Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Ciki Ko Mai Sayarwa Za Su Iya Aje Azumi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin yana halasta ga mai ciki ko mai shayarwa ta ajiye azumi??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Shaikh Ibnu baaz Allah ya masa rahama yana cewa "Mai ciki da Mai shayarwa hukuncinsu ɗaya ne da mara lafiya, idan azumi zai basu wahala ya halasta su ajiye, sai su rama adadin kwanakin da suka sha kamar mara lafiya. Wasu daga cikin malamai sun tafi akan cewa ya halasta su ciyar da abinci kawai akowace rana, amma wannan magana tanada rauni, abinda yafi inganci shine zasu rama azumin kamar matafiyi da mara lafiya, saboda faɗin Allah Subhanahu wata'ala

وَمَنْ كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِنْ أَيَّامٍ أُخَرَ يُرِيدُ اللَّهُ بِكُمُ الْيُسْرَ وَلَا يُرِيدُ بِكُمُ الْعُسْر

Kuma wanda ya zama mara lafiya ko a cikin tafiya to sai ya biya a waɗansu adadin kwanaki na daban. Allaah yana nufin sauƙi ne gare ku, kuma baya nufin tsanani a gare ku. (Surah Al-Baqarah: 185).

Haka kuma yazo a hadisin Anas bin Malik Al-Ka'abi; Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace "lalle Allah ya sauƙe azumi akan matafiyi, ya kuma rage masa sallah, ga mai ciki ko shayarwa kuma sai ya sauƙe musu azumi".

WALLAHU A’ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUq2GCCzlcdL6nknqLYYox

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments