Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Ya Neme Ni A Lokacin Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mijina ne ya neme ni, sai na ce: Bari in je ban-ɗaki in fito. Da na fito sai na ji Kiran Sallah, don haka sai na tsaya na yi sallah. Da na dawo, sai ya yi fushi ya ce, ya fasa. To, ko ina da laifi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Ya tabbata a cikin hadisin da Al-Bukhaariy (3237) da Muslim (3611) suka riwaito daga Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) cewa: Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« إِذَا دَعَا الرَّجُلُ امْرَأَتَهُ إِلَى فِرَاشِهِ فَأَبَتْ ، فَبَاتَ غَضْبَانَ عَلَيْهَا ، لَعَنَتْهَا الْمَلاَئِكَةُ حَتَّى تُصْبِحَ »

Idan miji ya kira matarsa zuwa ga shimfiɗarsa sai kuma ta ƙi, shi kuma sai ya kwana yana  fushi da ita, to mala’iku za su yi ta la’antar ta har sai asubah ta yi.

A wata riwayar kuma a cikin Al-Bukhaariy (5194) da Muslim (3612) ya ce

« إِذَا بَاتَتِ الْمَرْأَةُ مُهَاجِرَةً فِرَاشَ زَوْجِهَا لَعَنَتْهَا الْمَلاَئِكَةُ حَتَّى تَرْجِعَ »

Idan mace ta kwana tana mai ƙaurace wa shimfiɗar mijinta, mala’iku za su yi ta la’antar ta har sai ta komo.

A cikin wata riwayar Muslim (3613) kuma ya ce

« وَالَّذِى نَفْسِى بِيَدِهِ مَا مِنْ رَجُلٍ يَدْعُو امْرَأَتَهُ إِلَى فِرَاشِهَا فَتَأْبَى عَلَيْهِ إِلاَّ كَانَ الَّذِى فِى السَّمَاءِ سَاخِطًا عَلَيْهَا حَتَّى يَرْضَى عَنْهَا »

Na rantse da wanda raina ke a hannunsa! Babu namijin da zai kira matarsa zuwa ga shimfiɗarta, kuma sai ta ƙi yarda gare shi, face wanda ke cikin sama ya kasance mai fushi gare ta, har sai ya yarda da ita.

Waɗannan riwayoyin sun nuna cewa

1. Abin nufi da shimfiɗa shi ne: Saduwa. Yana daga cikin kyakkyawan ladabi a riƙa ɓoye duk abin da ake jin kunya wurin bayyana shi a fili.

2. Riwayar farko ta nuna wannan la’anar tana samuwa in da dare ne ya neme ta, saboda maganarsa: har sai asubah ta yi. Amma riwayar da ta ce: har sai ta komo, da wadda ta ce: har sai ya yarda da ita sun nuna la’antar tana tabbata ko da a kowane lokaci ne hakan ya auku daga gare ta. Allaah ya kiyaye.

3. Wannan la’antar tana aukuwa ga matar ce idan miji ya fusata a kan hakan. Amma idan ya yarda da uzurinta, ko ya kayar da haƙƙinsa, to babu fushi ko la’antar Ubangiji a kan ta.

Don haka, abin da ya wajaba ga kowace mace musulma shi ne ta kiyaye wannan haƙƙin dangane da mijinta. Ta yi ƙoƙarin zama a cikin shirin biya masa buƙata a duk lokacin da ya yi buƙata, sannan kuma ta yardar da shi a lokacin da ta ga ya fusata a kan hakan da kalmomi kyawawa daɗaɗa. Musamman dayake fushin miji a kan haka yakan janyo fushin Ubangiji Ta’aala a kan mace.

Haƙƙin Allaah da ke kanta na yin sallah a kan lokaci bai soke haƙƙin mijinta a kanta ba. Musamman ma dayake lokacin sallar yana da ɗan yalwa ta yadda za ta iya biyan buƙatar miji kuma ta koma ta yi sallar a cikin lokacinta. Ba ga shi nan da yawa mata a gidaje mata suna jin kiran sallar daga masallaci amma kuma sai su cigaba da ayyukansu na shirya abinci da wanke-wanke da sauransu, sai daga baya kuma su je su yi sallar a cikin lokacinta ba?!

Kodayake sanannen abu ne cewa buƙatar saduwa tasowa take yi, kuma ba a sanya mata lokaci, amma dai shi ma miji ya kamata ya riƙa kula da lura da lokutan da suka dace da neman buƙatarsa a wurin matarsa, don kar ya riƙa haɗa mata kashi.

Allaah ya datar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

08164363661

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments