𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Wasu matan jini ba ya ɗauke musu sai na kwana
biyu ko uku kawai sai ya sake dawowa, meye hukuncin azumin mace da sallanta a
irin wannan yanayin??
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Abunda yake sananne ne awurin
mafiya yawan malamai shine idan mace tana al'ada sai tayi tsarki to zatayi
wanka ta cigaba da Sallah da azumi, amma abinda zata gani bayan kwana biyu ko
uku ba haila bane, domin mafi ƙarancin tsarki awurin waɗannan malaman kwana goma
sha uku ne.
Wasu malaman kuma sukace: aduk lokacin da mace
ta ga jini to haila ne, idan taga tsarki to tsarkine, koda kuwa tsakanin hailan
farko da ta biyun bai kai kwana goma sha ukun ba"
Dawowar Jinin Al'ada
TAMBAYA (151)❓
Assalamu alaikum Malam Ina yini
ya aiki. Allah ya taimaka Malam dan Allah wata yar tambaya gare ni.
Nayi alada ne sati 4 da suka wuce
har na fara sallah nah Kawai Sai satin da ya gabata jini ya dawo min Amma ba
jini din nan dai da muka sani bani wannan wani brown ne haka yau sati daya
kenan yaki tafiya ni kuma nayi wanka nah Ina sallah toh bansan ya matsayin
sallar nawa take bah
AMSA❗
Waalaikumus salam warahmatullahi
wabarakatuhu
Anan Zaki duba nau'in jinin ne.
Idan nau'insa yayi kama da na haila to zaki dakatar da Ibadah ne saboda wannan
alamu ne na cigaban al'ada amman idan nau'insa ba na haila bane to zaki dauke
shi ne a matsayin jinin Istihadha sannan Kuma zaki ci gaba da ibadarki saidai
zaki dinga sabunta alwala a tsakanin kowacce sallah
(Sahihul Bukhari [Arabic-English]
Vol. 1 page 149 - Hadith #228)
Wallahu taala a'alam
Subhanakallahumma wabi hamdika
ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa
Usman Danliti Mato
(Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
HUKUNCIN
DAWOWAR JININ AL'ADA BAYAN YA ƊAUKE:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Na gama al'ada da kwana takwas
Kuma se jini ya dawo min ,to wannan jinin wani sabon haila ne ko Kuma sauran
Wanda na yi ne ko Kuma jinin istihada ne? Kuma idan jinin istihada ne idan zan
yi sallah ya zan yi niyyan wankan shin niyan wankan alokacin da yake zuba da
Kuma bayan ya yanke duk iri dayane ko Kuma akwai bambanci? Sannan Kuma idan
mace ta gama haila ba tare da ta yi wanka ba mijinta ze iya kusantan ta,? Kuma
idan hakane ya za ta yi niyan wankan? Allah ya ƙara ilimi me amfani
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis Salaam:-
Toh Idan misalin kina yin Jinin Hailar ki na
kwanaki 5 ne, sai Kuma Kika Yi Kwanaki biyar ɗin sai Jinin ya Ɗauke, Kika Yi wankan Ɗaukewar Jinin Hailar ki, sai Bayan kwana 8 sai ya dawo, toh wannan Sabon
Jini ne, Amma wasu Malaman Suka ce sai dai idan tsakanin ɗaukewar Jinin ki, da Wadda ya dawo tsakanin sa ya Kai
Kwanaki 10 ko 15, toh duk wannan Sabon Jini ne. Kuma ana irga wannan a matsayin
cewa kin yi tsarki 2 idan Idda kike yi.
Idan Kuma ba ki Cika kwanaki biyar ɗin da Kika sabayi a kowanne wata ba sai ya Ɗauke, Bayan Kwanaki 8
sai ya dawo, toh wannan ba Sabon Jini bane Tsohon Jinin ki ne har yanzu ya
dawo. Ko Kuma kin Yi Kwana biyu ko 3 ya ɗauke ya sake
dawowa, duk Tsohon Jinin ne. Amma idan ya Kai Kwanaki 10 ko 15 ko 8 ɗin da kika ce, toh wannan lissafin Sabon Jini ne.
Shi jinin Istihala Bai Hana yin Jima'i da Mace,
sabida haka Mijin ki na iya yin Jima'i da ke indai jinin Ciwo ne, Sa'annan Kuma
shi jinin Ciwo Bai Hana yin ibada kowane irin ibada, domin ba Jinin Haila bane,
wato Ciwo ne yake damun ki don haka Sai ki nemi Magani, Wata kila Ko Kin taɓa yin Planning, ko kuma kina da Infection Shiyasa Jinin
ki Zai Rikice irin Haka.
Idan kin Yi Wankan Ɗaukewar Jinin Hailar ki na Farko da Kika Cika
Kwanaki Biyar Ɗin ki da kika
saba yin su kowane wata, toh Shikenan idan Jinin Istihala ya zo Miki wanke
gurin kawai za ki yi Kamar Yadda kike yin Tsarki, idan Kuma jinin Yana zuba
Sosai, nan kuma Sai kiyi Kumzugu a hakan zaki yi ibadar ki babu Ruwan ki da
wannan Jinin indai na Ciwo ne.
Amma idan Jinin bawai Jinin Istihala bane, wato
Jinin Hailar ki, Amma Yana rikici ya zo yau gobe ya Ɗauke gata ya dawo, toh Nan Kuma duk Lokacin da
Jinin Hailar ya ɗauke, toh Za ki
yi Wankan Ɗaukewar Jinin
Haila, idan ya dawo, sai ki sake Dakatar da yin ibadar ki, idan ya ɗauke Ki sake yin Niyya ki yi Wankan Ɗaukewar Jinin Hailar ki, a Haka za ki yi ta Yi har
Cika iya Adadin kwanakin ki da Kika saba yin su kowanne wata, kwanakin na Cika
sai kiyi Wanka na Karshe daga Nan Kuma ko kin ga wani Jinin, toh jinin Istihala
ne ba Hailar ki bane, domin kin Gama Jinin Hailar ki.
Idan kin irga iya kwanakin da kika Saba yin Jinin
Hailar amma bai ɗauke ba, toh
kina iya Kara kwana 3 akan kwana 5 ya zama 8 kenan, idan kin Kara ukun ya cika
8 bai ɗauke ba, toh sai ki sake Kara kwana 3 ya zama 11 kenan,
idan yayi 11 bai ɗauke ba, sai ki
sake Kara 3 ya zama 14 kenan idan bai dauke ba, sai ki Kara kwana 1 tak ya zama
15 idan bai ɗauke ba a rana ta 16
kawai sai kiyi wanka ki kama yin ibadar ki, kin zama me jinin Ciwo.
Amma waɗannan Karin
kwanakin sai irin ga mata waɗanda su ba su
san iya adadin kwanakin jinin hailar su bane kamar misalin ace ba ki wuce irin
shekara 1 ko 2 da fara yin jinin haila ba, amma irin wadda ta Kai shekara 20 ko
10 tana yin Jinin haila kowane wata bata wuce kwanaki 5 jinin zai ɗauke mata bai taɓa haurawa a
kwanaki biyar ɗin ba kuma kin fi
shekara 10 ko 20 haka kika Saba yin sa, toh kin ga ke kin San Jinin hailar ki
kawai za ki yi amfani da asalin kwanakin ki hailar ki ko ya ɗauke ko bai ɗauke ba kawai za
ki yi wanka ki kama yin ibadar ki ne.
Sa'annan ga waɗanda suka yi Family planning jinin su yake zuba har ya
wuce kwanakin hailar su, su ma wasu Malaman suka ce tunda jinin ya zama na Ciwo
dalilin Family planning naki kin San me ya kawo shi toh kema babu abun da za ki
Kara akan kwanakin ki da kika Saba yin su kowane wata, akwai waɗanda suka ce a'a tunda an Shar'anta cewa kwanaki 15 ne
toh kema za ki yi ta Kara waɗannan kwanakin
har sai kin zo 15 in bai ɗauke ba sai kiyi
wanka.
Sa'annan idan kin san yaya jinin hailar ki yake
kina iya Banbance wannan Jinin Ciwo ne, wannan Jinin Haila ne, toh ba ki
Bukatar Karin wasu kwanakin kawai idan kin yi kwanaki Biyar naki sun Cika sai
ki duba Jinin dakyau yaya yake? idan kin ga har yanzu komai nashi iri ɗaya ne da Jinin hailar ki shikenan jinin hailar ne domin
yana iya Kara kwanakin zuwan sa, idan kin ga cewa bai yi kama da irin wannan
jinin hailar naki ba shikenan kawai sai kiyi wanka ki kama yin ibadar ki ba sai
kin Kara wasu kwanakin ba, waɗanda suke Kara
kwanakin sune waɗanda ba su iya
Banbance yaya jinin hailar yake? yaya jinin Ciwo yake? sa'annan ba su San iya
adadin kwanakin hailar su ba.
Sa'annan bai kamata Miji ya Sadu da Matar sa a
Lokacin da ta Gama Hailar ta, Amma batayi Wankan Ɗaukewar Jinin Hailar ta ba, domin Allah ya ce idan
Matayen ku Sun Tsarkaka Sun Yi Wanka, toh Ku Zo musu ta Inda Kuke so, Amma
Banda Saduwa ta Dubura. Saboda Haka kuskure ne Jinin Hailar ki ya ɗauke bakiyi Wankan Ɗaukewar jinin haila ba, wai Mijin ki ya zo ya sadu da ke saurin me yake
Yi?, indai ya sadu da ke bakiyi wanka ba, toh bakuyi abun da Allah da Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam suka ce ba.
Kuma a hakan ma ana iya Ɗaukar Ciwo domin ai akwai Sauran Jinin Hailar a
Farjin ki Yana Nan ba ki Wanke shi ba, Kuma shi ace ya hakaru na Kwana nawa Bai
sadu da ke ba, Babu Abun da ya same shi a rayuwar sa, Dan Hakuri da zai Yi na
Mintuna 30 kawai kiyi wankan ki Ki gama shine zai gagare shi? Ai idan ma kin Yi
Wankan ki kin yi kwalliyar ki kina Kamshi hakan zai fi Kara ba shi Karfin
Sha'awa yayi abun da yake so kema har ki ji daɗi Shima ya ji daɗi, Amma a hakan
wani Sha'awa zai ji bayan Yana ganin Kwanakin ki nawa Jini na zuba miki ba ki
Kamshi, ba ki komai Kamanin ki ma ya Ɗan Chanja. Sabida Haka a ji tsoron Allah a Rike Dokar Allah. Dafatan kin
gane Koh?
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.