Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Yin Sallar Tarawihi A Masallaci Bidi’a Ce Kyakkyawa?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Wani ne ya ce yin sallar tarawihi a masallaci bidi’a ce kyakkyawa saboda Sayyiduna Umar ya ce: Ni’imatil Bidi’ah Haazihi! Sannan kuma wai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) bai yi tarawihin a cikin jama’a ba, a cikin gida shi kaɗai ya yi. Wane ƙarin bayani malam zai yi a mahangar Ahlus-Sunnah wacce babu gauraye?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Da farko dai Al-Imaam Al-Bukhaariy (924) ya fitar da hadisi daga Ummul-Mu’mineen A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa) cewa

أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم - خَرَجَ ذَاتَ لَيْلَةٍ مِنْ جَوْفِ اللَّيْلِ ، فَصَلَّى فِى الْمَسْجِدِ ، فَصَلَّى رِجَالٌ بِصَلاَتِهِ فَأَصْبَحَ النَّاسُ فَتَحَدَّثُوا ، فَاجْتَمَعَ أَكْثَرُ مِنْهُمْ فَصَلَّوْا مَعَهُ ، فَأَصْبَحَ النَّاسُ فَتَحَدَّثُوا فَكَثُرَ أَهْلُ الْمَسْجِدِ مِنَ اللَّيْلَةِ الثَّالِثَةِ ، فَخَرَجَ رَسُولُ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم - فَصَلَّوْا بِصَلاَتِهِ ، فَلَمَّا كَانَتِ اللَّيْلَةُ الرَّابِعَةُ عَجَزَ الْمَسْجِدُ عَنْ أَهْلِهِ حَتَّى خَرَجَ لِصَلاَةِ الصُّبْحِ ، فَلَمَّا قَضَى الْفَجْرَ أَقْبَلَ عَلَى النَّاسِ ، فَتَشَهَّدَ ثُمَّ قَالَ « أَمَّا بَعْدُ فَإِنَّهُ لَمْ يَخْفَ عَلَىَّ مَكَانُكُمْ ، لَكِنِّى خَشِيتُ أَنْ تُفْرَضَ عَلَيْكُمْ فَتَعْجِزُوا عَنْهَا »

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya fita a cikin wani dare ya yi sallah a masallaci, sai waɗansu daga cikin Sahabbansa suka yi sallah tare da shi. Sai suka bayar da labari, sai kuma waɗanda suka fi su suka taru suka yi sallah tare da shi. Sai su kuma suka bayar da labari, sai kuma jama’a suka yi yawa a cikin masallaci a dare na uku. Sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya fita suka yi sallah tare da shi. A dare na huɗu sai masallacin ya kasa ɗaukar jama’a, shi kuma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) sai a lokacin sallar Asubah ya fita. Bayan ya yi sallar Asubah sai ya fuskanci mutane ya yi shimfiɗa da Kalmar Shahada, sannan ya ce: Bayan haka, haƙiƙa matsayinku a cikin daren nan fa bai ɓoyu a gare ni ba. Sai dai na ji tsoron kar a farlanta muku ne, kuma ku zo ku kasa yi.

A wata riwayarsa (lamba: 1129) da ƙarin bayanin cewa

وَذَلِكَ فِى رَمَضَانَ

Kuma wannan a cikin Ramadan ne.

A wata riwayar kuma (lamba: 2012) akwai ƙarin cewa:

فَتُوُفِّىَ رَسُولُ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم - وَالأَمْرُ عَلَى ذَلِكَ

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya rasu alhali al’amarin yana nan a haka.

Waɗannan riwayoyin da masu kama da su masu yawa sun nuna cewa

1. Yin jam’in sallar Tarawihi ko Asham ko Tahajjud a cikin masallaci a cikin dararen watan Ramadan Sunnah ne, domin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi har na tsawon dare uku tare da Sahabbansa.

2. Annabin Rahama mai tausayi ga al’umma (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya dakatar da hakan ne kawai domin tsoron da ya ji kar Allaah ya farlanta sallar a kan al’umma, kuma su kasa yi.

3. Haka nan Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya rasu ya bar al’umma ba a yin wannan sallar a masallaci, har tsawon zamanin halifancin Abubakar As-Siddeeq, har zuwa farkon zamani Umar Al-Faaruuq (Radiyal Laahu Anhumaa).

Wannan tsoron ya kau a bayan rasuwar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) bayan Allaah Ta’aala ya kammala wa wannan al’ummar dokokin shari’ar addini.

Tun da dai hukunci yana gudana tare da illarsa ce, to gushewar illar da ta hana jam’in sallar ta dalilin rasuwar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ta sa hukuncin farko na halacci jam’in ya komo kenan.

Shiyasa Sayyiduna Umar (Radiyal Laahu Anhu) ya sake rayar da wannan Sunnar, kamar yadda Abdurrahman Bn Abd Al-Qaariy ya ce

خَرَجْتُ مَعَ عُمَرَ بْنِ الْخَطَّابِ لَيْلَةً فِي رَمَضَانَ إِلَى الْمَسْجِدِ ، فَإِذَا النَّاسُ أَوْزَاعٌ مُتَفَرِّقُونَ ، يُصَلِّي الرَّجُلُ لِنَفْسِهِ ، وَيُصَلِّي الرّضجُلُ فَيُصَلِّي بِصَلَاتِهِ الرَّهْطُ ، فَقَالَ : [ وَاللهِ ] إِنِّي لَأَرَى لَوْ جَمَعْتُ هَؤُلَاءِ عَلَى قَارِىءٍ وَاحِدٍ لَكَانَ أَمْثَلَ ، ثُمَّ عَزَمَ فَجَمَعَهُمْ عَلَى أُبَيِّ بْنِ كَعْبٍ [ قَالَ ] : ثُمَّ خَرَجْتُ مَعَهُ لَيْلَةً أُخْرَى ، وَالنَّاسُ يُصَلُّونَ بِصَلَاةِ قَارِئِهِمْ [ فَ ] قَالَ عُمَرُ : نِعْمَتِ الْبِدْعَةُ هَذِهِ ، وَالَّتِي يَنَامُونَ عَنْهَا أَفْضَلُ مِنَ الَّتِي يَقُومُونَ ، يُرِيدُ آخِرَ اللَّيْلِ ، وَكَانَ النَّاسُ يَقُومُونَ أَوَّلَهُ "

Na fita tare da Umar Bn Al-Khattaab a cikin wani dare na Ramadan zuwa Masallaci, sai ga mutane a rarrabe daban-daban: Wani yana sallah shi kaɗai, wani kuma yana sallah tare da ’yan jama’an da ba su kai goma ba. Sai ya ce: Wallahi! Ina ga da zan haɗa waɗannan a bayan limami guda da ya fi daidai. Sai kuwa ya yi aniya ya tara su a bayan Ubayy Bn Ka’ab. Abdurrahman ya ce: Sai muka sake fita tare da shi a wani daren kuma, sai ga mutane suna sallah a bayan limaminsu, sai Umar ya ce: Madalla da wannan bidi’ar! Amma wacce suke yin barci kafin su yi ta fi wacce suke yin ta a yanzu falala. Mutane kuma a farkon dare suke yi a lokacin. (Maalik: 249)

Malamai suka ce: Waɗansu mutane sun yawaita kafa hujja da maganar nan ta Umar cewa: ‘Ni’imatil Bid’ah Haazihi’ a kan abubuwa guda biyu

1. Wai haɗuwar mutane wurin yin sallar tarawihi bidi’a ce, ba a yi shi ba a zamanin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba, sai a zamanin Umar (Radiyal Laahu Anhu)!

Wannan kuwa mummunar ɓarna ce, domin hadisan da suka gabata na sallarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) tare da jama’a har na tsawon darare uku sun isa su ƙaryata wannan da’awar. Kuma dakatar da cigaba da ya yi ba yana nufin soke hukuncin ba ne, sai dai domin gudun kar a mayar da sallar dare ta zama farilla ce kawai.

2. Wai daga cikin bidi’o’i akwai bidi’a kyakkyawa wacce har take zama abin yabo. Da wannan maganar ce wai suka keɓance gamammiyar maganarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa: ‘Kullu Bid’atin Dalaalah’ watau: Kowace bidi’a ɓata ce.

Wannan ma dai ba daidai ba ne, saboda dalilai masu yawa kamar haka

1. Kowace kalma a wurin malamai tana da ma’ana ko fassara biyu ne: Fassara a harshe ko al’adar Larabawa, sai kuma Fassarar da Shari’a ta kawo. Kamar Kalmar Sallah: A harshen Larabawa ma’anarta kawai ita ce addu’a, kamar yadda ya ce: ‘Wa Salli Alaihim’ watau: Kuma ka yi musu addu’a. Amma ba wai: Ka yi musu sallah mai kabbara da karatu da ruku’u da sujada da sauransu kamar yadda aka sani ba.

2. Bidi’a a cikin harshen Larabci ita ce

 الْأَمْرُ الْحَدِيثُ الْجَدِيدُ الَّذِي لَمْ يَكُنْ مَعْرُوفًا قُبَيْلَ إِيجَادِهِ

watau: Ƙirƙirarren abu sabo wanda ba a san shi ba kafin wani ya samar da shi. Amma a Shari’a kuwa bidi’a ita ce

إِحْدَاثُ شَيْءٍ فِي الدِينِ عَلَى غَيْرِ مِثَالٍ سَابِقٍ

 watau: Ƙirƙiro wani abu a cikin addini, wanda ba shi da wani misali da ya gabace shi.

3. Ba zai yiwu maganar Umar (Radiyal Laahu Anhu) ta ɗauki ma’anar bidi’a a cikin shari’a ba, domin kamar yadda ya ke a fili, shi bai ƙirƙiri komai ba a cikin addini. Kaɗai rayar da sunnar Ma’aiki (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ce ya yi.

4. Maganarsa sai dai ta ɗauki fassarar Bidi’a a harshen larabci, watau: Sabon abin da mutane ba su saba da shi ba a iya tsawon zamanin Abubakar da farkon zamanin Umar (Radiyal Laahu Anhumaa).

4. Haka manyan malamai muhaƙƙiƙai suka fassara wannan maganar ta Umar (Radiyal Laahu Anhu), kamar su Ibn Abdilbarr, da Abdulwahhaab As-Subkiy da Ibn Hajr Al-Haitamiy (Rahimahumul Laah).

(Salaatut Taraaweeh na Al-Allaamah Al-Albaaniy).

Sannan kuma maganar Sayyiduna Umar cewa: ‘Wacce suke barci sannan su yi ta ta fi wacce suke yi yanzu falala’ ya nuna sallar jama’a a ƙarshen dare ta fi ta masu yi farkon dare, saboda falalar ƙarshen daren a kan farkonsa. Amma idan a tsakanin yin sallar tare da jama’a a farkon dare da kuma yin ta shi kaɗai a ƙarshen dare ne, to farkon daren ya fi saboda dalilai kamar haka

1. Abu-Daawud ya faɗa a cikin Al-Masaa’il, shafi: 62 cewa

  سَمِعْتُ أَحْمَدَ قِيلَ لَهُ : يُعْجِبُكَ أَنْ يُصَلِّيَ الرَّجُلُ مَعَ النَّاسِ فِي رَمَضَانَ أَوْ وَحْدَهُ ؟

Na ji an tambayi Ahmad cewa: Mutum ya yi sallah tare da mutane a cikin Ramadan ne ya fi burge ka ko kuwa ya yi shi kaɗai?

قَالَ : يُصَلِّي مَعَ النَّاسِ

Ya ce: Ya yi sallah tare da mutane.

2. Ya ce

وَسَمِعْتُهُ أَيْضًا يَقُولُ : يُعْجِبُنِي أَنْ يُصَلِّيَ مَعَ الْإِمَامِ ، وَيُوتِرَ مَعَهُ

Kuma na ji shi yana cewa: Na fi sha’awar ya yi sallah tare da liman kuma ya yi wutri tare da shi.

قَالَ النَّبِيُّ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " إِنَّ الرَّجُلَ إِذَا قَامَ مَعَ الْإِمَامِ حَتَّى يَنْصَرِفَ ، كَتَبَ اللهُ لَهُ بَقِيَّةَ لَيْلَتِهِ "

Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: Shi dai mutum idan ya tsaya sallah tare da liman har kuma ya yi sallama, to Allaah zai rubuta masa tsayuwar sauran daren.

Haka kuma Ibn Nasr ya kawo a cikin Al-Masaa’il, shafi: 91.

3. Sai kuma Abu-Daawud ya ce

 " قِيلَ لِأَحْمَدَ وَأَنَا أَسْمَعُ : يُؤَخَّرُ الْقِيَامُ - يَعْنِي التَّرَاوِيحَ - إِلَى آخِرِ اللَّيْلِ ؟

An tambayi Ahmad alhali ina ji: Za a iya jinkirta sallar tarawih zuwa ƙarshen dare?

 قَالَ : لَا ، سُنَّةُ الْمُسْلِمِينَ أَحَبُّ إِلَيَّ

Sai ya ce: Sunnar da musulmai suke a kanta ta fi soyuwa gare ni.

Allaah ya ƙara mana fahimta.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments