Ticker

6/recent/ticker-posts

Ibadun Da Mai Haila Zata Iya Yi A Watan Ramadan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamou Alaikum wa Rahmatullah! Malam Allah ya kara ilimi mai amfani! shin Malam wanne irin ibadu ne ya kamata mace dake haila ta yi a cikinikin Ramadan ganin ita ba ta azumi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salámu. Kasancewar an hana masu haila yin Sallah da azumi bai dace hakan yasa su zama kasalallu a wannan wata mai alfarma na Ramadan ba. Saboda wannan ba wata ne na wasa da kasala a ibadoji ba.

Mata masu haila ba a haramta masu yin zikirin Allah ba, yana da kyau su dage da yin takbiri, da tasbihi, da tahmidi, da tahlili, da istigfari, da sauran duk zikirorin Allah.

Suna da damar sauraron karatun Alqur'ani, da sauran ilmomi na addini. Amma a game da su karanta Alqur'ani da kansu kuwa malamai sun yi saɓani, daga cikin malamai akwai masu fahimtar hana mai haila karanta Alqur'ani, amma a fahimta ta biyu kuma suna da damar karanta Alqur'ani da ka, ba tare da taɓa Almus'haf ba, wannan fahimtar ta fi zama daidai.

Harwayau, masu haila suna da damar yin umurni da kyakkyawa da hani da mummuna, kuma su dage wurin ciyar da masu azumi sadakar abinci gwargwadon iko, da sauransu.

Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IqsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments