Ticker

6/recent/ticker-posts

Lokacin Sallar Asubah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Ina yin Qiyaamul Layli amma ba na kai wa lokacin kiran sallar Asubah. Ina yin sallar Asubar ce a daidai lokacin da aka yi kiran sallar farko kafin a kira Asalatu. Shin sallata ta yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Ramatul Laah

Qiyaamul Layl aikin alkhairi ne. Lokacinsa daga bayan sallar Isha’i ne zuwa kafin ketowar alfijir na gaskiya. Yin sa a ƙarshen dare kafin ketowar alfijir ya fi yin sa a farkon dare. Domin ƙarshen dare shi ne lokacin saukowar Ubangiji Tabaaraka Wa Ta’aala zuwa saman duniya domin karɓar addu’o’i da buƙatu da neman gafarar bayi, kamar yadda hadisai sahihai suka nuna

« يَنْزِلُ رَبُّنَا تَبَارَكَ وَتَعَالَى كُلَّ لَيْلَةٍ إِلَى السَّمَاءِ الدُّنْيَا حِينَ يَبْقَى ثُلُثُ اللَّيْلِ الآخِرُ يَقُولُ مَنْ يَدْعُونِى فَأَسْتَجِيبَ لَهُ مَنْ يَسْأَلُنِى فَأُعْطِيَهُ مَنْ يَسْتَغْفِرُنِى فَأَغْفِرَ لَهُ »

Ubangijinmu Mai Albarka da Ɗaukaka yana saukowa zuwa saman duniya lokacin da sulusin ƙarshe na dare ya rage, yana cewa: Wa zai yi addu’a gare ni, in amsa masa? Wa zai roƙe ni, in ba shi buƙatarsa? Wa zai nemi gafara daga gare ni, in gafarta masa? (Sahih Al-Bukhaariy: 1145).

Allaah ya ƙara mana dacewa.

Kiran sallar asubah guda biyu ne: Ana kiran na-farko kafin ketowar alfijir na gaskiya, ɗayan kuma a bayan ketowar alfijir na gaskiya. Bambancinsu shi ne: Ana faɗin As-Salaatu Khairum Minan Nawm a ɗaya, ban da ɗayan. Waɗansu ladanai a kiran sallar farko suke yin As-Salaatu Khairum Minan Nawm! Amma a Sunnah sahihiya ana faɗin As-Salaatu Khairum Minan Nawm ne a kiran sallar farko kawai. Haka Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa wa Abu-Mahzuurah (Radiyal Laahu Anhu) lokacin da ya koya masa kiran sallah, ya ce

« وَإِذَا أَذَّنْتَ بِالأَوَّلِ مِنَ الصُّبْحِ فَقَلْ الصَّلاَةُ خَيْرٌ مِنَ النَّوْمِ الصَّلاَةُ خَيْرٌ مِنَ النَّوْمِ ».

Idan kuma ka zo kiran sallar farko na Asubah sai ka ce: As-Salaatu khairum Minan Nawm, As-Salaatu Khairum Minan Nawm. (Ahmad: 15772, kuma Shu’aib Al-Arnaa’uut ya sahhaha shi saboda yawan hanyoyinsa a cikin ta’aleeqinsa ga Masnad: 3/408).

Haka ma Sahabi Ibn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa) ya faɗa

كَانَ فِى الأَذَانِ الأَوَّلِ بَعْدَ الْفَلاَحِ : الصَّلاَةُ خَيْرٌ مِنَ النَّوْمِ ، الصَّلاَةُ خَيْرٌ مِنَ النَّوْمِ

Ya kasance a cikin kiran sallar farko bayan ‘Al-Falaah’ akwai: As-Salaatu Khairum Minan Nawm, As-Salaatu Khairum Minan Nawm. (Al-Baihaqiy a cikin Sunan Al-Kubraa: 2066, kuma Al-Albaaniy ya hassana shi a cikin Tamaamul Minnah, shafi: 147).

Hikimar hakan, in ji malamai: Domin a farkar da mai barci, ko kuma a faɗakar da mai Qiyaamul Layl cewa lokacin Sallar Asubah ya kusa. Idan yana da waɗansu addu’o’in da zai yi sai ya zauna ya yi su, ko idan yana buƙatar yin sahur a lokacin azumi sai ya samu ya yi kafin ketowar alfijir na gaskiya.

Lokacin sallar Asubah yana farawa ne daga ketowar alfijir na gaskiya, wanda haskensa ke cika sasannin gabas. Shi ne wanda daga shi sai fashewar hasken safiya, sai kuma wayewan gari. Amma alfijir na-ƙarya wanda yake cirawa sama kamar bindin kura shi ne wanda ake kiran sallar Asubah da farko a cikinsa, amma lokacin sallar Asubah ba ne. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« الْفَجْرُ فَجْرَانِ: فَجْرٌ يَحْرُمُ فِيهِ الطَّعَامُ وَتَحِلُّ فِيهِ الصَّلَاةُ، وَفَجْرٌ تَحْرُمُ فِيهِ الصَّلَاةُ وَيَحِلُّ فِيهِ الطَّعَامُ »

Alfijir nau’i biyu ne: Alfijir wanda a cikinsa abinci ke halatta kuma sallah take haramta; sai kuma alfijir wanda a cikinsa sallah take haramta kuma abinci yake hallata. (Al-Haakim: 687, kuma Al-Albaaniy ya sahhaha shi a cikin As-Saheehah: 693).

Daga cikin fiqhun wannan hadisin ne Al-Albaaniy ya kawo maganar ta Ibn Khuzaimah wanda ya ce

في هذا الخبر دلالة على أن صلاة الفرض لا يجوز أداؤها قبل  دخول وقتها. و قال : (فجر يحرم فيه الطعام) يريد على الصائم. (و يحل  فيه الصلاة) يريد صلاة الصبح. (و فجر يحرم فيه الصلاة) يريد صلاة الصبح ، إذا طلع الفجر الأول لم يحل أن يصلي في ذلك الوقت صلاة الصبح ، لأن الفجر الأول  يكون بالليل ، و لم يرد أنه لا يجوز أن يتطوع بالصلاة بعد الفجر الأول. و قوله:  (و يحل فيه الطعام) يريد لمن يريد الصيام .

A cikin wannan hadisin akwai dalili a kan cewa bai halatta a yi sallar Farilla kafin lokacinta ba. Kuma da ya ce: (alfijir da abinci ke halatta a cikinsa) yana nufin ga mai son yin azumi. (Kuma sallah take halatta a cikinsa) yana nufin sallar Asubah. (Kuma alfijir wanda sallah ke haramta a cikinsa) yana nufin sallar Asubah, idan alfijir na farko ya keto bai halatta a yi sallar farilla ta Asubah a wannan lokacin ba. domin alfijir na-farko yana kasancewa a cikin dare ne, ba wai yana nufin ba ya halatta a yi sallar nafila a bayan hudowar alfijir na-farko ba ne. Maganarsa cewa: (kuma abinci yake halatta a cikinsa) yana nufin ga wanda ke son yin azumi. (Silsilah Saheehah: 2/192).

Daga wannan ya bayyana a fili kenan cewa:

Abin da mai tambaya ke yi na yin sallar Asubah a bayan kiran sallar farko kafin a kira na-biyu, ba daidai ba ne. Domin lokacin sallah bai shiga ba a lokacin.

Kuma abu ne sananne cewa, ba a yin sallah sai a bayan shigan lokacinta, saboda maganar Allaah Ta’aala cewa

إِنَّ الصَّلَاةَ كَانَتْ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ كِتَابًا مَوْقُوتًا

Haƙiƙa, sallah a kan muminai ta kasance farilla ce mai iyakantaccen lokaci. (Surah An-Nisaa’: 103).

Tun da ita mai iyakantaccen lokaci ce, wannan ya nuna duk wanda ya yi ta kafin lokacinta to bai yi sallah ba, a haɗuwar dukkan malamai. Haka ma wanda ya yi ta a bayan ficewar lokacinta ba da dalili karɓaɓɓe a shari’a ba, a wurin muhaƙƙiƙai daga cikin malamai.

Don haka, wajibi ne a kan wannan mai tambayar ta tuba ga Allaah a kan abin da ta kasance tana aikatawa, kuma ta daina yin sallah kafin shigar lokacinta ko da me, ko don me! Sannan ta kusanci malamai domin sanin dokoki da ƙa’idojin ibadarta ga Ubangijinta.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments