Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Azumin Wanda Ya Fitar Da Maziyyi Da Gangan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum da fatan Malam yana nan lfy. Ya iyali. Mallam inada tambaya? Mallam menene hukuncin azumin wadda ya fitar da maziyyi ta hanyar tunani ko kuma taɓa jikin mace.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Wanda ya fitar da maziyyi da gangan ta hanyar taɓa jikin mace ko ta dalilin yawaita tunani akan abinda ya shafi jima'i, to tabbas azuminsa ya karye. Kuma zai rama azumi ɗaya ne amadadin wannan da ya karya ɗin. Wannan ita ce fatawar Mazhabin Imamuna Malik.

Don Qarin bayani aduba litattafan fiqhun Malikiyyah kamar Muqaddimatul Iziyyah da Risalatul Qairawaniy.

WALLAHU A'ALAM. 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments