Ticker

6/recent/ticker-posts

Zama Da Mijin Da Baya Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mijin da sai ya yi kwana biyu bai yi sallah ba, sannan kuma ko-a-jikin-shi! Idan aka yi masa nasiha sai ya ce zai gyara, in sha Allah! Kullum maganar kenan. Shin ko ya halatta a cigaba da zama da shi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Sallah babba ce daga cikin ƙarfafan ginshiƙan da suka riƙe addinin musulunci, kamar yadda Al-Imaam Muslim (122) ya riwaito maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

« بُنِىَ الإِسْلاَمُ عَلَى خَمْسٍ : شَهَادَةِ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ ، وَإِقَامِ الصَّلاَةِ ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ ، وَحَجِّ الْبَيْتِ ، وَصَوْمِ رَمَضَانَ »

An gina musulunci a kan abubuwa biyar ne: Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allaah, kuma cewa: Annabi Muhammad Bawansa ne kuma Manzonsa ne; da tsaida Sallah; da bayar da Zakkah; da Hajjin Ɗakin Allaah; da Azumin Ramadan.

Don haka ne malamai suka yi ijma’i ba tare da wani saɓani a tsakaninsu ba cewa: Duk mutumin da ya yi musun wajibcin sallah, to ya zama kafiri mai ridda kenan daga addinin musulunci. Amma idan ba ya yin sallar saboda kasala ce: Ba ya yin ta kwata-kwata har zuwa mutuwarsa, wannan kam kafiri ne, saboda hadisi sahihi da Al-Imaam At-Tirmiziy (2830) ya riwaito da isnadinsa har zuwa ga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

« الْعَهْدُ الَّذِى بَيْنَنَا وَبَيْنَهُمُ الصَّلاَةُ فَمَنْ تَرَكَهَا فَقَدْ كَفَرَ »

Alƙawarin da ke tsakaninmu da su ita ce sallah, don haka duk wanda ya bar ta, to kuwa ya kafirce.

Kamar yadda ya sake riwaito sahihiyar riwaya (2831) daga Abdullaah Bn Shaqeeq ya ce

كَانَ أَصْحَابُ مُحَمَّدٍ -صلى الله عليه وسلم- لاَ يَرَوْنَ شَيْئًا مِنَ الأَعْمَالِ تَرْكُهُ كُفْرٌ غَيْرَ الصَّلاَة

Sahabban Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) sun kasance babu wani abu daga cikin ayyukan musulunci da suke ganin barin yin sa kafirci ne sai dai Sallah.

Amma wanda yake yin sallar a wani lokaci, kuma ya bar yin ta a wani lokaci, to wannan ya shigar da kansa a cikin alƙawarin azabar Allaah Subhaanahu Wa Taaala. Al-Imaam Ibn Maajah (1465) ya riwaito hadisi sahihi daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

« خَمْسُ صَلَوَاتٍ افْتَرَضَهُنَّ اللَّهُ عَلَى عِبَادِهِ فَمَنْ جَاءَ بِهِنَّ لَمْ يَنْتَقِصْ مِنْهُنَّ شَيْئًا اسْتِخْفَافًا بِحَقِّهِنَّ فَإِنَّ اللَّهَ جَاعِلٌ لَهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَهْدًا أَنْ يُدْخِلَهُ الْجَنَّةَ وَمَنْ جَاءَ بِهِنَّ قَدِ انْتَقَصَ مِنْهُنَّ شَيْئًا اسْتِخْفَافًا بِحَقِّهِنَّ لَمْ يَكُنْ لَهُ عِنْدَ اللَّهِ عَهْدٌ إِنْ شَاءَ عَذَّبَهُ وَإِنْ شَاءَ غَفَرَ لَهُ »

Salloli guda biyar Allaah ya farlanta su a kan bayinsa: Duk wanda ya zo da su, bai rage komai daga cikinsu domin wulaƙantar da alamarinsu ba, to yana da alƙawari a wurin Allaah a Ranar Al-Qiyamah cewa zai shigar da shi Aljannah. Wanda kuma ya zo da su alhalin ya rage wani abu daga cikinsu saboda wulaƙantar da alamarinsu, to ba shi da wani alƙawari a wurin Allaah, in ya ga dama ya azabtar da shi, in kuma ya ga dama ya gafarta masa.

Don haka, matuƙar dai wannan mijin bai zama kafiri da wannan saɓon ba, to ba za a ce matar ta rabu da shi ba. Amma kuma wajibi ne ta cigaba da yi masa nasiha ta amfani da Ayoyi da Hadisan zaburarwa da tsoratarwa a kan haka. Sai kuma ta sanar da makusantansa kafin manyansa zuwa ga shugabannin addini da masu iko, domin a dawo da shi kan hanya kafin zuwan mutuwarsa.

Allaah ya shiryar da mu gaba-ɗaya.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

08164363661

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments