Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Fidda Maniyyi Da Azumi Ta Hanyar Istimna'i

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Slm malam sama da so uku ke nan ina tura tambaya amma kuma ba amsa min, malam dan Allah a taimaka a amsa min wannan, akwai wani a unguwarmu, shi dai yana yawan yin istmna'i kuma baya yin wankan janaba sama da mako guda kuma yanayin azumi, kuma yana yin sallah da janaban, munyi munyi mun kasa hanashi, yaki ya haqura, in ya tuba daga bisani sai ya fara. Toh mallam Allah ya saka maka da alkhairi

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Dukkanin Malamai sun yi Ittifaki akan cewa duk wanda ya fitar da Maniyyi daga jikinsa da gangan, acikin ranar da yake azumi to azuminsa ya karye.

Sauran Maluman suna ganin cewar zai rama azumi guda ɗaya ne. Amma Imamu Malik yace wajibi ne sai ya yi ramukon tare da kaffarah. (Wato Azumi 61 kenan) akan kowanne azumin Ramadan guda wanda ya karya.

Idan kuma cikin dare yake yin istimna'in, to wannan rashin tsarkin jikinsa ba zai shafi azuminsa ba. Azuminsa yana nan.

HUKUNCIN YIN SALLAH DA JANABAH

Yin Sallah da Janabah, yana daga cikin mafiya girman Kaba'irori. Hasali ma yin hakan da gangan kamar yin riddah ne.

Ya zama wajibi ku gabatar da wannan mai laifin agaban Hukumar Musulunci. ko kuma wajen Malaman Unguwarku ko garinku.

Za'a tambayeshi dalilinsa na yin wannan ta'asar. Idan yana yin hakan ne saboda lalaci, ba tare da sanin haɗarin dake cikin yin hakan ba, to za'a umurceshi da tuba sannan yaje ya yi wankan Janabah kuma ya rama dukkan sallolin da yayisu da janabar.

Idan kuma yana sane da cewa ba'a yin sallah sai da tsarki, Kuma yasan hatamcin yin sallah da janaba, amma ya yi ne da gangan, Ko kuma shi ara'ayinsa bai yarda da wajibcin tsarkin hadasin ba, to ya kafirta.

Hukuma zata iya zartar masa da haddi mutukar dai an tabbatar da cewa acikin hayyacinsa yake, shi ba Mahaukaci bane.

Ya kamata kuyi ma shari'ah gata, Ku ɗauki matakin kaishi gaban manya domin ladabtar dashi.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments