Ticker

6/recent/ticker-posts

Jigo A Finafinan Hausa

Daga
Isa Yusuf Chamo
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Bayero, Kano

1.1 Gabatarwa

Fim abu ne mai gajaren tarihi idan aka kwatanta shi da sauran ɓ angarori na adabin zamani. Misali wa ƙ a da rubutun zube. A wajen Hausawa wasan kwaikwayo shi ne tushen samuwar finafinan bidiyo na Hausa, domin shi aka fara aiwatarwa a dandali kafin a sami na’urar ɗ aukar hoto ta majigi wadda daga baya kuma aka sami gidajen talabijin da na’urar bidiyo da ake amfani da ita a yau. Dangane da fim wanda aka fara aiwatarwa a harshen Hausa kuwa shi ne “Baban Larai”. Abdul ƙ adir (1988: 24).

Finfinan Hausa na bidiyo kuwa, an fara samun su ne daga shekarar 1980 zuwa 1984. Sakamakon irin ho ɓɓ asar da ƙ ungiyoyin marubuta litatttafai da na wasan kwaikwayo na dandamali da na wasan motsa jiki (kareti), suka fara jarraba shiryawa. A shekarar 1990 ƙ ungiyar Tumbin Giwa ta shirya wani fim mai suna Turmin Danya. To sai kuma a shekarar 1994 suka sake shirya fim ɗ in “Gimbiya Fatima”. Kamfanin Gidan Dabino ya shirya In da so da Ƙ auna a 1994. Samuwar wa ɗ annan finafinai da wasunsu shi ne ginshi ƙ in da ya ba wa kamfanoni da ƙ ungiyoyin ƙ asar nan damar yin finafinan Hausa.

A wannan takarda an yi nazari ne, sannan aka fito da nau’o’in saƙonni waɗanda ake ƙulluawa a cikin zubin finafinan Hausa. Domin haka, manufar wannsan takarda ita ce fito da wasu jigogi na finafinan Hausa da kuma bayaninsu tare da kafa hujjoji da misalai daga finafinan Hausa.  

1.2 Ma’anar kalmar Jigo

Kalmar jigo tana da ma’anoni guda biyu wato ma’ana ta lugga da kuma wadda aka ba wani fannin ilimi da ake kira da Larabci ‘isdillahi’.

Jigo a luggance na nufin abin da ake amfani da shi wajen ban ruwa a lambu. Ganin muhimmancin da jigo yake da shi wajen ban ruwa wadda idan babu shi babu ban ruwa, ya sa manazarta suka yi amfani da kalmar a matsayin manufa ko kuma sa ƙ o. (East da Wasu, 1948:47)

Malamai da manazarta da kuma ɗ alibai sun bayyana ma’anar jigo ta lugga ko isdilahi a rubuce-rubucen da suka yi. Alal misali:

Ɗ angambo, (1981:6) cewa ya yi “Jigo shi ne sa ƙ o ko manufa ko abin da wa ƙ a ta ƙ unsa, wato abin da take magana a kai”.

Gusau (1983:142) Ya bayyana Jigo da cewa “shi ne sa ƙ o wato ainahin gundarin sa ƙ on da wa ƙ a take ɗ auke da shi”.

Shi ma Muktar (1984:1) Ya ce “Jigo wani abu ne da aka yi ko kuma ake so a sadar da wannan ƙ uduri ga wani ko wasu, domin wanda aka sadarwa da wannan ƙ uduri ya yi aiki da shi, ko kuma ya zamana yana sane da wannan abu shi ma”.

Buhari (1988:26) Ya bayyana jigo da “Duk wani sa ƙ o ko manufa da marubuci ke so ya isar ko ya gabatar, shi ne jigonsa. Lallai ne wanda duk ya yi irin wannan rubutu ya zamana yana da manufa. Manufar nan ita ce ginshi ƙ in rubutun shi jigo”.

Sai kuma Halima, Ɗ . (2002:25) ta bayyana jigo da cewa “Madogari da madosar da ake son nusarwa ga jama’a wadda hakan yana iya zama gyara da kuma maganganu a cikin al’umma baki ɗ aya don amfanin gaba”.

Idan aka duba za a fahimci cewa wa ɗ annan ma’anoni da malamai da manazarta suka bayar kusan abu ɗ aya suke magana a kai, sai dai bambancin kalmomi da zurfin za ɓ ensu na kowane malami ko manazarci ne suke da ɗ a fito da ma’anar ko da ɗ a armasa ta.

Jigo a fim na Hausa, kai tsaye yana nufin sa ƙ on da aka sar ƙ a a zubin labari na fim. Abu ne wanda aka yi wa mutane ishara da a kansa ake son su koyi wani darasi daga abin da aka nuna abin nisha ɗ i a kansa. Haka kuma jigo ra’ayi ne wadda manazarci zai iya bayyanawa da kare kansa ta hanyar fito da wadatattun hujjoji daga fim ɗ in da yake nazari a kai.

Muhimman hanyoyin fitar da jigo daga finafinan Hausa sun ha ɗ a da:

-            kallon fim

-            wa ƙ a

-            sunan fim

i) Kallon Fim

Kallon fim yana nufin mai nazari ya kalli fim tun daga farkonsa har ya zuwa ƙ arshensa. Ta haka ne za a iya gano sa ƙ on da fim ɗ in yake ɗ auke da shi. Wannan hanya tana ɗ aya daga cikin muhimman hanyoyin da mutum zai iya yanke hukunci a kan wani fim dangane da jigonsa ta hanyar kawo hujjoji daga fim ɗ in da ya kallata.

ii) Wa ƙ a

Wa ƙ a wani zance ne tsararre kuma shiryayye da ake yi da ya bambanta daga magana ko zance na hira da ake yi domin yabon wani ko wata ko kuma isar da wani sa ƙ o. Wa ƙ a ma hanya ce da ake iya fayyace jigo a finafinan Hausa daga zubinta, musamman wasu daga cikin finafinan, manufarsu ba ta fita sai ta hanyar wa ƙ ar da take cikinsu. Misali a cikin fim ɗ in Sutura da wuya mutum ya iya gane takamaiman jigonsa bayan ya gama kallon fim ɗ in, domin ɓ angarori na rayuwa da kowannensu za a iya shirya fim a kai, aka gwama su. Amma sai a wa ƙ ar ƙ arshe ne jigon ya bayyana kansa inda matan da suka fito a cikin shirin suka bayyana matsayinsu wato na 'yar masu ku ɗ i da mai kyau da kuma mace mai ilimi wadda a cikin shirin aka nuna aurenta ya fi na sauran.

Haka kuma, su ma kansu masu shirya fim sukan sa a rubuta musu wa ƙ a wadda a cikinta za ta bayyana jigon fim kawai. (Sani Sidi Sharifai)

iii) Sunan Fim

Sunan fim na nufin la ƙ abin da aka yi wa wani shiri wanda kuma ake kiransa da shi. Wasu finafinan kan bayyana jigoginsu daga sunayensu ma’ana da mutum ya ga sunan zai iya yanke hukunci a kan jigonsa tun akfin ya kallace shi, misali finafinai irin su Nagari da Salihi da Ha ƙ uri da Zato da Lokaci da Sauyi da Mahandama da sauransu. Sai dai akwai finafinai masu yawa da mutum ba zai iya yanke hukunci a kan jigonsu ta hanyar sunayensu ba, misali Khusufi da Khushu’i  da Limaza da Namshaza da Zabari da Gidauniya da Girma da sauransu.

1.3 Nau’o’in Jigo a Finafinan Hausa

A wannan ɓ angare an duba yadda jigo yake fitowa a cikin finafinan Hausa. Akwai abubuwa da yawa wa ɗ anda ake gina jigon fim a kansu wa ɗ anda suka shafi rayuwar al’umma daban-daban tun daga zamantakewarsu da ma’amalolinsu da dai sauran hul ɗ o ɗ in rayuwa. An lura a finafinan Hausa a kan gina jigon fim a kan ɗ aya daga cikin wa ɗ annan abubuwa.

A wannan ɓ angare kuma an zo da rabe-raben jigo a cikin finafinan Hausa tare da kawo misalai daga finafinan da suka dace da kowanne rabo kamar haka:

1.3.1    Jigon Ha ƙ uri

Haƙuri na nufin juriya da kawaici da ƙin nuna damuwa a kan wasu abubuwan rashin jin daɗi da kuma da-na-sani. Haƙuri halin manzon allah ne, kuma ya umarci al’ummarsa da su yi shi. Sakamakon ƙarancinsa a zukatan al’umma ya sa masu shirya finafinan Hausa suke shirya fim a kansa, domin tunatar da mutane sakamakon wadda yake aikata shi da kuma illolin rashinsa, don mutane su gyara halayensu.

Misali fim ɗ in Ha ƙ uri , an shirya shi ne a kan jigon Ha ƙ uri domin tun daga farkon fim ɗ in har ƙ arshensa jigon ya ratsa ko’ina.

Babban jigon wannan fim shi ne Ha ƙ uri sai dai akwai ƙ ananan jigogi da aka yi amfani da su wajen gina babban jigon, wa ɗ anda suka ha ɗ a soyayya kamar yadda ta faru tsakanin Aminu da Asma’u da zumunci kamar yadda Lami take yawan ziyarar Asma’u da kuma cin amana kamar yadda Lami ta juya wa Asma’u baya, lokacin da ta sami haihuwa. Sauran misalan finafinan da suke ɗ auke da jigon ha ƙ uri sun ha ɗ a da Madadi da Ha ƙ uri Magani da Ƙ addara da Nagari da Duniya da kuma Umarni da sauransu.

1.3.2 Jigon Siyasa

Bisa lugga kalmar siyasa wadda take Balarabiya ce, tana nufin sau ƙ i ko rangwame ko kuma jin ƙ ai. A da idan an ce wa mutum “ Ɗ an siyasa” to ana nufin mutum mai jin ƙ ai mai rangwame mai nasiha wato mutum mai yayyafi ga rayuwar al’umma. Funtua, 2002:4)

Ƙ amus ɗ in Turanci na O ɗ ford, ya fassara siyasa da cewa “hanya ce da mutane suke mulkar kansu ta dimokra ɗ iyya.

Mashi (1986:16) ya kalli siyasa bisa isdillahi fuskoki guda uku. Fuska ta farko ya fassara siyasa da cewa kalma ce ta Girkawa (politics) wadda ke nufin salo. Fuska ta biyu da ta uku su ne wa ɗ anda Hausawa suka ba kalmar “siyasa” wadda ke nufin sulhu ko sau ƙ i, domin ganin cewa siyasa ta kasance hanya ta lallashi da lalla ɓ awa da neman goyon baya, ko kuma siyasa ta zama yaudara da ƙ arya saboda yadda 'yan siyasa kan tsara wani labari na yaudara domin neman biyan bu ƙ ata.

Shi kuma Gusau (1995:13) ya bayyana siyasa da cewa “hanya ce wadda ake amfani da hankali da lafazi mai da ɗ i a jawo ra’ayin mutane zuwa ga kyautata rayuwarsu. Ta haka ne siyasa ta ƙ unshi tsarin tafiyar da mutane, da matsalolinsu da ra’ayoyinsu har ta zama hanyar mulki bisa tafarkin dimokra ɗ iyya”.

Kuma ta ita ne ake za ɓ en shugabannin bayan kowanne shekaru hu ɗ u. Sannan duk finafinan da aka shirya masu jigon siyasa suna koyarwa ne ko hannunka-mai-sanda ga 'yan siyasa da su gyara halayensu na babakere da almundahana da dukiyar al’umma, su rungumi adalci da kwatanta gaskiya.

Misali fim ɗ in Mahandama wadda kamfanin Mandawari enterprises ya shirya, yana da jigon siyasa kamar yadda aka nuna a fim ɗ in, mun ga yadda Gwamna da sakataren gwamnati da kwamishinoni da matayensu suke wacaka da dukiyar al’umma, ban da wani kwamishina guda ɗ aya na ayyuka wato Ibrahim Mandawari. Da kuma yadda Ibrahim Mandawari ya tsaya takarar gwamna da za ɓ e ya zagayo ya kuma ci saboda kyawawan halayensa na kamanta gaskiya.

Babban jigon wannan fim shi ne siyasa sai dai akwai ƙ ananan jigogi da aka gano a cikin fim ɗ in wa ɗ anda suka ha ɗ a da soyayya kamar yadda ta faru tsakanin 'yar tsohon gwamna da ɗ an sabon gwamna, da muhimmancin ri ƙ e gaskiya kamar yadda kwamishinan ayyuka ya yi da kuma facaka da dukiyar al’umma kamar yadda 'yan siyasa da matansu suka yi.

Sauran misalan finafinan da ke ɗ auke da irin wannan jigo na siyasa sun ha ɗ a da siyasa da Dare Ɗ aya da kuma Gaskiya Dokin Ƙ arfe .

1.3.3 Jigon Soyayya

Masana da ɗalibai sun yi ta ƙoƙarin bayyana ko bayanin ma’anar so. Sa’id B. (1982:1-6) cewa ya yi “wani ɗarsashi ne zaunanne a cikin zukatan halittu wanda yakan bayyana a sakamakon bege ko ƙauna ko sha’awa. So yakan sa abu ya kwanta a zuciya a ji ana matuƙar muradinsa.

Gusau (1995:15) ya bayyana soyayya da cewa “So da ke aukuwa tsakanin masoya guda biyu inda za su dinga ƙ aunar juna, suna masu begen saduwa da juna”.

Buhari (1988:47) ya bayyana soyayya da “wani hali ne na ƙ auna da mutane biyu kan shiga tsakanin junansu, musamman mace da namiji. Wato ya zamana wani mutum ko yaro na son wata mace ko wata yarinya. A kuma yi dace wanda yake so ɗ in ana sonsa. Wato kana so, ana sonka shi ne soyayya”.

Sa’id (1982:8) ya karkasa soyayya zuwa kaso shida kamar haka:

i)       Son da ke tsakanin mutum da Ubangijinsa Mahalicci.

ii)    Son da ake yi wa annabawa musamman annabi Muhammadu mai tsira da aminci.

iii) Ƙ aunar da ke tsakanin uwa ko uba da 'ya’yansu ko kuma akasi.

i ɓ ) Son da mace ke yi wa namiji ko wanda namiji ke yi wa mace.

ɓ ) Ƙ aunar da ke tsakanin abokai maza ko ƙ awaye mata.

vi)  So irin na ɗ abi’a wanda mutum yake yi wa wani abu kamar doki ko wata dabba ko makami ko wani wasa na motsa jiki ko dai wani mutum haka don kawai ra’ayinsa.

Bayan haka Sa’id (1982:9) ya ƙ ara bayyana wasu sigogi na soyayya da suka ha ɗ a da:

-         Soyayya mafificiya – wato wadda ake musayarta tsakanin masoya biyu (kana so ina so)

-         Soyayya mafi tsarki wato wadda babu batsa a cikinta. Soyayya ce tsantsa ba tare da tunani ko bu ƙ atar saduwa ta jiki ba.

-         Soyayya gurguwa – Wato wadda ɓ angare ɗ aya yana matu ƙ ar so, amma ya kasa bayyana son a wajen namiji ko wajen mace.

-         Soyayya mafi muni – Wato wadda ɓ angare ɗ aya kawai ke so ɗ ayan ba ya so (wato yana so, ba ta so, ko tana so, shi ba ya so).

Dangane da irin soyayyar da ake nunawa a finafinan Hausa ta shafi kaso na biyu wato soyayya tsakanin mace da namiji da soyayya mafi muni wadda ɓangare ɗaya kawai ke so ɗayan ba ya so, da kuma soyayyar yaudara da ake yi saboda kuɗin iyayen mace ko namiji.

Misali a cikin fim ɗ in Kallabi da kamfanin H.R.B Production suka shirya an fito da jigon a fili domin tun daga farko har ƙ arshe soyayya kawai aka nuna a matsayin babban jigo kamar yadda Ahmad S. Nuhu ya ri ƙ a nace wa Maryam, ita kuma ta yi ta ja masa aji, kafin daga baya ta ba da kai bori ya hau. Sannan ƙ ananan jigogin da ke cikin wannan fim sun ha ɗ a da taimako kamar yadda ƙ awar Maryam ta taimaki Murtala da kuma yaudara kamar yadda 'yanmata da samarin cikin wasan suke yi wa kawunansu.

Sauran finafinan da suke ɗ auke da jigon soyayya sun ha ɗ a da Dawayya da Kushu’i da Ɗ ansoyayya da Haya ƙ i da Wasila da Mujadala da Tsumagiya da haya ƙ i da Girma da Masoyiyata da Soyayya Ƙ aunar Zuci da In da so da Ƙ auna da Rana da Ƙ ugiya da Ciwon Ido da Isan da U ƙ uba da Ina son sa haka da Zabari da Katanga da Dafi da Limza da Shara ɗ i da Ƙ amshi da Turare da sauransu.

1.3.4 Fa ɗ akarwa

Wannan na nufin fa ɗ akar da mutane a kan wani abu marar kyau da suke aikatawa da su daina ko su gyara ko a ƙ arfafa ri ƙ o da wani aiki mai kyau. Akan shirya fim a nuna wani mutum yana aikata wani hali da bai dace ba kuma a ƙ arshe ya wula ƙ anta, har yakan nuna ya yi nadama. Irin wa ɗ annan finafinan suna taimakawa wajen canza halayen mutanen da suke aikata ba daidai ba, wala Allah  a bisa dalilin jahilci ko rashin mafa ɗ i.

Bargery, (1934:288) ya bayyana ma’anar fa ɗ akarwa da “zaburar da fa ɗ akar da a sa mutum ya fahimta, a sanya mutum ya gano wani abu na ha ƙ i ƙ a wanda aka rigaya aka mance”. Ya ci gaba da cewa fa ɗ akarwa takan ta da tsimin mutum”.

'Yar’aduwa (2001:126) cewa ya yi fa ɗ akarwa na nufin “nusar da mutum a kan abubuwna da ya sani tun tuni, amma saboda sakaci ya ƙ yale su, ya manta da su. Don haka ne ake yi masa tuni, da yi masa hannunka-mai-sanda, don ya dawo ya yi la’akari da su”.

Fa ɗ akarwa takan shafi garga ɗ i da nasiha da gyran hali da sauran hanyoyin inganta rayuwa da kuma gyara ta.

Misali a cikin fim ɗ in Jankunne an fa ɗ akar da mutane a kan yadda ake kamuwa da cutar ƙ anjamau, da kuma irin halin da samari masu neman mata suke fa ɗ awa. Babban jigon wannan fim shi ne fa ɗ akarwa a kan cutar ƙ anjamau. Sannan kuma akwai ƙ ananan jigogi da suka ha ɗ a da illar tallan 'ya mace da ha ɗ arin da ke tattare da neman mata da kuma sakamakon marar ɗ aukar shawara.

Sauran finafinan da suke ɗ auke da irin wannan jigo, sun ha ɗ a da Nasaba da Zarge da Aisha da Bada ƙ ala da Dangaye da Sihiri da jahilci ya fi Hausa da Jirwaye da Buri da Halak da Tubali da Darasi da Ƙ auli da Ruhi.

Daga cikin abubuwan da finafinan Hausa kuma sukan yi garga ɗ i a kansa, akwai nuni a kan illolin cin amana. Cin amana na nufin yi wa wani abin kirki shi kuma ya saka da na tsiya. Kuma tana faruwa a kowane ɓ angare na rayuwa kamar iyali ko abokai ma ƙ wabta ko abokan kasuwanci ko aiki da sauransu. Sannan a wannan zamanin abin ya zama uwan dare, wanda sai mutane ƙ alilan en suke kare kansu daga cin amana kuma sakamakon ta ne ya sa mutane da yawa na wannan lokaci suka kasa ci gaba a rayuwarsu. Sakamakon yawaitar cin amana a tsakanin al’umma ya sa ake shirya finafinai a kai domin tunasar da al’umma illolinta da kuma muhimmancin ri ƙ e ta domin a ci gaba da ri ƙ e ta ko a daina aikata ta. Bagery (1934:116) ya bayyana cin amana da “tona asiri ko Baraka”.

Misali a cikin fim ɗ in Maula mun ga yadda sakamakon mai cin amana ya kasance wato Hindatu Bashir da ƙ aninta Ali Nuhu wadda ta kai su har da bara a tiit, kuma babban jigon wannan wasa na Maula  shi ne fa ɗ akarwa kan cin amana domin duk sauran abubuwan da aka yi a cikin shirin an yi shi su ne domin su taimaka wajen fito da babban jigon shirin, wato fa ɗ akarwa kan cin amana. Ƙ ananan jigogin da ke cikin fim ɗ in kuwa sun ha ɗ a da taimako kamar yadda Alhaji ya taimaki Ali Nuhu da yayarsa Hindatu Bashir da Makirci kamar yadda Ciroki da Hindatu suka yi da kuma magani kamar yadda Hindatu ta yi wa Alhaji ya saki matarsa.

Haka zalika sauran finafinan da suke ɗ auke da irin wannan jigo na fa ɗ akarwa kan cin amana sun ha ɗ a da Ɗ an’uwa da Ɗ an’adam da Mukhtar da Jinsi da Juyin Mulki da Ruhi da Furuci da Saura ƙ iris da Ayah da Sufuri da Gadar zare da sauransu.

1.3.5 Jigon Wayar da Kai

Wayar da kai wata hanya ce da ake amfani da ita wajen sanar da mutane a kan wani abu da suke aikatawa ba daidai ba, kuma ana amfani da wayar da kai wajen neman al’umma su kar ɓ i wani abu da ake so su kar ɓ a daga gwamnati ko wa ɗ ansu ƙ ungiyoyi masu zaman kansu.

Gusau (1995:16) Ya bayyana wayar da kai da cewa “yakan yi ƙ o ƙ ari ne ya sanar da mutane wasu abubuwa sababbi da suke aukuwa a rayuwar yau da gobe”. Ta haka ne finafinan Hausa ke taimakawa wajen yi wa jama’a sanarwa da fa ɗ akarwa da garga ɗ i kan gyaran rayuwa.

Misali a fim ɗ in Tsautsayin Takaba mun ga yadda aka wayar wa da 'yanmata kai wajen soyayyar gaskiya maimakon ta ku ɗ i da kuma irin sakamakon da Bebi ta samu na gamuwa da cutar ƙ anjamau. Kuma babban jigon wannan fim shi ne wayar da kai, sannan akwai ƙ ananan jigogi wa ɗ anda suka ha ɗ a da cin amana kamar yadda Bebi ta yi wa Abdul da sakamakon mai kwa ɗ ayi kamar yadda Bebi ta gamu da cutar ƙ anjamau da kuma soyayya kamar yadda aka nuna a cikin fim ɗ in.

Sauran finafinan da suke ɗ auke da irin wannan jigo na wayar da kai sun ha ɗ a da Inuwar Giginya da Alheri da Linzami da Sutura da Gashin Ƙ uma da Gyale da Lokaci da Fito na Fito da Sundu ƙ i da Sansani da Halacci da Sukuni da Kasko da Ki Yarda da ni da Ƙ asarmu ce da Sadaki da Sauyi da sauransu.

1.3.6 Jigon Bandariya

Bandariya hanya ce da ake amfani da ita wajen sanya mutane su yi dariya da walwala da kuma nisha ɗ i wanda suke ɗ aukar wani darasi ta hanyar dabara.

Bargery, (1934:76) ya bayyana “bandariya da cewa ta samo asali daga “Bandare wadda take nufin mutum mai bayar da dariya ko mai sa a yi dariya”. Shi kuma Ibrahim M.S. (1976:104), ya bayyana bandariya da irin wa ƙ o ƙ in da 'yan gambara da 'yan kama da 'yan galura da 'yan ƙ oroso suke yi. Amma kuma sun bambanta ta hanyar da suke bi, su bai wa mutane dariya. Misali 'yan kama sukan ba mutane dariya ta wajen kwaikwayo da wa ƙ ar abinci. 'Yan gambara kuma ta wajen batsa da ba’a. 'Yan ƙ oroso kuma ta wajen sha ƙ iyanci da alfasha. Haka ma 'yan galura”.

A finafinan Hausa ana amfani da bandariya wajen isar da wani sa ƙ o ta hanyar wasa, wadda mutane suke koyar da wani darasi ta hanyar nisha ɗ i, yawancin finafinan bandariya Ibro ne yake shirya su, sannan ya bayyana cewa yana yin su ne domin isar da wani sa ƙ o cikin raha tun da mutane ba wa’azi suke son saurara ba. (Hira da BBC, 2003).

Misali fim ɗ in “Jahilci Ya Fi Hauka Wuyar Magani”. Babban jignsa shi ne bandariya, domin tun daga farkon shirin har ƙ arshensa jigon ya ratsa ko’ina kuma ya koyar da hanyar nisha ɗ i. Akwai kuma ƙ ananan jigogi da suka bayyana a cikin fim ɗ in wa ɗ anda suka ha ɗ a siyasar gargajiya da illar jahilci da tafiye-tafiye.

Sannan misalan finafinan da suke ɗ auke da irin wannan jigo sun ha ɗ a da Ibro Mafiya da Ibro Maitsine da Ibro D.P.O. da Ibro Siniya da Ibro Ɗ andaudu da Ibro Maishayi da Kar-ta-san-kar da Ibro Usama da Ibro Shata da Ibro Ɗ an ƙ waito da Gidauniya da Bobmai da sauransu.

1.4     Na ɗ ewa

Tun a farkon wannan takarda an yi bayanin cewa fitar da jigo a finafinan Hausa ra’ayi ne, da za a iya samun daidaito ko bambanci a tsakanin manazarta a kan wani fim da suka yi nazari a kansa .
Haka a wannan takarda an yi hasashen wasu nau’o’in jigogi da ake iya samu a finafinan Hausa kuma aka kawo misalansu. An yi magana a kan jigon ha ƙ uri da fa ɗ akarwa da siyasa da soyayya da wayar da kai da kuma ban-dariya.

Manazarta

Abdullahi, I.I. (1998). “Nazarin Littattafan Soyayya na Hausa”. Kundin Digiri na Biyu, Jami’ar Bayero, Kano .

Abdul ƙ adir, H.M. (1988). “Rayuwar Malam Ibrahim Mandawari ta Fuskar Wasan Kwaikwayo da Yunƙurin Samar da Finafinan Hausa”. Kundin Digiri na Ɗaya, Jami’ar Bayero, Kano.

Adamu, A.U. (2003). The Hausa Home Ɓideo: Media Parenting and Changing Popular Culture in Northern Nigeria (In press)

Adamu, U.A. (2004). Passage to India Media and Construction of African Identities. Essay Report of a Seminar Held in Nairobi, Kenya .

Adamu, Y. (2002). Between the Word and the Screen: A Historical Perspectiɓe on the Hausa Literary Moɓement and the Home Ɓideo Inɓasion, Journal of African Cultural Studies Ɓol. 15. No2. 203-213.

Alfred, E.O. and Opubor, O.E. (1977) .The Deɓelopment And Growth of the Film Industry in Nigeria Lagos . Third Press International.

Bargery, G.P. (1934). Hausa-English Dictionary And English-Hausa Ɓocabslary London Oɗford Uniɓersity Press.

Buhari, M. (1988). “Nazarin Jigon Wasu Littattafan Ƙagaggun Labarai na Hausa”. Kudnin digiri na Biyu, jami’ar Bayero, Kano.

Centre for Hausa Cultural Studies (2004) Hausa Home Ɓideos Technology, Economy and Society, Kano . Gidan Dabino Publishers

Chamo, I.Y. (2002). “Tasirin Al’adun Turawa a cikin Finafinan Hausa”. Kundin Digiri na Ɗaya, Jami’ar Bayero, Kano.

Ɗangambo, A. (1981). “Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa”. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Ɗ angambo, A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano : Triumph Publishing Company.

Ɗangambo, H.A. (2002). “Salon Sarrafa Jigo a Adabin Baka na Hausa: Nazari Kan Jigon Faɗakarwa”, Kundin Digiri na Ɗaya, Jami’ar Bayero, Kano.

 East R.M. da Wasu (1948) Zaman Mutum da Sana’arsa, Kamfanin NNPC, Zaria.

Funtua, A.I. (2002). Waƙoƙin Siyasa na Hausa a Jamhuriya ta Uku: Jigoginsu da Sigogsin”, Takarda da Aka gabatar a Taron Ƙara wa Juna Ilimi, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, jami’ar Bayero, Kano.

Furniss, G. (1977). “Some Aspects of modern Hausa Poetry: Hikima Poetry Circle Club in KanSo” London SOAS.

Gusau, S.M. (1983). “Waƙoƙin Noma na baka: yanaye-yanayensu da sigoginsu Musamman a Sakwkato”. Kundin Digiri na Biyu, Jami’ar Bayero, Kano.

Gusau, S.M. (1995). Saƙo a Waƙoƙin Baka: Tsokaci Kan Turke da Rabe-Rabensa”. Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna ilimi a Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Kan harshe da Adabi da Al’adun Hausawa, Jami’ar Bayero, Kano.

Ibrahim, M.S. (1976). Kowa Ya Sha Kiɗa: Abinsa ya Bayar, Kundin Digiri na Ɗaya, Jami’ar Bayero, Kano

Inuwa, U.A. (2000). “Tarbiyya cikin Finafinan Wasan Kwaikwayo na Hausa”. Kundin Digiri na Biyu, Jami’ar Bayero, Kano

Kundila, H.M. (2002). “Yadda Ake shiryawa da Gudanar da Finafinan Hausa” Kundin Digiri na Ɗaya, Jami’ar Bayero, Kano

Mashi, M.B. (1986) Waƙoƙin Baka na Siyasa: Dalilansu da Tasirinsu ga Ryuwar al’umma” Kundin Digiri na Biyu, jami’ar Bayero, Kano.

Muhammad, N.M. (2002). “Mata a cikin Finafinan Hausa, Kundin Digiri na Biyu, Jami’ar Bayero, Kano

Umar, A.A. (2002). “Gudunmawar Finafinan Zamani a Ɓangaren Adabin Hausa”. Kundin Digiri na Ɗaya, Jami’ar Bayero, Kano

'Yar’aduwa, T.M. (2001). “Wasan Kwaikwayo: sigoginsa da Jigoginsa” cikin Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies Ɓol. 1, No. 1 Department of Nigerian Languages, Bayero Uniɓersity, Kano.

  www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments