesa ita kuma take sha'awa tazo mata harta jika pant ɗinta. Menene hukuncin azuminta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To yar uwa da farko dai anyi wasa da azumi kwarai da gaske kuma ba daidai bane kina azumi ki bari mijinki ya sumbaceki ta yadda har zaki fitar da wani abu dazai ɓata miki azumi' wannan akwai ganganci a ciki.

Amma shi azumin nafila dama mai shi yanada yan'cin ya karyashi koya cigaba Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya faɗa cikin hadisi sahihi mai azumin nafila shi ne sarkin kansa idan yaga dama ya karya. manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya bada wannan damar.

Malamai suna cewa fitar maziyyi idan har maziyyine ya fita karamar sha'awa kenan zance mafi inganci baya karya azumi amma idan maniyyi ne ya fita to azumi ya karye shi ke nan idan na nafila ne bakida lada idan kuma farilla ne akwai kaffara akansu bisa kaulin malamai amma wasu malaman sukace sai anyi jama'i kaffara take wajabta idan nafilane shi ke nan idan kuma na farillah ne saiki rama guda ɗaya wannan shi ne zance mafi inganci

Allah shi ne mafi sani

Amsawa: Dr Abdallah Gadon kaya

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments