𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, malam don Allah yin allura yana karya azumi idan mutum bai ji shi ta makogwaron shi ba?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salam, yin allura ba
ya karya azumi a zance mafi inganci, sai dai fa idan ya zamo allurar abinci ne,
wanda idan aka yi shi zai je uwar hanji ya samar da qoshi, amma matuqar allura
ba ta abinci ba ce babu laifi idan aka yi ta da azumi, kamar yadda malamai suka
tabbatar. Amma idan da za a bari sai bayan shan ruwa da daddare sannan a yi
allura, to hakan ya fi kyau.
Sannan kuma allura ba a lissafa
ta a cikin jinsin ci ko sha, ko cikin abin da ake kira abinci ko abin sha,
hakan sai yake qara nuna cewa yin ta ba ya karya azumi matuqar ba wadda take sa
qoshi ba ne.
Duba Fataáwál Lajnatid Daá'ima
10/252. Ko Majmu'u Fataáwá na Sheikh Ibn Bazz 15/257.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.✍🏻
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.