Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Hadiye Yawu Da Kaki Ga Mai Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam. Mene ne hukuncin haɗiye yawu da kaki ga mai azumi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

Yawu baya cutar da azumi, don haka in aka haɗiye shi babu komai, kamar yadda idan aka tofar da shi babu komai. Amma kaki da ke fitowa daga qirji ko daga hanci, wanda larabawa ke kira (nukhamah), ko kuma (nukha'ah) wanda shi kuma shi ne kaki mai kauri da ke fitowa daga qirji ko kuma daga kai, irin Waɗannan wajibi ne ga mutum namiji ko mace tofar da shi, da fitar da shi, da rashin haɗiye shi. Yayin da shi kuma yawu na al'ada babu matsala akansa, kuma baya cutar da mai azumi; namiji ne ko mace.

MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 313).

ALLAH NE MAFI SANI.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments