𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin wai gaskiyane cewa duk Mace
Mai-Ciki ko Mai Shayarwa zata iya ajje azumi ta ciyar kawai amadadinsa kokuma
ya abin yake??
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Ko Shakka bābu cewa wannan magana
ba gaskiya bace domin kuwa bahaka Shari'a tace ayiba, danhaka dai da farko yana
dakyau musani cewa bawai haka kawai dan saboda kasancewar Mace tana da Ciki ko
tana Shāyarwa hukuncin yin azumi yafāɗi
akantaba, domin dayawa daga cikin 'Yan'uwa Mātā sunyiwa wannan hukunci mummunar
fahimta, kodai wasu saboda Jāhilcinsu ko saboda son zuciya kokuma saboda ƙarancin
bayani daga wajen su Mālaman
da suke basu fatawa akan hakan, domin dayawa daga cikin Ɗāliban-Ilimi zaka samu suna bada fatawane kawai akan
cewa Mai-Ciki da Mai Shāyarwa
zasu ciyarne kaɗai
amadadin azuminsu, wanda kuma bahaka hukuncin yake a Sake ba Ƙaidi
ba.
idan Mai-Ciki ko Mai Shāyarwa
kokuma Maras lāfiya sunājin ƙarfin jikinsu yadda zasu iyayin azumi
batare da sun galabaita irin galabaitar da ta sāɓāwa
yadda akasaba gani abisa al'āda ba, to wajibine akansu suyi wannan azumin, idan
kuma sukaƙiyi
to susani cewa sunbar wani wājibi
da Aʟʟαн(ﷻ) Ya wajabta musu
suyi, kuma Sai Aʟʟαн(ﷻ) Yākamasu da laifin
hakan domin Shidai Aʟʟαн(ﷻ) baza'a iya yimasa ƙarya
ko wayoba, amma idan yakasance Mutum yana cikin laulayin da idan yayi azumi zai
tagayyara irin tagayyarar da yawuce na al'ada, kamar misalin Mutum yafita daga
hayyacinsa ko yariƙa suma saboda wahala ko wani abu makamancin haka, kokuma yin
azumin zai iya ƙāra
cutar datake dāmunsa
ko tayi jinkirin warkewa kokuma yakamu da wata sabuwar rashin lafiyar adalilin
azumin dayayi, to anan sai Shari'a tayimasa rangwame akan cewa zai iya cin
abincinsa, daga baya kuma idan yawarke sai yarama adadin azumin da yasha, amma
ba dalili bane wai kaji Mace tace wai azumi yana bata wahala danhaka bari tasha
ruwa itama bayan Sallah sai taciyar, wannan wasane da addini kawai, domin kuwa
ana maganane akan irin wahalar da ta sāɓāwa
irin wahalar da aka saba ji a al'ada, amma inba hakaba ai koma waye zaiyi azumi
dole sai yaji ajikinsa
Danhaka kuskurene babba Mutum
yarika wasa da lamarin addininsa, Sannan wasu daga cikin Mutāne kuma sukayi
wani wāyo na son zuciya, yāyin da akace Mālamai sunyi Saɓāni akan wata Mas'ala ta Fiƙhu,
to kawai sukan dubane suga wanne ɓangarene
yafi sauƙi
sai su ɗauka suyi
amfani dashi, ko shakka babu wannan kuskurene babba, domin kuwa idan Mālamai
sukayi Saɓāni to
anasone Mutum yaɗauki
ɓangaren da yake da
Dalilai da Hujjoji masu ƙarfi koda kuwa shine ɓangaren
da yafi wahala ɗin,
Aʟʟāн(ﷻ) Ya gānar damu
gaskiya ya bāmu ikon aiki da'ita Āmīn-Yā-Rabbi.
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ
AMSAWA
Mυѕтαρнα Uѕмαn
08032531505
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.