Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mai Barin Lokacin Sallah Ya Fita Da Gangan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullah. Allah gafarta malam mutun ne ya balaga amman ba ya cika sallah sai daga baya ya cigaba da sallah cikakka, to ya zai yi da waɗanda bai cika ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalamu wa rahmatullah. Ƴar'uwa game da wanda ya balaga amma ya zama ba ya cika sallolinsa, wani lokacin ya yi, wani lokacin ya qi yi, mai yin wannan ba ya rasa nasaba da halaye guda biyu, ko dai ya zamana ya bar sallah har lokacinta ya fita saboda wani uzuri da sharia'a ta yarda da shi, ko kuma ya zamana ya bar sallah ne da ganganci, ba tare da wani uzuri ba, wato kawai sakaci ne, duk malamai sun yi maganganu a kan haka filla-filla.

Sai dai kafin mu je ga kawo maganganun manyan malaman Musulunci, yana da kyau a sani cewa duk wanda ya bar sallah saboda wani uzuri da shari'a ta yarda da shi a matsayin uzuri karɓaɓɓe kamar barci ko mantuwa, ko suma ko taɓin hankali har lokacin sallah ya wuce, wannan ba laifi a kansa, kamar yadda hadisin da Bukhariy ya ruwaito daga Anas ɗan Malik r.a cewa, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya ce: "Duk wanda ya mance da wata sallah to ya sallace ta a lokacin da ya tuna da ita, ba ta da wata kaffara sai hakan". Sahihul Bukhariy 572.

A ruwayar Imamu Muslim kuwa, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam cewa ya yi: "Idan ɗayanku ya yi barci bai sami sallah ba, ko ya mance da ita, to ya sallace ta a lokacin da ya tuna da ita, saboda Allah mai girma da buwaya yana cewa

وَأَقِمِ الصَّلَاةَ لِذِكْرِي

 "ka tsayar da sallah don ambatona" (Suratu Daha 14). Sahihu Muslim 684.

Waɗannan dalilan ke nuna cewa idan mutum ya bar sallah bai yi ta ba har lokacinta ya wuce saboda wata lalura ko uzuri karɓaɓɓe wajibi ne ya rama ta a duk lokacin da ya tuna ta, ko ya sami dama. Saɓanin wanda ya bar lokacinta ya wuce ta dalilin lalaci ko wata harkar duniya, shi wannan malamai sun yi kai komo a kan halascin rama sallarsa da ya bari lokacinta ya wuce da ganganci, ga kaɗan daga maganganun malamai

Ibn Hazm ya bayyana cewa: "Duk wanda ya bar sallah har lokacinta ya wuce da gangan, to wannan mutum ba zai rama wannan sallah ba har abada, sai dai kawai ya yawaita yin ayyukan alheri, da yin sallolin taɗawwu'i (nafila), ya nauyaya mizaninsa saboda gobe Qiyama, sannan ya tuba zuwa ga Allah, ya kuma yawaita yin istigfari".

"Amma Imamu Abu Haneefa da Imamu Malik da Imamus Shafi'iy sun ce: Zai rama sallar da ta kuɓuce masa ko da lokacinta ya fita da gangan. Har ma ta kai ga Malik da Abu Haneefa sun ce: Duk wanda ya bar wata sallah ko wasu salloli da gangan zai rama su kafin ya sallaci wadda ake cikin lokacinta, in ya kasance sallolin da ya bari da gangan ɗin guda biyar ne ko qasa da biyar, amma idan sun wuce salloli biyar, dai-dai ne lokacin wadda ake ciki ne ko lokacinta ya wuce; idan sallolin da ake binsa sun wuce guda biyar, to zai fara da wadda ake cikin lokacinta ne". Duba ALMUHALLA 2/10.

Bayan waɗannan akwai manyan malaman Sahabbai da Tabi’ai da suke da fahimtar cewa duk wanda ya bar lokacin sallah ya wuce da gan-gan bai yi ta ba, to ba zai rama ba, sai dai kawai ya yi ta yin istigfari a kan wannan laifi, daga cikinsu akwai Sayyiduna Umar ɗan Khaɗɗab, da ɗansa Abdullahi, da Sa'ad bin Abiy Waqqas, da Sulaimanu, da Ibn Mas'ud da Qasim ɗan Muhammad ɗan Abubakar, da Badeel Al’uqailiy, da Muhammad ɗan Seereen, da Muxarrif ɗan Abdullahi, da Umar Ɗan Abdulaziz, da wasunsu. Almuhalla 2/13.

A taqaice dai wannan matsala ce da ta sha wahala a hannun malaman Musulunci tun da can.

Amma bayan da Imamus Shaukaniy ya gama lissafo hujjojin Malaman da suke ganin wanda ya bar lokacin sallah ya wuce da gan-gan ba zai rama ba, da kuma hujjojin malaman da suke ganin mai sakaci har lokacin sallah ya fita zai rama, sai ya rinjayar da maganarsa da cewa

"Allah ne mafi sani, maganar da ta fi rinjaye ita ce, lallai mai barin lokacin sallah ya fita da gangan ba zai rama sallar ba, abin da ya wajaba a kansa shi ne istigfari da tuba zuwa ga Allah".

Don qarin bayani duba littafin Shaukaniy Nailul Auɗar, a qarqashin sharhin hadisi mai lamba 479.

WATA FA'IDA;

Idan ana bin mutum bashin sallolin da bai san iya adadinsu ba saboda wata lalura ko uzuri karɓaɓɓe a Shari'a da ya sami kansa a ciki, to wanda ya sami kansa a irin wannan hali zai yi ta yin sallah ne iya adadin da shakka za ta yanke a zuciyarsa. KITABUL AKHDARIY shafi na 53.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments