Ticker

6/recent/ticker-posts

Matar Da Jinin Haila Ya Zo Mata Sau Biyu A Cikin Kwana Goma Sha-Biyar

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, ya gida ya azumi, don Allah malam ina da tambaya, in lokacin hailata ya zo ina yin kwana 6 da shi, to wannan karon ya zo min na yi kwana 6, sai na ga alamun tsarki na yi wanka na yi azumina na rana ɗaya, washe gari na sake tashi da azumi daidai qarfe Tara na safe sai na ga wani jini yana fita, to wannan jinin na hailan ne ko kuma istihada ne? Kuma ya matsayin azumin jiya da na yi kuma zan rama ne ko kuma yana nan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, duk matar da jinin haila ya zo mata sau biyu a cikin kwana goma sha biyar, to da jinin farko da na biyu duka haila ɗaya ne, misali kamar yadda kika ce; kin kasance kina yin al'ada na kwana shida, da kwana shidan suka cika, da aka kwana biyu sai ya dawo, to a nan tun da tsakanin jini na farko da jini na biyu ba a sami kwana sha-biyar ba, to za ki lissafa shi ne a matsayin jinin farkon nan ne ya sake dawowa, saboda malamai sun bayyana cewa Sai idan jinin haila ya cika kwana sha-biyar bai ɗauke ba ne yake zama jinin istihala, kuma a tsakanin haila zuwa wata haila sai ya kai kwana sha-biyar musamman a maz'habar Malikiyya, a wata maz'habar kuma kwana sha uku, saboda haka wannan jini da ya sake dawo maki ba jinin ciwo (istihadha) ba ne, jinin hailan nan ne ya sake dawowa.

Shi kuma hukuncin azumin da kika yi na ranar farko da jinin ya yanke, wannan azumi ya inganta, amma azumin washe gari da jinin ya sake dawo maki, wannan azumi ya ɓaci, za ki rama shi in Allah ya kai mu bayan sallah, saboda duk azumin da aka yi shi a cikin jinin haila wannan azumin bai inganta ba, idan ma da gangan aka yi, to ya zama laifi domin Shari'a ta hana, idan kuma da kuskure ne kamar wannan, to babu laifi, saboda Allah ya yafe wa al'ummar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam abin da suka yi shi da kuskure, kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya faɗa a wani hadisi.

Allah ne masani.

Dr. Jamilu zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments