Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Ci Ko Ya Sha Da Mantuwa, Alhali Yana Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Menene hukuncin wanda ya ci ko ya sha da mantuwa, a cikin yinin ramadana?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Babu wata matsala akansa kuma azuminsa ingantacce ne, saboda fadin Allah a qarshen suratul baqara ayata 286:

رَبَّنَا لاَ تُؤَاخِذْنَا إِن نَّسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا

MA'ANA: "Ya Ubangijinmu kada ka kama mu idan muka yi mantuwa ko muka yi kuskure"

Kuma ya inganta daga Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) cewa Allah Ta'alah ya ce:

قد فعلت.

Ma'ana: "Lallai na Amsa"

Muslim ya rawaito shi daga hadisin Abdullahi bn Abbas (ra), a lamba ta 1206).

Da kuma abin da ya tabbata daga Abu-huraira (ra) daga Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) lallai ya ce: "Duk wanda ya manta -alhalin yana azumi sai ya ci ko ya sha, to ya cika azuminsa; saboda Allah ne ya ciyar da shi, ya kuma shayar da shi"

Bukhari da Muslim su ka rawaito shi.

👉Duba cikin littafin: TUHFATUL IKHWAN, (tambaya

ta 16), da

👉 MAJMU'U FATAWA WA MAKAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 291-292).

ALLAH NE MAFI SANI

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments