Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sanya Ayar Alkur'ani A Ringtone

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam, shin mene ne hukuncin mutum ya sanya ayar Alkur'ani a Ringingtone ɗin wayarsa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

Shi alƙur'ani an saukar da shi ne domin a karanta shi, a san ma'anarsa, ayi tun tuni dashi, a nemi kusanci da Allah dashi, a bautawa Allah da shi, kuma shi lallai waraka ne ga dukkanin wata cuta.

Kada ka wulaƙanta shi, kuma kada ka sanya shi a inda bai dace dashi ba, haƙiƙa idan kayi hakan to ka saɓawa Allah maɗaukakin sarki.

Kada ka mayar dashi shi ne Ringtone na wayarka, kada ka dinga kunna Ƙira'ar alƙur'ani a cikin wayar da kasan za'a iya kiranka da ita domin gudun kada kana cikin tsaka da sauraronsa sai kiran waya ya shigo ya katse shi ba tare da ya kai kan aya ba, kuma sannan ka kiyayi maishe shi ringing wayarka, wanda da zarar an kiraka sai aji sautin alƙur'ani ne yake tashi, haƙiƙa wannan babban kuskure ne, domin za'a datse alƙur'ani a inda bai kamata a datse shi ba.

Duk wanda ya sanya wani yanki na alƙur'ani a matsayin shi ne Ringtone ɗin wayarsa, to ya yi laifi, sabida wataran zai iya shiga ban-ɗaki da wayarsa kuma a kira shi (sai aji alƙur'ani a cikin ban-ɗakin alhalin kuma shi alƙur'anin mai tsarki ne, bai da ce a ji shi a ban-ɗaki ba, domin shi gurin ƙazanta ne), ko kuma a kira shi ɗin, kafin ayar takai kan gaɓa an katse ta ba tare da ayar taje ƙarshe ba, kuma shi ma ɗin bazai iya bari ayar taje kan gaɓa ba, sai ya karɓi wannan kiran ba tare da ayar ta bayar da cikakkiyar ma'ana ba an katse ta, sabida haka a guji sanya alƙur'ani a matsayin Ringtone na waya.

WALLAHU A'ALAM

Mallam Nuruddeen Lawan Abubakar.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments