Ticker

6/recent/ticker-posts

Istimna’i Da Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Saurayi ne mai shekaru 19 ya tsinci kansa a cikin mummunan halin yin istimna’i har a cikin azumi. Ina hukuncin wannan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Istimnaa’i shi ne mutum ya yi amfani da hannunsa ko wata na’ura a gabansa har ya biya buƙatarsa ta hanyar fitar da maniyyi. Malamai sun saɓa wa juna a kan hukuncin wannan aikin, amma maganar da ta fi bayyana a wurinmu ita ce maganar waɗanda suka ce: Shi haram ne. Saboda maganar Allaah Ta’aala

وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ

(Muminai bayin Allaah na-gari) su ne kuma waɗanda suke karewa ga al’aurorinsu. (Suratul Muminina Aya ta 5)

إِلَّا عَلَىٰ أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ

Sai dai ta hanyar matan aurensu ko kuma kuyanginsu kawai, to lallai kam su (a nan) ba abaiban zargi ba ne. (Suratul Muminina Aya ta 6)

فَمَنِ ابْتَغَىٰ وَرَاءَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْعَادُونَ

Duk wanda kuma ya nemi wata hanya a bayan haka, to waɗannan su ne masu ƙetare haddi. (Suratul Muminina Aya ta 7).

Abu ne a fili kuwa cewa: Amfani da hannu ko wata na’ura, kamar budurwar roba ko saurayin roba wasu hanyoyi ne a bayan haka, watau a bayan aure ko amfani da kuyanga. Don haka ya shiga ƙarƙashin ƙetare haddi.

Wannan shi ne asali.

Amma ko ya halatta ga matasa waɗanda ba su da aure, kuma suka ji tsoron faɗawa a cikin zina ko luwaɗi da sauransu a ba su fatawar cewa su riƙa aikata wannan?

Malamai sun nuna ba kai-tsaye ba ne, har sai in an fara da gwada waɗansu matakan da shari’a ta kawo don yin maganin matsalar kuma ba a samu nasara ba, kamar waɗannan

1. Saurayi ya fara da yin yaƙi da ransa, har ya fi ƙarfinta ya hana ta aikata saɓo.

2. Ya yawaita yin Isti’aazah: Neman Allaah ya tsare shi daga yaudara shaiɗan.

3. Ya yi ƙoƙarin zama mai khushui da ƙanƙan da kai ga Ubangijinsa a cikin sallah.

4. Ya yawaita yin azumin nafila saboda Allaah, da neman kashe kaifin sha’awarsa.

5. Ya yawaita karatun Alqur’ani da lura da ma’anoninsa da yin aiki da koyarwarsa.

6. Ya kula da Zikirorin Safiya da Maraice da kwanciya barci da farkawa da sauransu.

7. Ya nisanci cin duk abinci ko abin shan da aka san suna ƙara motsar da shaawa.

8. Ya riƙa runtse ganinsa daga kallon tsiraici a koina, kamar waya da TV da sauransu.

9. Ya nisantar da kansa daga cakuɗa da mata ko da muharramansa ne, sai da larura.

10. Ya nisanci abokan banza waɗanda za su ja shi, ko su zuga shi ga saɓon Allaah.

11. Ya yawaita addu’a da ƙanƙan da kai ga Allaah, don ya kare shi daga wannan masifar.

Amma fa ya riƙa tunawa da maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

إِنْ تَصْدُقِ اللهَ يَصْدُقْكَ

Idan ka gaskata Allaah zai gaskata ka. (Sahih An-Nasaa’iy: 1845).

(A duba: Buluughul Munaa Fee Hukmil Istimnaa’i na As-Shaikh Mas-huur Al-Salmaan (Hafizahul Laah)).

Sannan game da hukuncin wanda ya aikata wannan mummunan aikin a cikin azumi, watau wanda ya yi amfani da hannunsa ko wata na’ura kamar budurwar roba ko namijin roba ya fitar da maniyyi daga gare shi, malamai sun saɓa wa juna

1. Waɗansu malamai suna ganin wanda ya yi hakan azuminsa ya ɓaci, saboda hadisin da Al-Imaam Al-Bukhaariy da Al-Imaam Muslim suka riwaito mai cewa

« يَتْرُكُ طَعَامَهُ وَشَرَابَهُ وَشَهْوَتَهُ مِنْ أَجْلِى »

Yana barin abincinsa da abin shansa da sha’awarsa saboda ni. (Sahih Al-Bukhaariy: 1894, Sahih Muslim: 2763).

Suka ce: Wanda ya yi amfani da hannunsa don fitar da maniyyi, bai bar sha’awarsa saboda Allaah ba. Don haka, azuminsa ya ɓaci! (Tamaamul Minnah: 2/154).

2. Wasu malaman kuma suka ce: Azuminsa bai ɓaci ba, domin babu wani dalili da ya nuna ɓacin azumin saboda haka. Musamman ma dayake wasu daga cikin waɗanda suka zaɓi cewa azumin ya ɓaci, ba su kuma yarda da cewa akwai kaffara a kansa ba. Suka ce: Domin abin da ya yi ba daidai ya ke da jima’i ba! Jima’i ya fi kauri, don haka babu ƙiyasi a tsakaninsu!

Kamar haka, sai waɗannan malaman su ma suka ce: A asali azumin mai istimna’i ma bai ɓaci ba, saboda jima’i ya fi istimna’in kauri, kuma babu ƙiyasi a tsakaninsu! (Al-Awaayshah ya tattauna wannan masalar a cikin Al-Mausuuah: 3/314-318).

Amma a kan hadisin da waɗancan suka jawo, sun bayar da martani da jawabai kamar haka:

1. Asalin hadisin a cikin Sahih Al-Bukhaariy (1894) shi ne

عَنْ أَبِى هُرَيْرَةَ - رضى الله عنه - أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ - قَالَ « الصِّيَامُ جُنَّةٌ ، فَلاَ يَرْفُثْ وَلاَ يَجْهَلْ ، وَإِنِ امْرُؤٌ قَاتَلَهُ أَوْ شَاتَمَهُ فَلْيَقُلْ إِنِّى صَائِمٌ . مَرَّتَيْنِ ، وَالَّذِى نَفْسِى بِيَدِهِ لَخُلُوفُ فَمِ الصَّائِمِ أَطْيَبُ عِنْدَ اللَّهِ تَعَالَى مِنْ رِيحِ الْمِسْكِ ، يَتْرُكُ طَعَامَهُ وَشَرَابَهُ وَشَهْوَتَهُ مِنْ أَجْلِى ، الصِّيَامُ لِى ، وَأَنَا أَجْزِى بِهِ ، وَالْحَسَنَةُ بِعَشْرِ أَمْثَالِهَا »

Daga Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) cewa: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: ‘Azumi garkuwa ne, (a ranar azumin ɗayanku) kar ya yi batsa, kuma kar ya yi wauta. Idan kuma wani mutum ya nemi yin faɗa da shi, ko ya nemi su zagi juna da shi, sai ya ce: Ni mai yin azumi ne. Na rantse da wanda rayuwata ke ga hannunsa, sauyin bakin mai yin azumi ya fi ƙamshi a wurin Allaah Taaala fiye da turaren miski: Yana barin abincinsa da abin shansa da shaawarsa saboda ni. Azumi na wa ne, kuma ni nake bayar da sakayyarsa. Kuma kyakkyawan aiki guda daidai da guda goma kwatankwacinsa ne.

Kalmar: Sha’awarsa a cikin hadisin, saduwar jima’i da matarsa ake nufi, ba istimna’i ba. Ibn Hajr Al-Asqalaaniy (Rahimahul Laah) ya kawo riwayoyin da suka bayyana haka a cikin Fat-hul Baariy: 5/574-575, ya ce

وَالْمُرَادُ بِالشَّهْوَةِ فِي الْحَدِيثِ شَهْوَةُ الْجِمَاعِ لِعَطْفِهَا عَلَى الطَّعَامِ وَالشَّرَابِ

Abin nufi da Sha’awa a cikin Hadisin shi ne: Sha’awar jima’i, saboda an goya ta a kan abinci da abin sha.

Sai ya cigaba da kawo bayanai da riwayoyi a kan haka, har dai zuwa inda ya ce

وَأَصْرَحُ مِنْ ذَلِكَ مَا وَقَعَ عِنْدَ الْحَافِظِ سَمَوَيْهِ فِي فَوَائِدِهِ مِنْ طَرِيقِ الْمُسَيَّبِ بْنِ رَافِعٍ عَنْ أَبِي صَالِحٍ : يَتْرُكُ شَهْوَتَهُ مِنَ الطَّعَامِ وَالشَّرَابِ وَالْجِمَاعِ مِنْ أَجْلِي

Kuma abin da ya fi fitar da wannan fassarar a fili shi ne abin da ya zo a wurin Al-Haafiz Samawaihi a cikin littafinsa Al-Fawaa’id ta hanyar Al-Musayyib Bn Raafi’i, daga Abu-Saalih cewa: Yana barin Sha’awarsa na abinci da abin sha da jima’i saboda ni.

Don haka dai: Maganar waɗannan malaman na ƙarshe ita ta fi a fahimtarmu. Sannan kuma abin da ya wajaba ga wannan saurayin shi ne

1. Ya tuba ga Allaah Ta’aala tuba ta gaskiya a kan wannan laifin da ya yi.

2. Ya nemi Allaah Ta’aala ya gafarta masa wannan ɗanyen aikin da ya aikata.

3. Ya yi nadama da baƙin ciki da da-na-sani a kan wannan ɓarnar da ya tafka.

4. Kuma ya ɗaura niyyar cewa: Ba zai sake komawa ga sake aikata wani irin laifin makamancin wannan ba, har zuwa ƙarshen rayuwarsa.

Muna taya shi da addu’ar Allaah ya ƙara tsare masa alaurarsa, ya kiyaye shi har zuwa lokacin yin aurensa. Allaah ya taimake mu gaba ɗaya.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments