Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Ci Abinci Da Rashin Sanin Cewa Al-Fijir Ya Keto

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum ina kwana mallam. Nine zanyi azumi sai na makara na tashi ankira assalatu Amma ba'a shiga sallah a anguwanmu ba Kuma banji Ana sallah a wani waje ba Sai nace bari nasha ko ruwane Ina sha kawai sai naji an tada kabbara, Shin zan cigaba da azumin ne ko Babu azumin?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalam Warahmatullahi Wabarakatuh.

Mallamai sun yi saɓani game da wanda yaci wani abu ko ya sha akan rashin sanin cewa alfijir ya riga ya fito zuwa maganganu guda biyu

1. kashin farko na mallamai suna ganin wanda ya ci wani abu ko yasha a tsammanin shi alfijir bai fito ba sai daga baya yasan cewa alfijir ya riga ya fito to zai cigaba da azumin shi sannan zai rama wannan yinin. wannan shine ra'ayin Imamu Abi haneefa da Malik bin Anas da Imamushshafi'i da Imamu Ahmad bin Hanbal.

2. Kashi na biyu na mallamai suna ganin zai cigaba da azumin shi sannan azumin yayi ba zai rama ba. Wannan shine ra'ayin Ishaq bin Rahawaihi da riwaya daga Imamu Ahmad bin Hanbal da Imamul Muzani da Ibnu Taimiyya da Dawuduzzahiri da Ibnu Hazmi, dawasu daga cikin magabata, dalilansu faɗin Allah (S.W.T)

رَبَّنَا لاَ تُؤَاخِذْنَا إِن نَّسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا

Ya Allah kada Ka kama mu da laifin da mukayi akan mantuwa ko kuskure, (Suratul baqara, Ãya ta 286)

Shiyasa sukace wannan shi kuma yayi ne akan rashin sani kuma duk wanda yayi abu akan rashin sani ba'akamashi da laifi.

Sannan suka kara kafa hujja da faɗin Allah SWT

 ۚ وَلَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ فِيمَا أَخْطَأْتُم بِهِ وَلَٰكِن مَّا تَعَمَّدَتْ قُلُوبُكُمْ ۚ

Babu laifi akan abin da kuka yi shi akan kuskure matukan bakuyishi da gangan ba. (Suratul Ahzab Aya ta 5).

Sai kuma suka kafa hujja da hadisin Asma'u bintu Abubakar wanda tayi tafiya da Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) sai suka yi buɗa baki akan kuskure sai daga baya suka gane cewa rana bata faɗi ba, Imamul Bukhari a cikin littafin shi Aljaami'ussahih hadisi da (1959).

Amma Abinda Mallamai suka rinjayar ra'ayi na biyu cewa azumin shi ya yi bazai rama ba.

WALLAHU A'ALAM

DR NASIR YAHYA ABUBAKAR BIRNIN GWARI

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments