Ticker

6/recent/ticker-posts

Ramuwar Azumi Ga Mara Lafiya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam A bani shawara: Na kamu da wata cuta ta zubar da yawu wanda bana iya kai azumi yau shekara uku kenan, nasha azumi 23 da farko, shekara ta zagayo ban samu sauki ba na kuma shan 20 kuma ina tsoron kada wata shekaran ta riskeni shine na auno masara mudan nabi 43 akan akwai makwabtanmu yaran marayu ne, shin idan na basu na biya azumi na ko ko? Nagode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam In har akwai tabbacin ciwon ba zai warke ba ka rama azumin, kana iya ciyarwa. Amma in har akwai tunanin za ka warke to ba za ka ciyar ba, saboda wajibi akan mara lafiyan da ya sha azumi saboda lalura ya rama a wasu kwanakin na daban kamar yadda Allah yake cewa:

وَمَن كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ

"Kuma wanda ya kasance mara lafiya bai azumci Ramdan ba, to ya rama abin da ya sha a kwanaki na daban" (Suratu Al-bakarah aya ta 185).

Aya ta (184) a cikin surar ta nuna wanda ya sha azumi saboda rashin lafiya ko tsufa kuma babu tunanin ya samu damar ramawa nan gaba zai iya ciyarwa

أَيَّامًا مَّعْدُودَاتٍ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ فِدْيَةٌ طَعَامُ مِسْكِينٍ فَمَن تَطَوَّعَ خَيْرًا فَهُوَ خَيْرٌ لَّهُ وَأَن تَصُومُوا خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ 

 Kwanuka ƙidãyayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam. Kuma a kan waɗanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya ƙãra alhri to, shi ne mafi alhri a gare shi. Kuma ku yi azumi (da wahalar) ne mafi alhri a gare ku idan kun kasance kuna sani. (Suratul Bakara aya ta 184)

A bisa abin da ya gabata In har likita ya tabbatar za ka samu damar ramawa nan gaba to azumin yana nan akanka, ciyarwa ba za ta wadatar maka ba.

Sannan in har ciyarwa ce ta halatta akanka ai ba mudun-nabi ake bayarwa ba !!!

Allah ne mafi sani

DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments