𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
shin mace mai jinin biki zata
zauna har kwana arba'in baza tayi sallah ba Kuma baza tayi Azumi ba, ko Kuma
abin lura daga gareta za ta yi tsarki, tayi sallah Kuma nawa ne mafi ƙarancin
kwanakin da za tayi kafin tayi tsarki?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Mace mai jinin biki bata da
kaiyadadden lokaci sai dai duk lokacin da jinnin ya zo mata zata zauna baza
tayi sallah ba Kuma baza tayi Azumi ba Kuma mijinta bazai iya saduwa da ita ba.
Amma idan taga jinin ya dauke, wato ta tsarkake ko da kafin ta cika kwana
arba'in ne ko da jinnin iyakacin kwana goma kawai yayi ko kwana biyar kawai sai
ya ɗauke, to sai
tayi wanka tayi sallah, tayi Azumi Kuma mijin ya sadu da ita babu laifi a cikin
hakan.
Sai dai abin da yafi muhimmanci
shine shi jinin biki al'amari ne kebantacce Kuma hukuncinsa yana ratayuwa ne da
shi, wato idan jinin yazo to hukuncinsa yana nan ba za tayi Azumi da sallah ba
Kuma idan jinin Bai zo ba to hukuncinsa baya nan. duk lokacin da tayi tsarki to
ta wofanta daga hukuncinsa.
Sai dai idan jinin ya karu matar
ta zamo mai jinin Istihada, wato jinin ciwo kenan, sai tayi lissafin iya
kwanakin al'adarta sai tayi wanka tayi sallah. sai ta nemi maganin wannan jinin
cuta.
WALLAHU A'ALAM
Nusaiba Tasiu Abdulrahim
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.