Ticker

6/recent/ticker-posts

Rama Cuta Ta Hanyar Sihiri

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Wani ne yake bin mutum domin ya kashe shi ko ya lalata masa rayuwa ta hanyar sihiri, to ko ya halatta shi ma ya bi wannan hanyar domin ya ga bayan sa kafin shi ya iya cutar da shi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Bai halata musulmi ya bi hanyar sihiri domin warware sihiri ko domin ya kare kansa ko ya ɗauki fansa a kan wanda ya cutar da shi ta hanyar sihirin ba. An tambayi Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alaa Alihi Wa Sallam) a kan ‘an-nushrah’ wato warware sihiri sai ya ce

هِيَ مِنَ الشَّيْطَانِ.

Daga aikin sheɗan ne. (Ahmad ya riwaito shi, kuma sanadinsa nagrtacce ne).

Abu-Daawud ya ce: An tambayi Ahmad a kan hakan sai ya ce

 ابنُ مَسْعُودٍ يَكْرَهُ هَذَا كُلَّهُ.

Ibn Mas’ud yana ƙyamatar dukkan hakan.

Wannan a kan an-nushrah da ake bin hanyoyin bokaye na mu’amala da sheɗanu kenan.

Amma idan hanyar ruqya ta Sunnah ce, kamar a samu musulmin kirki masani ya yi wa mara lafiyan ruqya da ayoyin Alqur’ani da Sahihan addu’o’in Sunnah, wannan daidai ne ba laifi ba ne. Qataadah ya tambayi Sa’eed Bn Al-Musayyib (Rahimahumal Laah) a kan mutumin da aka yi wa sihiri har ba ya iya kusantar iyalinsa, ko za a iya warware masa? Sai ya ce

لَا بَأْسَ بِهِ، إنَّمَا يُرِيدُونَ بِهِ الْإصْلَاحَ ، فَأمَّا مَا يَنْفَعُ فَلَمْ يُنْهَ عَنْهُ.

Babu laifi ga hakan. Ai gyara suke nema kawai da shi. Amma abin da zai amfanar ba a hana yin shi ba.

Wannan duk a cikin Fat-hul Majeed (shafi: 302).

A taƙaice dai: Haƙuri da dogaro ga Allaah su ne babban magani. Sai kuma kulawa da Zikirori da Adduoin da suka tabbata a cikin Sunnah Sahihiya.

Amma komawa ga bin hanyoyin bokaye domin neman kariya ko ɗaukar fansa a kan wanda ake zaton yana yin wannan abin, ba daidai ba ne. Kamar wanke kashi ne da fitsari!

Kuma ƙara ƙarfafa wa bokaye gwiwa ne da ɗaure musu gindi a kan ɓarnarsu da cigaba da yaɗa sharrorinsu a cikin al’umma. Tun tuni dai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi tsawa a kan zuwa wurinsu, ya ce

« مَنْ أَتَى عَرَّافًا فَسَأَلَهُ عَنْ شَىْءٍ لَمْ تُقْبَلْ لَهُ صَلاَةٌ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً ».

Duk wanda ya je wurin mai duba kuma ya tambaye shi a kan wani abu, ba za a karɓi sallarsa na kwana arba’in ba. (Sahih Muslim: 5957).

Sannan kuma ya ce

« مَنْ أَتَى كَاهِناً أَوْ عَرَّافاً فَصَدَّقَهُ بِمَا يَقُولُ فَقَدْ كَفَرَ بِمَا أُنْزِلَ عَلَى مُحَمَّدٍ ».

Duk wanda ya je wurin boka ko mai duba kuma ya gaskata shi a kan abin da yake faɗa, to ya kafirce wa abin da aka saukar wa Annabi Muhammad. (Ahmad (9536), Ibn Maajah (639), Ad-Daarimiy (1176) daga hadisin bu-Hurairah kuma Sahihi ne in ji Al-Albaaniy a cikin Sahih Ibn Maajah da Al-Arna’uut a cikin ta’aleeq na Musnad).

Allaah ya ƙara tsare mu daga sharrin masharranta na ɓoye da na bayyane.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments