Ticker

6/recent/ticker-posts

Sahur Kafin Da Bayan Kiran Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salamu Alaikum, A kan hadisin da ka kawo a cikin Goron Azumin Ramadan cewa: Mai Azumi na iya cigaba da cin abinci bayan ya ji kiran sallah, ina son ƙarin bayani. Domin na ji wani malami yana cewa bai halatta a yau mutum ya kai sahur ɗinsa har zuwa ketowar alfijir ba. Yana ganin yin hakan a yau wai son-zuciya ne, kuma wai ganganci ne?!

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Malamai sun saɓa da juna a kan mas’alar alfijir wanda yake haramta cin sahur ga mai azumi kuma yake wajabta yin sallar Asubah. Kuma abin da muka gamsu da shi, shi ne: Maganar malaman da suke ganin halaccin ci da sha har zuwa lokacin da alfijir na-gaskiya ya fito kuma ya bayyana. Menene hujjojinsu?

Da farko dai Allaah Maɗaukakin Sarki ya ce

وَكُلُوا۟ وَٱشۡرَبُوا۟ حَتَّىٰ یَتَبَیَّنَ لَكُمُ ٱلۡخَیۡطُ ٱلۡأَبۡیَضُ مِنَ ٱلۡخَیۡطِ ٱلۡأَسۡوَدِ مِنَ ٱلۡفَجۡرِۖ

 ‘Kuma ku ci, ku sha har sai farin zare ya bayyana muku daga baƙin zare na alfijir.’  (Surah Al-Baqarah: 178)

Sannan kuma Al-Imaam Al-Bukhaariy ya riwaito (1916) hadisi da isnadinsa zuwa ga Sahabi Adiy Bn Haatim (Radiyal Laahu Anhu) cewa, a lokacin da ya ji wannan ayar sai ya ɗauki igiyoyi guda biyu fara da baƙa ya ajiye su a ƙarƙashin matashin kansa, sannan ya cigaba da dubansu a cikin duhu amma ba su bayyana masa ba. Don haka, sai ya yi sammako zuwa ga Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ambata masa, sai kuwa ya amsa masa da cewa

إِنَّمَا ذَلِكَ سَوَادُ اللَّيْلِ وَبَيَاضُ النَّهَارِ

Ai wannan baƙin duhun dare da farin hasken yini ne kawai.

Sai kuma ya sake riwaitowa (1919) daga A’ishah Ummul-Mu’mineen (Radiyal Laahu Anhaa) daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

كُلُوا وَاشْرَبُوا حَتَّى يُؤَذِّنَ ابْنُ أُمِّ مَكْتُومٍ ، فَإِنَّهُ لاَ يُؤَذِّنُ حَتَّى يَطْلُعَ الْفَجْرُ

Ku ci kuma ku sha har sai Ibn Ummi-Maktuum ya kira, domin shi ba ya kira har sai alfijir ya keto.

Waɗannan nassoshi sun nuna a fili cewa: Mai azumin da ke cikin yin sahur na da daman cigaba da ci da sha, har sai lokacin da alfijir ya bayyana. Musamman idan aka yi nazari a cikin riwaya ta ƙarshe, wadda ta nuna Ibn Ummi Maktuum makaho ne, ba ya iya ganin bayyanan alfijirin da idonsa. Don haka, ba ya kiran sallah har sai an ce masa: Asubah ta yi! Asubah ta yi!! Kamar yadda ya zo a cikin wani lafazi na hadisin. Kuma duk da haka Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya umurci musulmi su cigaba da ci da sha har zuwa lokacin da zai kira, wanda kuma yake aukuwa a bayan bayyanan alfijir.

Daga wannan ta yaya za a iya gano mustahabbanci ma balle kuma wajibcin dakatar da ci ko sha kafin bayyanan alfijir ɗin da minti biyar ko goma ba, kamar yadda wasu malamai suke faɗi a yau?

Shiyasa Ibn Hajr (Al-Fat-hu: 5/621) ya ce: Wannan ayar da hadisin sun nuna cewa: Bakin iyakan lokacin ci da sha ga mai azumi shi ne ketowar alfijir.

Watau: Amma ba kafin ketowansa da mintuna ba!

Amma hadisin da tambayar ta zo a kansa, shi ne hadisin da Al-Imaam Abu-Daawud da Ibn Jareer At-Tabariy da Al-Haakim da Al-Baihaqiy da Ahmad suka riwaito shi da isnadansu har zuwa ga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), kuma lafazinsa kamar yadda Abu-Daawud (2035) ya kawo ta riwayar Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) shi ne

إِذَا سَمِعَ أَحَدُكُمُ النّدَاءَ وَالْإِنَاءُ عَلَى يَدِهِ ، فَلَا يَضَعَهُ حَتَّى يَقْضِيَ حَاجَتَهُ مِنْهُ

Idan ɗayanku ya ji kiran sallah alhali kwanon abincinsa na hannunsa, to kar ya ajiye shi har sai ya gama buƙatarsa daga cikinsa.

Al-Imaam Al-Haakim da Az-Zahabiy da Abdul-Haqq Al-Ishbeeliy duk sun inganta shi, kamar yadda ya ambata a cikin Sahih Sunan Abi-Daawud: 7/115 .

Al-Imaam Al-Albaaniy shi ma ya tabbatar da ingancin wannan hadisin saboda waɗansu shawaaheed masu yawa da ya ke da su, kamar yadda ya kawo a cikin Silsilah Saheehah: 1394. Daga ciki akwai: Riwayar Ammaar Bn Abi-Ammaar mai lafazi daidai da wannan, sannan ya ƙara da cewa

وَكَانَ الْمُؤَذِّنُ يُؤَذِّنُ إِذَا بَزَغَ الْفَجْرُ

Kuma Ladan ya kasance yana kira ne idan alfijir ya keto.

 (Sanadinsa sahihi ne a kan sharaɗin Muslim).

Sai kuma riwayar Abu-Umaamah, ya ce: An tayar da iqamah alhali ƙwaryar (nono) tana hannun Umar, sai ya ce

أَشْرَبُهَا ، يَا رَسُولَ اللهِ ؟ قَالَ : نَعَمْ ، فَشَرِبَهَا

Ya Manzon Allaah! In shanye shi? Ya ce: E! Sai kuwa ya shanye shi.

 (Sanadinsa hasan ne).

Ga kuma riwayar Abu-Az-Zubair wanda ya ce: Na tambayi Jaabir game da mutumin da yake son yin azumi, ga kuma ƙwaryar abin sha a hannunsa yana nufin zai sha, sai kuma ya ji kiran sallah? Sai Jaabir (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce

كُنَّا نَتَحَدَّثُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَ سَلَّمَ قَالَ : لِيَشْرَبْ

Mun kasance muna tattaunawa cewa Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: Ya sha kawai.

 (Babu matsala a sanadinsa a wurin kafa shaida).

A fili yake cewa waɗannan riwayoyin suna bayani ne a kan cewa: Mai azumi yana iya ci ko sha a lokacin da alfijir ya keto alhalin yana cikin yin sahur bai gama ba! To, ta yaya za a iya cewa wanda ya yi aiki da waɗannan nassoshin a yau ya bi son-zuciya? Ko ya auka cikin ganganci da kasada?!

Sannan kuma Abu-Daawud (1/369-370) da At-Tirmiziy (705) da Ibn Khuzaimah (1930) da Ad-Daaraqutniy (shafi: 231) sun riwaito ta hanyar Abdullaah Bn An-Nu’umaan As-Suhaimiy, ya ce:

Qaisu Bn Talqi ya zo wurina a cikin Ramadaan a ƙarshen dare bayan har na gama cin sahur saboda tsoron wayewan gari. Sai ya nemi in ba shi ɗan mai ko miya, sai na ce ma sa: Baffa! In da akwai sauran dare yanzu ai da kuwa na shigar da kai na ba ka abinci da abin sha da nake da shi. Ya ce: Kana da shi a wurinka? Sai ya shiga, ni kuma na kawo masa abinci da nama da kunun-zaƙi, ya zauna ya ci kuma ya sha, kuma ya tilasta ni har sai da na ci tare da shi, alhalin ina ɗar-ɗar saboda tsoron wayewan gari. Sannan sai ya ce:

(Babana) Talqu Bn Aliy ya gaya mini hadisi cewa: Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

كُلُوا وَاشْرَبُوا وَلَا يَهِيدَنَّكُمُ السَّاطِعُ الْمُصَعَّدُ ، فَكُلُوا وَ اشْرَبُوا حَتَّى يَعْتَرِضَ لَكُمُ الْأَحْمَر

Ku ci kuma ku sha, kar (alfijir) mai ɗagawa sama ya zaburar da ku. Amma dai ku ci kuma ku sha, har sai mai ja-jan ya gitto mu ku.

Al-Imaam At-Tirmiziy a ƙarshen riwayarsa ga wannan hadisin ya ce

وَالْعَمَلُ عَلَى هَذَا عِنْدَ أَهْلِ الْعِلْمِ ، أَنَّهُ لاَ يَحْرُمُ عَلَى الصَّائِمِ الأَكْلُ وَالشُّرْبُ ، حَتَّى يَكُونَ الْفَجْرُ الأَحْمَرُ الْمُعْتَرِضُ . وَبِهِ يَقُولُ عَامَّةُ أَهْلِ الْعِلْم

Da wannan ake aiki a wurin malamai cewa: Ci da sha ba su haramta a kan mai azumi har sai alfijir mai ja-ja ya gitta. Kuma wannan shi ne maganar ɗaukacin malamai.

Waɗanne malamai yake nufi?

Al-Imaam Al-Haafiz Al-Mubaarakafuuriy a cikin Tuhfah Al-Ahwaziy: 3/119-120 ya bayyana cewa:

Malamai daga cikin Sahabban Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da Tabi’ai da ma waɗanda ba su ba. Kuma zuwa ga wannan ɗin ne hadisai marfu’ai sahihai suka yi nuni.’

Daga nan sai kuma ya cigaba da kawo sunayen malaman da irin kalmominsu a kan wannan mas’alar, har zuwa inda ya kawo maganar Muslim Al-Bateen, ɗalibin Ataa’u Bn Abi-Rabaah da Mujaahid kuma malamin su Sulaiman Al-A’mash, wanda kuma Ahmad da Ibn Ma’een da Abu-Haatim da An-Nasaa’iy suka ce amintacce ne. (Tahzeeb Al-Kamaal). Shi ne Ibn Abi-Shaibah ya riwaito maganarsa cewa

 لَمْ يَكُونُوا يَعُدُّونَ الْفَجْرَ فَجْرَكُمْ ، إِنَّمَا كَانُوا يَعُدُّونَ الْفَجْرَ الَّذِي يَمْلَأُ الْبُيُوتَ وَالطُّرُقَ

Su (Magabata) fa ba suna ɗaukar alfijir irin alfijirinku ba ne, amma dai suna ɗaukan alfijir kawai shi ne wanda (haskensa) ya cika gidaje da hanyoyi.

Sai kuma ya kawo magana a kan Ma’amar Bn Raashid malamin su Sufyaan At-Thauriy da Ibn Uyainah da Ibn Al-Mubaarak cewa:

 أَنَّهُ كَانَ يُؤَخِّرُ السُّحُورَ جِدًّا ، حَتَّى يَقُولُ الْجَاهِلُ لَا صَوْمَ لَهُ

Shi ya kasance yana jinkirta sahur sosai, har wani jahili ya riƙa cewa: Ba shi da azumi!

Sai kuma maganar Ibn Al-Munzir mai cewa

ذَهَبَ بَعْضُهُمْ إِلَى أَنَّ الْمُرَادَ بِتَبْيِينِ بَيَاضِ النَّهَارِ مِنْ سَوَادِ اللَّيْلِ ، أَنْ يَنْتَشِرَ الْبَيَاضُ مِنَ الطُّرُقِ وَالسِّكَكِ وَالْبُيُوتِ

Wasu malaman sun zaɓi cewa, abin nufi shi ne: Bayyanan hasken yini daga cikin duhun dare, watau hasken ya yaɗu a manyan hanyoyi da ƙanana da kuma cikin gidaje.

 Daga nan kuma sai ya kawo riwaya sahihiya daga Sahabi Saalim Bn Ubaid Al-Ashja’iy (Radiyal Laahu Anhu) cewa

أَنَّ أَبَا بَكْرٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ لَهُ : اخْرُجْ فَانْظُرْ هَلْ طَلَعَ الْفَجْرُ؟ قَالَ : فَنَظَرْتُ ثُمَّ أَتَيْتُهُ فَقُلْتُ : قَدِ ابْيَضَّ وَسَطَعَ ، ثُمَّ قَالَ : اخْرُجْ فَانْظُرْ ، هَلْ طَلَعَ ؟ فَنَظَرْتُ ، فَقُلْتُ : قَدِ اعْتَرَضَ ، فَقَالَ : الْآنَ ابْلِغْنِي شَرَابِي

Abubakar (Radiyal Laahu Anhu) ne ya ce masa: Fita ka duba, ko alfijir ya keto? Ya ce: Sai na dubo sannan na komo na ce masa: Haƙiƙa! Ya yi haske, ya ɗago. Daga baya sai kuma ya ce: Fita ka dubo, ko ya hudo? Sai na duba, sai na ce: Haƙiƙa ya gitta. Shi ne sai ya ce: To, yanzu kawo min abin sha na.  

Ba na jin akwai musulmin da ke cikin hankali da cikar tunanin ƙwaƙwalwarsa da zai iya ƙarfin halin faɗin cewa: Waɗannan manyan Magabatan sun bi son-zuciya ne a wurin waɗannan ayyukan da suka yi! Kamar yadda babu musulmin da zai iya cewa: Akwai wata hanyar bi da ta fi ta su inganci ko kyau a bayansu har zuwa yau, ko kuma ya yi zaton cewa: Koyi da su a yau kuma kasada ne ko kuma hatsari ne!

Shi kuma Al-Allaamah Al-Mujaddid Al-Albaaniy (Rahimahul Laah) bayan ya gama tattaunawa a kan wannan hadisin na Talqu Bn Aliyy (Radiyal Laahu Anhu) a cikin Silsilah Saheehah: 5/50 sai ya ce:

Kuma ka sani cewa: Babu cin-karo-da-juna a tsakanin siffatawar da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi wa hasken alfijir da cewa: (ja-ja) da kuma siffata shi da Allaah Ta’aala ya yi masa da cewa: (Farin Zare). Domin abin nufi dai, kuma Allaah shi ne Masani, shi ne: Farin haske ne wanda ya gauraya da ja-ja, ko kuma a ce: Wani lokaci yana zama fari ne, wani lokacin kuma ja-ja. Yana saɓawa da gwargwadon yanayin shekara da kuma mafitan rana. Kuma na sha ganin hakan ni da kaina, daga gidana da ke Jabalu Hamalaan (a kudu maso gabashin garin Ammaan - Jordan).

Wannan shi ya ba ni damar tabbatar da gaskiyar abin da wasu masu kishin gyara ibadojin musulmi suke faɗi cewa: A wasu ƙasashen Larabawa ana fara kiran sallar Asubah ne tun kafin bayyanar alfijir na-gaskiya da tsawon lokacin da ke sauyawa tsakanin mintuna ashirin zuwa talatin: Watau tun kafin bayyanan alfijir na-ƙarya ma kenan!’

 (Dubi ƙarin bayani a cikin: Siffar Alfijirin da ke wajabta kamewa).

Amma hadisin da Al-Bukhaariy ya riwaito daga Sahabi Anas Bn Maalik (Radiyal Laahu Anhu) cewa

عَنْ زَيْدِ بْنِ ثَابِتٍ - رَضِىَ اللهُ عَنْهُ - قَالَ تَسَحَّرْنَا مَعَ النَّبِىِّ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - ثُمَّ قَامَ إِلَى الصَّلاَةِ . قُلْتُ : كَمْ كَانَ بَيْنَ الأَذَانِ وَالسَّحُورِ؟ قَالَ : قَدْرُ خَمْسِينَ آيَة

Daga Zaid Bn Thaabit (Radiyal Laahu Anhu) ya ce: Mun yi sahur tare da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), sai kuma ya miƙe zuwa sallah. Sai na ce: Nawa ne a tsakanin kiran sallar da sahur ɗin? Ya ce: Gwargwadon ayoyi hamsin.

A wata riwaya kuma

فَلَمَّا فَرَغَا مِنْ سَحُورِهِمَا قَامَ نَبِىُّ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - إِلَى الصَّلاَةِ فَصَلَّى . قُلْنَا لأَنَسٍ : كَمْ كَانَ بَيْنَ فَرَاغِهِمَا مِنْ سَحُورِهِمَا وَدُخُولِهِمَا فِى الصَّلاَةِ؟ قَالَ : قَدْرُ مَا يَقْرَأُ الرَّجُلُ خَمْسِينَ آيَة

Lokacin da suka gama cin sahur ɗin sai Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya miƙe zuwa sallah. Sai muka ce wa Anas: Na wa ne a tsakanin gama sahur ɗinsu da shigansu a cikin sallah? Ya ce: Gwargwadon yadda mutum zai karanta ayoyi hamsin.

Wannan hadisin bai isa dalilin soke abin da ya gabata ba. Domin idan aka ce haka, to yaya kuma za a yi da wasu riwayoyin da suka yi hannun-riga sosai da wannan ɗin, kamar riwayar da Zirr ya yi daga Huzaifah (Radiyal Laahu Anhu) cewa

تَسَحَّرْنَا مَعَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ، هُوَ وَاللَّهِ النَّهَارُ غَيْرَ أَنَّ الشَّمْسَ لَمْ تَطْلُعْ

Mun yi sahur tare da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), kuma wallahi! Gari ya waye, sai dai kawai ranar ce ba ta fito ba!

Al-Haafiz a cikin Al-Fat-hu ya tabbatar da cewa Ibn Abi-Shaibah da Abdur-Razzaaq sun riwaito wannan daga Huzaifah ta hanyoyi sahihai.

(i) Kodayake, kamar yadda Al-Haafiz Ibn Hajr (Rahimahul Laah) ya faɗa a cikin Fat-hul Baariy: 5/626 a ƙarshen sharhinsa, ba za a ce akwai saɓani a tsakanin waɗannan riwayoyin ba, sai dai kawai bambancin hali ne. Ma'ana: A watarana ce ya yi suhur da Zaid Bn Thaabit ya dakata kafin kiran sallah ko fara sallah, a wata ranar kuma ya jinkirta sosai har sai da gari ya waye tangaran, kamar yadda ya yi da Huzaifah (Radiyal Laahu Anhumaa).

Watau ba abu ne da ya dawwama a kansa ba. Shiyasa shi kansa Ibn Hajr ɗin ya cike maganar da cewa

فَلَيْسَ فِي رِوَايَةِ وَاحِدٍ مِنْهُمَا مَا يُشْعِرُ بِالْمُوَاظَبَة

Daga cikinsu babu wanda riwayarsa ta nuna dogewa.

Watau: Wannan hadisin yana nufin wani abu ne da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya aikata shi na wani ɗan lokaci, daga baya kuma ya bar shi, har kuma aka samu masu yawa daga cikin Sahabbansa, kamar yadda At-Tirmiziy ya ambato, suka riwaito saɓaninsa daga gare shi, kuma suka kafe a kan yin aiki da shi a bayan rasuwarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam).

(ii) Sannan kuma a cikin Sahih Al-Bukhaariy, kafin ya kawo wannan hadisin na Zaid Bn Thaabit (Radiyal Laahu Anhu) sai da ya fara zuwa da hadisin Sahal Bn Sa’ad (Radiyal Laahu Anhu) lamba: 1920 wanda ya ce

كُنْتُ أَتَسَحَّرُ فِى أَهْلِى ، ثُمَّ تَكُونُ سُرْعَتِى أَنْ أُدْرِكَ السُّجُودَ مَعَ رَسُولِ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ

Ina yin sahur a gidanmu, sannan sai gaggawa ta zama in samu sallar Asubah ne tare da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam).

Fassarar wannan, kamar yadda Al-Haafiz ya kawo a cikin Fat-hul Baariy: 5/624 daga Ibn Al-Muneer shi ne

الْمُرَادُ : إِنَّهُمْ كَانُوا يُزَاحِمُونَ بِالسُّحُورِ الْفَجْرَ ، فَيَخْتَصِرُونَ فِيهِ ، وَيَسْتَعْجِلُونَ خَوْفَ الْفَوَاتِ

Abin nufi dai shi ne: Sun kasance suna haɗa suhur ɗin da alfijir ne, sai su ɗan tsakura daga cikinsa, kuma su yi gaggawa a cikinsa don tsoron kufcewarsa.

Wannan ma dalili ne a fili cewa: Ba su kasance suna barin cin abinci minti biyar ko goma kafin fitowar alfijir ba.

(iii) Sannan kuma: Buɗe wannan ƙofar na dakatar da ci ko sha kafin alfijir ya fito, wata hanya ce ta ƙara shigar da wasu mintoci a cikin tsawon lokacin azumin musulmi ba da umurnin Allaah ba. Sannan kuma hanya ce mai kai wa ga a yin kiran sallar Asubah tun kafin shigar lokaci don wai a tsare wa musulmi azummansu daga lalacewa, kamar yadda ake ji da ganin masu yin hakan suke riyawa da aikatawa. Wannan kuwa shi ke kai wa ga yin sallar Raka’atal Fajri wani lokaci ma har sallar Asubahin kanta, kafin lokaci!

Kuma malamai sun yarda cewa: Duk lokacin da aka yi kabbarar haramar wata sallah kafin shigar lokacinta, to wannan sallar ba ta yi ba.

Allaah ya kiyaye.

A nan kafin in dakata bari in sake tuna mana abin da na ambata a ƙarshen amsar Fatawa mai lamba A079 a baya cewa

Sai dai mu a Markazu Ahlil-Hadeeth a cikin rubuce-rubucenmu kamar na: Goron Azumin Ramadan da makamantansa muna ƙoƙarin tafiya a kan doron hadisai sahihai ne, kamar yadda manyan malamai masana hadisin suka bayyana. Kuma muna fatar hakan ya zama kyakkyawar mafita gare mu da sauran al’umma a duniya da lahira, in shaa’al Laah. Domin malamai muhaqqiqai sun tabbatar da cewa: Hanyar malaman hadisi ita ce hanya sahihiya ingantacciya wacce a cikinta babu irin matsalolin da sauran hanyoyin suke fama da su. (Dubi littafina: Darajar Malaman Hadisi).

Amma ba mu cewa sauran malamai waɗanda suka saɓa a cikin mas’alolin fiqhu daga wannan matafiyar da ijtihadinsu , ko don bin malamansu mujtahidai , ɓatattu ne ko hallakakku ba ne! Musulmi ne Ahlus-Sunnah ’yan uwanmu matuƙar dai sun nufaci dacewa da gaskiya ne, ba sun bi sha’awar-rai ko son-zuciya ba ne.

Allaah ya haɗa mu gaba-ɗaya a Ranar Lahira tare da waɗanda Allaah ya yi musu Rahama: Daga cikin Annabawa da Siddiƙai da Shuhada’u da Salihai.’

WALLAHU A'ALAM

Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments