Ticker

6/recent/ticker-posts

Lokacin Shan Ruwa (Buda Baki)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam khamis Muna godiya sosai. Allah ya saka muku da alkhairi Ameen. Tambaya ta anan shine Yaushe ne lokacin buɗa baki (shan ruwa) kuma wacce addu'a ake yi lokacin buɗa baki?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

Lokacin buɗa baki yana tabbata ne da zarar rana ta faɗi. Dalili kuwa shine, hadisin da aka karbo daga Malik, daga Abdurrahman ɗan harmala al Aslami, daga Sa'eed ɗan al Musayyabi, yace: Lallai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, ya ce: "Mutane baza su gushe ba suna cikin alkhairi matuƙar za su gaggauta yin buɗa-baki"

Muwatta Malik (640)

Yana daga cikin sunnah ta Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama yin gaggawa wajen buɗa-baki idan yakai azuminsa, har ma yake kwaɗaitar damu cewa mu ma muyi koyi dashi wajen yin gaggawar buɗa-bakin sabida tarin alkhairin dake cikin yin hakan.

Haka hadisin da aka karbo daga Abdullahi Ibn Abī Auf yace: "ya kasance tare da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam a lokacin tafiya suna azumi, sai rana ta faɗi, sai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace da wani daga cikin sahabbansa ya sauka ya shirya musu kayan buɗa baki sai sahabin yace: "Ya Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam da sauran rana, akayi haka har sau uku, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam na cewa dashi ya shirya musu abin buɗa baki. Daga karshe bayan sun kammala sai Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yace: “Idan kuka ga dare ya gabato daga nan (wato rana ta faɗi), haqiqa mai azumi ya buɗe bakinsa (ana nufin koya sha ruwa ko bai sha ba)

Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.

Daga Ansa bn Malik(RA) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya kasance yana yin buɗe baki kafin ya yi sallah da danyen dabino, idan bai samu danyen dabino ba sai yayi da busassun dabino, idan kuma bai samu busasshen ba, sai ya kurɓi wasu kurɓi na ruwa". Tirmidhi ya ruwaitoshi.

Idan ka kai azuminka, ka jaraba fara yin buɗa-baki da dabino, ko ruwa, tabbas za kaga amfanin hakan, domin shawara ce daga bakin wanda ba ya cutarwa.

Amma don ka yi buɗa-baki da wani abu saɓanin dabinon ko ruwa, wannan ba laifi kayi ba, domin ai Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama ba umurni yake ba ka ba a cikin wannan hadisin, shawara ce dai kawai ya ba ka, amma za ka iya yin buɗa-bakinka da duk abun da kake sha'awar ci idan lokacin buɗa-bakin ya yi.

«ADDU'AR BUƊA BAKI»

ذَهَبَ الظَّمَأُ وَابْتَلَّتِ الْعُرُوقُ، وَثَبَتَ الأَجْرُ إِنْ شَاءَ اللَّهُ

FASSARA: Ƙishirwa ya tafi, an yayyafawa jijiyoyi ruwa, kuma lada ya tabbata in Allah ya so.

(Abu Dawud)

ADDU'A IDAN MUTUM YAYI BUƊA BAKI A GIDAN WASU MUTANE

أَفْطَـرَ عِنْدَكُم الصّـائِمونَ وَأَكَلَ طَعامَـكُمُ الأبْـرار، وَصَلَّـتْ عَلَـيْكُمُ الملائِكَـة.

FASSARA: Allah yasa masu azumi su yi buɗa baki a wajenku, kuma Allah yasa nagartattun bayi su ci abincinku, kuma Allah yasa Mala'iku su yi muku addu'a.

(Abu Dawud 3/367, Ibn Majah 1/556)

Mai azumi a lokacin da zai yi buɗa baki (kafin ya ci ko ya sha wani abu) addu'arsa karɓabbe ne ba a mayar da shi.

(Tirmidhi)

Ƴan uwa haƙiƙa addu'armu a wajen buɗa baki karɓaɓɓiya ce, saboda haka muyi addu'o'i muna masu sakankancewar an karɓa mana, amma mu sani cewa Allah baya karɓar addu'ar wanda zuciyarsa rabkananniya ce mai wasa daga ambaton Allah.

Allah Ta'ala ya amsa mana.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments