Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wacce Jinin Haila Ta Yanke Mata Ba Ta Yi Wanka Ba Sai Bayan Fitowar Alfijir

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Idan mace hailarta ta yanke kafin fitowar Alfijir amma ba ta yi wanka ba sai bayan fitowar alfijir yaya azuminta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Idan mace jinin hailarta ta ya yanke kafin fitowar Alfijir ko da da minti ɗaya ne matukar ta tabbartar da jinin ya yanke da auduga ko da farin kyale to azuminta bai ɓaci ba.

Don ta yi azumi ne lokacin da jininta ya ɗauke. Koda yake ba ta yi wanka ba sai da Alfijir ya keto, to ba komai a kanta, hakanan kuma da za ta wayi gari da janaba amma ba ta yi wanka ba Sai bayan fitowar Alfijir to Azumin ya yi.

Da wannan ne na ke so na ja hankalin mata don wasun su sukan yi buɗe baki bayan rana ta faɗi amma ba su yi sallah ba sai jini ya zo musu suna gani kamar ba su da wannan azumin.

Wannan magana tasu ba ta da asali tun da ta riga ta sha ruwa kuma rana ta faɗi, ko da minti ɗaya ne sai jini ya zo mata to babu abin da ya shafi azuminta.

Allah ta'ala yasa mudace

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments