Ticker

6/recent/ticker-posts

Mafarkin Saduwa

TAMBAYA (78)

Salamu alaikum. Malam miye hukuncin wanda yayi mafarkin ana saduwa dashi. Yana tashi bacci yaga har yayi releasing?

AMSA

Waalaikumussalam, warahmatullahi, wabarakatuhum

Alhamdulillah

Tabi'i kuma malaminnan na fassarar mafarki Imam Muhammad Ibn Seerin (Rahimahullah) ya ce: mafarkin saduwa da namiji na nufin fadawa tarkon zunubi, ko kuma fadawa tarkon zina da wata daga cikin danginku ko kuma aikata zina da wadda babu aure a tsakaninku. Mafarkin zina da bawa na nufin masifa da bala'i wanda za'a dade ba'a fita ba

Kwanciya da kyakkyawar mace a mafarki na nufin ribar kasuwa (profits) zina da mummunar mace kuma na nufin karayar arziqi. Saduwa da matar wani a mafarki na nufin qulla alaqar kasuwanci da mijin. Idan mara lafiya yayi mafarkin yana zina da mahaifiyar sa hakan na nufin mutuwarsa, anan mahaifiyar na nufin duniya

SHARHI

Hukuncin hakan shine, indai har tayi releasing to wankan janaba ya wajaba a gareta. Sannan kuma shawarar da zan bayar anan shine; idan da hali, ki tsayar da mijin aure mai addini da rufin asiri. Sannan kuma ki dinga karanta azkar din da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya koyar idan mutum zai kwanta bacci

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments