Ticker

6/recent/ticker-posts

Lokacin Fara Zikirin Safe Da Yamma

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam wane lokaci ya kamata mutun ya fara azkar wato zikirin safe da yamma?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

Ibnul Qayyeem acikin littafinsa Alwabilul sayyeeb, yayi bayanin lokacin da ake fara zikirin safe da kuma yamma, kuma yarinjayar da maganarsa da cewa ana yin na yamma bayan sallar la'asar, ya faɗi ɓangaren rana da dare, shi ne tsakanin asubahi da hudowar rana, da kuma tsakanin la'asar zuwa  magriba, Allah madaukakin sarki yace

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْرًا كَثِيرًا 

Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ambaci Allah, ambata mai yawa. (Suratul Ahzab Aya ta 41)

وَسَبِّحُوهُ بُكْرَةً وَأَصِيلًا 

Kuma ku tsarkake shi, a sãfiya da maraice. (Suratul Ahzab Aya ta 42)

Malam jauhary yace: Abunda ake cewa "ASEEL" shi ne lokacin nan na bayan sallar la'sar izuwa sallar magriba. Allah madaukakin sarki yace

وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ بِٱلْعَشِىِّ وَٱلْإِبْكَٰرِ

Kayi tasbihi tare da godewa ubangijinka da yamma da kuma dare. (Suratul Gafir Aya ta 55).

Farko rana shi ne Al'ibkãr (ٱلْإِبْكَٰرِ)

Al'ashiyyi (ٱلْعَشِىِّ) shi ne karshen rana yini kenan.

Haka Allah madaukakin sarki yasake cewa

وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ قَبْلَ طُلُوعِ الشَّمْسِ وَقَبْلَ غُرُوبِهَا وَمِنْ آنَاءِ اللَّيْلِ فَسَبِّحْ وَأَطْرَافَ النَّهَارِ لَعَلَّكَ تَرْضَىٰ 

kuma ka yi tasbĩhi da gõd wa Ubangijinka a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacwarta, kuma daga sã'õ'in dare sai ka yi tasbĩhi da sãsannin yini, tsammãninka zã ka sãmi yarda. (Suratul Dáhá Aya ta 130)

Ma'anar wannan aya malamai sukace: wanda yace kaza da kaza kamar yanda ahadisai suka zo lokacin da yawayi gari, ko lokacin da ya wuni abunda ake nufi shi ne kafin fitowar rana da kuma kafin faduwarta.

Lokacin yin azkar ɗin shi ne bayan sallar asuba da kuma bayan sallar la'asar zancen ibnu qayyeem yakare.

Hadisai sahihai sunzo waɗanda suke karfafa maganarsa, kamar hadisin da amru ɗan shu'aibu ya karɓo daka babansa, babansa kuma ya karɓo daka kakansa.yace: manzan Allah sallahu Alaihi wasallam yace: (Duk wanda yace ALLAHU AKBAR sau 100 kafin hudowar rana, da kuma sau 100 kafin faduwarta, babu wani awannan yini dazaizo da wani aiki wanda yafi nasa, kuma zai kasance mafificin mutane ranar alkiyama saifa wanda yazo da irirn abunda ya faɗa ko yazo da fiye danasa.)

Sheik Albany ya ingnata wannan hadisi acikin sahihul targibu wattarheebu.

Sai kuma hadisi yazo da nuni akan anayin waɗannan zikirai bayan magariba kamar yadda shaddãd ɗan Ausu yabruwaito hadisin sayyedul istigfari da falalarta, inda yace wanda yafadeta acikin wani yanki na dare dazai mutu awanna daren kan fitowar alfijir to zaishiga aljannah.

Antambayi majalisar malamai ta addinin musulunci da kuma fatawa ta kasar saudiyya akan wannan mas'ala sai suka amsa da, cewa zikrin safe yana farawa ne daka hudowar alfijir har zuwa lokacin da rana zatayi zawali, zikirin yamma kuma yana farawane daka lokacin da rana ta yi zawali zuwa faduwarta da kuma farkon dare. saboda fadin Allah madaukakin sarki

وَاذْكُر رَّبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعًا وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالْآصَالِ وَلَا تَكُن مِّنَ الْغَافِلِينَ 

Ka ambaci ubangijinka azuciyarka kana mai kaskantar da kanka ga Allah da kuma tsoran azabarsa karka daga murya da zikirin, safe da kuma yamma. kuma kada ka kasance daga gafalallu. (Suratul A'araaf Aya ta 205)

Sukace: "AL'ASEEL" shi ne tsakanin la'asar da kuma magriba.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments