Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Ruwa Mai Yauki Da Yake Zubowa Mace Bayan Ta Gama Haila

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Dan Allah Malam tambaya ce Dani kamar haka: Da azumi ne bayan an kira sallar magriba naci dabino nasha ruwa, naje zanyi alwala ina tsugunnawa sai naga jini yazo min kuma ban gansa akan pant dina ba. Ina tunanin adaidai lokacin yazo. Shin yaya azumina ?

Na biyu kuma inada matsala ne duk bayan kwana 8 da gama period dina akwai wani ruwa mai yauki da yake zubo min Wanda likitoci suke cewa ovulation period toh idan yana zuba ina ganin 'dan jini-jini aciki, kuma yana daukar lokaci kafin ya daina zuba har sai yakai lokacin zuwan wata al'adar, ko kuma brown ɗin ruwa ya dinga zuba shima haɗe da jini kuma ba lokacin al'adata bane ko yau nayi wanka toh gobe zai iya dawowa toh gaskiya ina rikecewa game da ibadata cikin azumi nagani har sau 2 Dan Allah yaya batun ibadata da azumina??.

Dan Allah zan iya yin azumin ahaka? kuma idan na daina ganinsa dole sai nayi wanka?

Dan Ina wahala duk randa ban gansa ba sai nayi wanka kuma ajima kaɗan zai sake dawowa Dan Allah abani fatawa yana daga cikin jinin hailata ne ko kuma na cuta ne??.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

1. Amsar tambayarki ta farko : Azuminki yayi. Tunda jinin yazo ne bayan faduwar rana.

2. Amsar tambayarki ta biyu : Akwai hadisin Ummu A'diyyah (ra) wacce tace "Sun kasance (su matan sahabbai) basu yin la'akari da duk wani digon jini ko gurbatacce jini (Coffee Colour) da duk wani fatsi-fatsi idan yazo musu bayan sun riga sunyi wankan tsarki (bayan kammalar jininsu na haila).

 Bisa wannan dalilin ba zaki sake wanka dan kinga irin wanann ya digo miki ba. Wankeshi kawai zakiyi kici gaba da ibadarki.

Sai dai idan kika ganshi ya dawo bisa kalar jinin haila da siffofinsa, to sai ki dena yin ibada har sai ya dauke. Kuma zaki dora lissafin kwanakinsa ne akan wadancan kwanakin da kikayi na haila. Idan lissafin yakai kwana 15 shikenan sai kiyi wanka kici gaba da yin ibadarki. Jinin ya zama na Istihadha kenan. Bazai hana yin sallah ko azumi ba. Sai dai wajibi ne ki rika yin sabon tsarki, da sabuwar alwala kafin kowacce sallar farilla. Kuma zaki iya haɗa azahar da la'asar, hakanan ki haɗa Maghriba da isha'i .

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments