Hukuncin Yin Rinin Gashi (Dyeing)

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum Pls meye hukuncin chanja wa gashin kai kala ma'ana yima gashi kai dying saboda yakara baki, shin ko ya halatta?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam warahamtullahi Wabarkatuh

    Jabir bin Abdullah ya ruwaito cewa anzo da Abu Quhaafa a ranar buɗe Makkah, gashin kansa da gemunsa fari ne sosai kamar "thaghaamah" (wata plant ce wacce furenta da 'ya'yanta farare ne fet), sai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce: Ka canza wannan (farin gashin) da wani abu, amma kar kayi (amfani) da baqi. ( Muslim ya ruwaito shi, 3962).

    Ibn Abbas (Allah ka yarda dashi) ya ce: Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce: A karshen zamani za'ayi wasu mutane masu rine baqin gashinsu (ya koma) kamar gashin tantabara (Saboda farinsa), bazasu taɓa jin kamshin aljannah ba. (Imam Ahmad ya ruwaito shi, duba Saheeh al-Jaami‘, hadisi mai lamba 8153).

    An ruwaito daga Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) cewa ya umarni da canza kalar gashi daga launin kore zuwa kowace irin colour amma banda baqin kala. Abu Dharri ya ruwaito cewa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce: Abu mafi kyau na canza kalar koren gashi shine lalle (henna) da katam (wata ciyawa mai kamar lalle da ake canza gashi da ita, ana kiranta "gadon maciji" a wani yanki na kasar Hausa). (Tirmizi ya ruwaito shi, 1675. Kuma ya hassana shi).

    Yin rinin gashi (dyeing) da baqin dye zallah haram ne. Saboda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce "Kar kayi (amfani) da baqi". Amma idan za'ayi haɗin baqin dye da wani kala ayi mix babu laifi domin bazai bada baqar kala zallah ba. Duba (Fatawa al-Islamiyyah 4/424, da Fatawa al- mar’ah al-Muslimah 2/520).

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.