Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Sadu Da Matarsa Da Rana A Watan Ramadan Kuma Ba Zan Iya Yin Kaffara Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assaalamu Alaikum Dr. Ina da tambaya game da Hadisin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) akan wani mutum da ya sadu da matarsa da rana cikin Ramadan, duba da yadda Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya warware masa matsalarsa, to idan har an sami wani ya sadu da matarsa da azumin kuma ba zai iya Azumi, ƴanta wuyaye ko ciyarwa ba, kuma bai sami wanda zai ba shi abin da zai ciyar ba, yaya zai yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. To ɗan uwa, ƙissar da ka faɗa ta zo a Hadisi tabbatacce mai lamba ta (616) a cikin Sahihil Bukhari, saidai Malamai sun yi saɓani akan abin da ka tambaya zuwa zantuttuka guda biyu

1. Kaffarar ba za ta faɗi a kansa ba, za ta wanzu har zuwa lokacin da zai samu damar yin ɗaya daga cikinsu, kamar yadda suke a jere a Hadisin, saboda Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) a cikin Hadisin bai ce masa kaffara ta faɗi a kansa ba, ya yi masa shiru ne.

2. Kaffarar ta faɗi akansa, saboda lokacin da ya ce ba zai iya ba, Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) ya bar masa dabinon don ya ciyar da iyalansa.

Wasu Malaman suna rinjayar da zance na ƙarshe, saboda shi ne ya fi dacewa da zahirin Hadisin.

Don neman ƙarin bayani, duba: Al-minhaaj na Nawawy 3/182-183.

Allah ne mafi sani.

 Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments