𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Saƙonnin
da ake turawa ta social media na neman gafara daga mutane kafin shigowan
Ramadan, da gaske wai hakan Sunnah ne? Akwai wani hadisi ne a kan hakan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah.
Ni dai ban san wani hadisi da ya
kwaɗaitar da cewa
kafin shigowar watan Ramadan mai albarka a nemi jama’a gafara a kan zunuban da
aka aikata musu ba. Haka kuma ban san wani hadisi da ya nuna akwai wata falala
ga wanda ya sanar da jama’a ranar da watan Ramadan zai kama ba.
Muna tsoron duk waɗannan su zama daga cikin ƙarairayi
ne da ake ƙirƙirawa
ana jinginawa ga Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Wannan
kuwa kowa ya san haram ne, saboda hadisai sahihai masu yawa da suka zo a kan
haka, kamar abin da Al-Imaam Muslim ya riwaito a Muqaddimar littafinsa
As-Saheeh, a babin (Wajibcin Riwaya Daga Amintattu Da Barin Riwayar Maƙaryata),
daga Samurah Bn Jundub da Al-Mugheerah Bn Shu’ubah (Radiyal Laahu Anhumaa) cewa: Manzon Allaah
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
« مَنْ حَدَّثَ عَنِّى بِحَدِيثٍ يُرَى أَنَّهُ
كَذِبٌ فَهُوَ أَحَدُ الْكَاذِبِينَ »
Duk wanda ya bayar da wani hadisi
daga gare ni wanda kuma ake tsammanin shi ƙarya ne, to shi (mutumin) ɗaya daga cikin maƙaryata
ne. (Sahih Muslim: 1)
Haka kuma Al-Imaam Al-Bukhaariy a
cikin Kitaab: Al-Ilm, Baab: Ithmu Man Kazzaba Alan Nabiy (Sallal laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) ya riwaito da isnadinsa sahihi har zuwa daga Anas (Radiyal
Laahu Anhu) cewa: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
« مَنْ تَعَمَّدَ عَلَىَّ كَذِبًا فَلْيَتَبَوَّأْ
مَقْعَدَهُ مِنَ النَّارِ »
Duk wanda da gangar ya ƙaga
mini ƙarya,
to ya nemi mazauninsa a cikin Wuta. (Sahih Al-Bukhaariy: 108)
Wannan hadisi ne mutawaatir,
domin sahabbai sama da sittin suka riwaito shi daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam), kamar yadda malamai suka faɗa.
(Dubi: Sahih Al-Jaami’: 2837).
Don haka dai wajibi ne musulmi su
yi taka-tsantsan a kan yaɗa
duk abubuwan da suke ji da gani musamman a cikin kafafen yaɗa bayanai na zamani irin
su: Twitter da Facebook da Whatsapp da Telegram da sauransu. Kafin mutum ya
tura wani abu ya yi ƙoƙarin tabbatarwa ko samun marinjayin zato a kan sahihancinsa
daga malamai a kusa ko a nesa da shi tukun, don kar ya shigar da kansa a cikin
waɗannan da hadisai
suka yi magana a kansu.
Amma fa neman gafara da neman
yafiya daga ’yan uwa, da ƙoƙarin samu ƙarin aminci da fahimtar juna a tsakanin musulmi
kyakkyawan abu ne da ake nemansa a koyaushe ba sai a watan Ramadan kaɗai ba. Keɓance watan Ramadan da yin
hakan har da cewa wai ma Sunnah ce ta Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) ne, shi ne muke cewa ba mu san hakan ba. Janyo gamammun ayoyi ko
hadisai a kan kyautatawa ko yawaita ayyukan alkhairi a cikin Ramadan a nan ba
su isa dalilai ba. Sai a kiyaye.
Allaah ya ƙara mana fahimta da
shiriya gaba-ɗaya.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.