Ticker

6/recent/ticker-posts

Karar Waya A Masallaci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam Mene ne hukuncin mutanen da suke barin wayoyinsu a buɗe a cikin masallaci, kusan kullum sai waya ta yi ƙara ana cikin sallah.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Ya kamata kowannenmu ya san cewa

1. Masallaci ɗakin Allaah ne. Masallaci shi ne wurin da Allaah ya fi so duk a cikin duniya. Masallaci wuri ne da Allaah ya keɓe domin bayinsa su ziyarce shi sau biyar a kowace rana. An gina masallaci ne kaɗai don ayyukan bauta, kamar Sallah da Tilawa da Zikiri da sauransu.

2. Wajibi ne a kawar da duk abin da zai iya ɗauke hankalin bayin Allaah a cikin masallaci. Mai ɗauke hankalin nan ko, jin sa ake yi ko gani  ko shaƙe ko makamantan haka, duk ɗaya ne.

3. Sallah ita ce mafificiyar ibadar da Allaah Maɗaukakin Sarki ya halicce mu domin ta. Sallah ita ce aikin da za a fara yi wa bawan Allaah hisabi a kanta a ranar Ƙiyama.

4. Wajibi ne mu riƙa natsuwa a cikin sallah, mu nisanci duk abin da zai ɗauke hankali a cikin sallah.

5. Wayar GSM ce ta fi ɗauke hankalin bayin Allaah a cikin masallacin Allaah a  yau! Ta hanyar GSM ake cutar da bayin Allaah a cikin ibadarsu ga Allaah a cikin masallacin Allaah. Don yawancin sautukan da mutane suke sanyawa a cikin wayar GSM muryoyin sheɗan ne. Muryar sheɗan ita ce: Busa da goge da kiɗa da tafi da ƙwarya da shantu da  sauransu. Haka ma sautukan waƙe-waƙen addini, waɗanda ake amfani da komfuta kafin a fitar da su. Alƙur’ani da Sunnah da Haɗuwar Malamai duk sun nuna haram ne  sauraron muryar sheɗan. Har Alƙur’ani ba a yarda a buɗe shi ta yadda zai cutar da masu sallah ba, ina kuma ga muryar sheɗan. Shigar da muryar sheɗan cikin masallaci alamar sako-sako da addinin Allaah ne.

6. Dole ne musulmi ya kashe wayarsa kafin ya shiga masallaci, ko da babu muryar sheɗan a cikinta. Idan kuma ya manta, to sai ya yi gaggawar kashewa da zaran ya tuna ko an tuna masa. Kamar idan ya ji wayar wani ta yi ƙara, shi ma sai ya tuna, kuma ya ɗauki matakin rufe tasa. Kuma ko da ana cikin sallar ne ya tuna, ko kuma ya ji ta yi ƙara, to sai ya yi gaggawar kashe ta. Kashewa murus ya wajaba ya yi, ba wai ya sanya ta a ‘silence’ ko a ‘vibration’ kawai ba. Ba daidai ba ne ya kashe na ɗan lokaci ba kawai, ta yadda idan ta sake ƙara ya sake kashewar. Fitarwa da kashewar ba za ta jawo wa mai sallah wani abu ta fuskar sujadar rafkanuwa ba! Wannan matakin shi ya fi da a ƙyale wayar ta cigaba da yin ƙara, tana ta cutar da masallata.

7. Daidai ne a tuna wa masallata tun kafin a fara sallah, cewa su kashe wayoyinsu, kuma lallai su bi wannan umurnin. Waɗansu sukan ce, sun manta da kashe wayoyin ne tun kafin su shiga  masallacin Allaah! Amma ba su yin irin wannan mantuwar wurin shiga ofisoshin tsaro da sauransu! Don me?! Ko sun fi ganin girman waɗannan wuraren ne fiye da Masallatan Allaah Maɗaukakin Sarki? Mutum ba ya shiga wurin duk mai matsayi a idonsa a duniya da wani abin da ba ya so. Amma yau ga mutane suna shiga masallaci da abubuwan da suka tabbatar Allaah ba ya so! Sannan kuma wai sun je neman ya biya musu buƙatunsu na duniya da barzahu da lahira ne!

8. Waɗansu kuma ba su kashe wayoyin ne, wai gudun kar a neme su, ba a same su ba! Wai shin ko daga Lahira ce za a kira su don a gaya musu cewa takardar Aljannarsu ta fito?!! Watau ba za su iya bayar da mintoci goma zuwa sha-biyar don Sallar da Allaah ya halicce su dominta ba! In kuwa haka ne to, don Allaah ina cikan imani da musulunci da taqawa a irin wannan halin?! Shin wayar da suke yi a lokacin ta fi Aljannar da suka zo nema muhimmanci ne a lokacin?!

9. Wajibi ne mu san cewa duk yadda harkokin duniya su ke ba su isa a wulaƙantar da sallah saboda su ba. Dole duk mai neman mu ta waya ya san cewa: Ba za mu taɓa ɗaukar wayarsa a lokacin sallah ba. Kuma lallai mu san cewa: Alhaki na kan duk wanda ƙarar wayarsa ta ɗauke wa wani hankali a cikin sallah.

Laa Haula Walaa Quwwata Illaa Bil Laah.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments