Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Cikin Saduwa Da Iyalina Sai Ladan Ya Yi Kiran Sallar Asalatu

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Ina cikin saduwa da iyalina sai ladan ya yi kiran sallar asalatu (Watau Al-fijir Ya keto) Shin mene matsayin azumina? Shin akwai kaffara a kaina?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Na'am yayin dakake cikin saduwa da iyyalinka sai ladanin unguwarku ko na wata unguwar ya yi kiran sallar Asalatu to idan wannan kiran Asalatun kirane na farko watau alfijir bai keto ba to babu ruwanka da wannan kiran sallah zaka cigaba da saduwa da iyyalinka ne tunda al-fijir bai keto ba.

Amma idan wannan kiran sallar Asalatun yakasance kirane na biyu haka kuma a lokacin da kake wannan saduwar da iyyalinka ka tabbata ba hakikanin ce alfijir bai keto ba wannnan ladanin ya yi kiran sallar Asalatu na biyu to ananma babu ruwanka da wannan kiran sallar zaka cigaba da saduwa da iyyalinka ne har sai ka tabbata al-fijir yaketo.

Haka kuma idan yakasance wannan kiran sallar da ladani ya yi watau kirane na Asalatu na biyu kuma hakika a wannan lokacin alfijir yaketo to abinda zakayi shine wajibi ne ka fitar da Azzakarinka daga cikin farjin iyyalinka domin dakatawa da saduwa da iyyalinka. Idan kayi haka to babu abinda yasami azuminka sai kaje kayi wanka.

Amma idan kacigaba da saduwa da iyyalinka alhali lokacin da ladani yake kiran sallah Asalatu na biyu kuma a wannan lokacin kasan cewa hakika alfijir yaketo to kasani wajibi ne karama wannnan Azumin wannan ranar sa'annan wajibi ne kayi kaffara wajan yanta bawa guda ɗaya, idan babu bawan dazaka yanta kamar a wannnan zamanin to wajibi ne da mutum ya yi azumin wata biyu bayan sallah, idan mutum yana da larura rashin yin azumi to wajibi ne da yaciyar da mutum 60 daidai rabin Sa'a na abinci. Sa'a guda na abinci shine=3kg saboda haka rabin sa'a na abinci shine =1.5kg watau mutum 60.

Hakama itama matar wannan kaffara ta hau kanta muddin ta tabbatar da cewa alfijir yaketo sa'annan takyale mijinta yacigaba da saduwa da ita a wannnan lokacin. Idan kuma mijin ne ya tilastata yacigaba da saduwa da ita a wannan lokacin to muddin tana da ikon hannashi saduwa da ita to wajibi ne data kaurace masa wajan janye jikinta daga gareshi a wannan lokacin da yake saduwa da ita bayan tayi yakini cewa alfijir yaketo to harramunne a gareta domin yin biyayya ga mijinta a wannan lokacin saɓawa Allah ta ala ne. Allah ta'ala yana cewa

وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَىٰ وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ

kutaimakawa ɗan'uwanku wajan aikata alkairi da tsoran Allah, kada kutaimakawa wani wajan saɓon Allah da wuce iyyaka. (Suratul Mâ'ida Aya ta 2)

Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) yana cewa

لاطاعةفي المعصية إنماالطاعةفي المعروف

Ba ayin biyayya ga aikata saɓo (watau saɓawa Allah) bisa umarnin duk wani mahaluki, anayin biyayyane ga abinda addinin musulinci ya amince da aikatawa ne (watau Al-Ma aruf). [Sahih Bukhari hadisi no 7257], da [Sahih Muslim hadisi no 1840].

Muddin ta amince masa yin haka to itama kaffara ta kamata domin tasan cewa tana aikata saɓo.

Idan kuma ya tilastatane bisa aikata saɓo babu yadda zata iyya bijire masa sakamakon tana matukar tsoransa bisa cutarwarsa to ita takasance bata da laifin komai shikuma kaffara kashi biyu ta hau kansa.

Hujjar yin kaffara kuwa ya tafi akan dogaran hadisin da yazo daga Malik daga Imam Shihab (watau Imam Zuhuri) cewa wani mutum yasadu da iyyalinsa da gangan da rana lokacin azumin Ramadan sai Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) ya umarceshi dayin kaffara na sakin bawa, ko azumin wata biyu ko ciyar da miskinai 60 daidai rabin sa'a na abinci. [Sahih Muslim hadisi no 1111] da [Muwat Malik hadisi no 1/296-297] da [Sunan Abu-Dawud hadisi no 2392, Sahih].

Allah shine mafi sani

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments