Ticker

6/recent/ticker-posts

Jinin Haila Ya Dauke Mata Kafin Lokacin Daukewar Yayi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malamai Allah ya saka da alkairi. Tambayata itace mace ce take jinin haila to sai ya ɗauke mata kafin lokacin daukewar yayi, zatayi wanka ne ta cigaba da ibada ko zata kara wasu kwanaki a kai?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Walaikum sallam warahmatahi wabarkatahu

Mafi yawan mata idan jinin al'ada ya Ɗauke musu suna jinkirta wanka da niyar ko jinin zai Qara dawowa. Wasu sukan Qara kwana Ɗaya zuwa biyu bayan haila ya Ɗauke. Wasu kuma idan suka ga alama guda Ɗaya na ɗaukewar jinin, sai suce zasu jinkirta wanka domin su jira zuwan sauran alamomin.

Misali: Mace taga bushewar gaba amma bata ga Farin ruwa ba, wanda ake kiransa da larabci ( ﻗﺼﺔ ﺍﻟﺒﻴﻀﺎﺀ ), daga nan sai tace bari ta bari sai farin ruwa yazo sannan tayi wanka ta cigaba da sallah da azumi.

Duka Wannan kuskure ne babba Abinda yake wajibi shine: Da zarar taga jini ya tsaya ko taga alamomin Ɗaukewar Jinin haila, toh wajibi ne tayi wanka nan take ta cigaba da ibadar ta. Qin yin wanka har lokacin sallah ya wuce babban zunubi ne. Allah ya tanadi Azaba mai tsanani ga masu wasa da sallah.

Allah yace a suratul má'un Aya ta 4-5

فَوَيْلٌ لِلْمُصَلِّينَ

To, bone yã tabbata ga masallata.

الَّذِينَ هُمْ عَنْ صَلَاتِهِمْ سَاهُونَ

Waɗanda suke masu shagala daga sallarsu.

Allaah ya qara da cewa:-

فَخَلَفَ مِنْ بَعْدِهِمْ خَلْفٌ أَضَاعُوا الصَّلَاةَ وَاتَّبَعُوا الشَّهَوَاتِ ۖ فَسَوْفَ يَلْقَوْنَ غَيًّا

Sai waɗansu ´yan bãya suka maye a bãyansu suka tõzarta Sallah, kuma suka bi sha'awõwinsu. To, da sannu zã su hau da wani sharri. (Suratul Maryam aya ta 59)

...... Da ayoyi masu yawa cikin Al-Qur'ani.

daga lokacin da jini ya Ɗauke, ibadah ya wajaba ga mace. idan mace ta jinkirta sallah toh sai ta rama su bayan tayi wanka, sannan tayi istigfarin jinkirin Sallah da tayi.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments